Editor

9513 Posts
Har yanzu ana kulle a aure?

Har yanzu ana kulle a aure?

Tare Da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan mako kuma, mun kawo muku bayani a kan yadda wasu mazan aure musamman ma mazajen Hausawa waɗanda suke yi wa iyalansu kulle. Menene kulle? Kulle shi ne a hana mace ta fita ko ta yi mu'amala da waɗanda take so. Yawancin mazan Hausawa suna da kulle amma sai dai yayin da wasu mazan suke da sauƙi wajen mu'amala da tafiyar da iyali, wasu mazan kuma suna da zafin kishi da tsaurarawa. A yau za mu yi magana a kan…
Read More
Fuska mai maiƙo

Fuska mai maiƙo

Daga AISHA ASAS Maiƙo a fuska ba ɓoyayen abu ba ne musamman ga mata. A lokacin da ki ka fahimci fuskarki na ƙyali fiye da adadin yanda ki ka shafa ma ta mai, za ki tabbatar da fuskarki na cikin layin fuskokin da ake cewa ‘oily face’ inji bature. A wannan sati da yardar Allah shafin kwalliya na jaridar Manhaja zai kawo wa masu bibiyar mu ababen da ke janyo maiƙon fuska da hanyar magance su. Idan kin gyara mu shiga cikin darasin kai tsaye: Ana samun fata mai maiƙo ta sanadiyyar yawan fitar ‘sebun’wanda ke ƙarƙashin ikon sabashiyos gilans…
Read More
Talakawa sun wawushe rumbun ajiyar kayan abincin gwamnati a Bayelsa

Talakawa sun wawushe rumbun ajiyar kayan abincin gwamnati a Bayelsa

Daga BASHIR ISAH A ranar Lahadin da ta gabata talakawa a Jihar Bayelsa suka yi wa rumbun ajiyar gawamnatin jihar da ke yankin Kpansia a Yenagoa babban birnin jihar dirar mikiya tare da wawushe kayan abincin da ke adane a cikinsa. Majiyarmu ta ce kayan abincin da jama'a suka kwashe sun haɗa da buhunan shinkafa da garin kwaki da sauransu. Tuni dai gwamnatin jihar ta bakin Hukumar Bada Agajin Gaggawar Jihar (BYSEMA) ta yi tir da wannan aika-aikar. Cikin sanarwar da ta fitar, hukumar ta ce ma'ajiyar mai zaman kanta ce, tana mai cewa lamarin ya auku ne da misalin…
Read More
Shugabannin Nijeriya ku ji tsoron Allah

Shugabannin Nijeriya ku ji tsoron Allah

Tun lokacin da shugaba Tinubu ya ayyana janye tallafin fetur tun kafin lokacin da Shugaba Buhari ya ayyana zai janye, Amma ya dakatar zuwa watan Juni saboda ’yan takardar APC sun buƙaci a dakatar don su ci zaɓe. Kuma an dakatar sun yi kamfen buƙatar su ta biya, madadin ya tsaya ya nazarci ƙasar da matsalolin ta bai yi hakan ba nan take ya aiwatar kuma aikin gaggawa da na sani ke biyo baya. Hankalin ’yan siyasa ya kwanta mutane sun afka cikin yunwa da talauci da rashin aikin yi mutane basa iya zuwa aiki masu abin hawa sun ajiye,…
Read More
Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (2)

Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (2)

Ci gaba daga makon jiya Tare Da AISHA ASAS Abu na farko kamar yadda ka faɗa kana son matarka, kuma na lura sosai, zai iya yiwa tsananin son da ka ke yi mata ya wuce tunanin ka, takan yiwu kana son rabuwa da ita saboda kana cikin matsanancin fushi da ita kan cin amanar da ta yi ma ka, amma wannan fushin naka bai shafi ɓangaren da ka mallaka mata a zuciyarka ba, don haka duk fushin da ka ke yi da ita, zuciyarka ba za ta iya lamunce wa rabuwa da ita ba. Idan kuwa hakan ne zancen, kana…
Read More
Gare ku Ministocin Tinubu

