27
Aug
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce, ba zai sayi ɗan wasan gaba Kylian Mbappe daga Paris St-Germain a bana ba. Mbappe, ɗan shekara 24 ya zuwa yanzu ya ƙi rattaba hannu a kan kwantiragi da PSG, lamarin da ya sa ake raɗe-raɗin cewa zai koma ƙungiyar ta La Liga. Ana tunanin cewa PSG a shirye take ta sayar da kyaftin ɗin na Faransa, maimakon yin kasadar rasa shi kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a shekara mai zuwa. Da aka tambaye shi game da yarjejeniyar Mbappe, Ancelotti ya ce "A'a, na yanke hukunci kashi 100." Mbappe…
