Ku mara wa gwamnatin Tinubu baya, kiran Ministan Labarai ga gwamnoni

Daga BASHIR ISAH

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga gwamnoni da su mara wa ƙudurori takwas na Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, yana mai cewa burin ƙudurorin ne janyo wa Nijeriya martabawa a tsakanin ƙasashen duniya.

Malagi ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Neja, Mohammed Umar Bago, a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a yayata ƙudurorin gwamnatinsa don amfanin ‘yan ƙasa, ya ce Tinubu na sane da tsananin da ‘yan ƙasa ke fuskanta sakamakon koma bayan tattalin arziki.

Daga nan, ya ce Shugaban Ƙasa ya sha alwashin nan gaba walwala za ta biyo bayan ƙuncin da ake fuskanta.

A cewar Ministan, domin rage wa ‘yan ƙasa raɗaɗin rayuwa Gwamnatin Tarayya ta raba tallafin kayayyakin masarufin ƙarfafa tallafin kuɗin da ta bai wa jihohi.

A nasa jawabin, Gwamna Mohammed Bago ya ce shi da tawagarsa sun kai ziyarar ne don taya Ministan murnar naɗa shi muƙamin minista da Shugaban Ƙasa ya yi da kuma nuna godiya ga Shugaba Tinubu dangane da hakan.

Daga nan, ya buƙaci Ministan da ya kasance jakada nagari ga Jihar Neja wajen yaɗa kyawawan manufofinta da kuma irin arzikin da jihar ke da shi.

Kana ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin Ministan zai taka rawar gani fiye da yadda ake zato dangane da muƙamin da aka naɗa shi.

Gwamna Bago ya yi ziyarar ne bisa rakiyar mambobin Majalisar Zartarwar jihar da ‘yan Majalisar Tarayya daga jihar.