Gare ku Ministocin Tinubu

Ga dukkan alamu a wannan sabuwar gwamnati ta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta miƙa wa zaƙaƙurai wuƙa da nama ta fuskar sabbin ministoci da aka rantsas su 45 duk da dai a ranai ta Litinin ana da tabbacin ida kawo wasu cikin mutane uku su zamo 48 kamar yadda tun farko shugaba Tinubu ya aika ma majalissa jerin sunayen su. Mu dai a yanzu saon mu su ba maraɗa kunya ai gwamnati mai faɗa da cikawa wacce za mu ce madalla da ku. Batun tallafi na rage raɗaɗin cire tallafin mai wanda a ka fara. Babu yabo kuma ba bu…
Read More
Farashin mai ya kusa sakkowa a Nijeriya – Bincike

Farashin mai ya kusa sakkowa a Nijeriya – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI Akwai yiwuwar farashin man fetur a Nijeriya ya yi raga-raga in dai har farashin ɗanyen man fetur a duniya ya cigaba da faɗowa. A tarihi dai an riga an san cewa duk lokacin da farashin mai ya ɗaga a duniya, to farashin man fetur yana ƙaruwa a gidajen mai a Nijeriya ma. Alal misali ma wannan tsadar man fetur da ake fama da ita a Nijeriya ta afku ne sanadiyyar tashin farashin ɗanyen man fetur a duniya a karo na farko a watan Mayun shekarar 2023. Saboda haka, ake tunanin a halin yanzu da farashin ɗanyen…
Read More
Ban mayar da martani kan batun hidimar ƙasata ba – Musawa

Ban mayar da martani kan batun hidimar ƙasata ba – Musawa

Daga UMAR GARBA a Katsina Ministar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arziki, Hannatu Musa Musawa ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na zamani da ma wasu jaridun ƙasar nan dangane da tirka-tirkar da ta mamaye batun hidimar ƙasarta, wato NYSC. Batun ya samo asali ne tun bayan da wata ƙungiyar marubutan kare haƙƙin ɗan'adam wato YURIWA, ta fitar da ƙorafi a kan ministar cewa ba ta kammala hidimar ƙasa ba ta shekara ɗaya wanda doka ta wajabta wa kowane ɗan Nijeriya bayan ya kammala karatun jami'a. Fitar wannan labari ke da wuya sai d'Daraktan hulɗa da jama'a…
Read More
Majalisar dokokin Legas ta ƙi tantace mutum 17 a matsayin kwamishinoni

Majalisar dokokin Legas ta ƙi tantace mutum 17 a matsayin kwamishinoni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar dokokin jihar Legas a ranar Larabar da ta gabata ta tabbatar da 22 daga cikin 39 da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya aika kwanan nan domin tantance su a matsayin kwamishinonin sa. Kakakin majalisar Rt. Hon. Mudashiru Obasa, wanda ya jagoranci zaman na ranar, ya ce tabbatar da hakan ya biyo bayan tsaiko da tantance mutanen da kwamitin wucin gadi ƙarƙashin jagorancin babban mai shigar da ƙara na majalisar, Hon. Fatai Mojeed. Ya yaba wa kwamatin kan yadda yake gudanar da ayyukansa, ya kuma buƙaci waɗanda aka zaɓa da su riƙa tunawa da cewa…
Read More
Gwamnatin Sakkwato za ta maida yara 132,000 makaranta

Gwamnatin Sakkwato za ta maida yara 132,000 makaranta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF da gwamnatin jihar Sakkwato sun rattava hannu kan wata yarjejeniya, da nufin mayar da yara da 'yan mata 132,000 zuwa makaranta. Da ta ke zantawa da manema labarai bayan sanya hannu kan takardar a ranar Laraba, A’ishatu Ɗantsoho, babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin mata da ƙananan yara, ta ce shirin zai shafi ƙananan hukumomi 23 na jihar. Ɗantsoho ta ce haɗin gwiwar ya ƙunshi ɓangarori shida, sannan kuma an zaɓo ƙananan hukumomi takwas domin gudanar da shirin na gwaji don ɗaukar nauyin yara mata da…
Read More