Jaruma Hannatu Umar Sani ta rasu

Daga AISHA ASAS 

A ranar Lahadin ta makon iiya, 20 ga watan Agusta, masana’antar Kannywood ta tashi da wani sabon rashi. Duk da cewa ta rasa ɗaya daga cikin tsofaffin jarumanta ne, hakan bai hana mutuwar ta zama abin alhini gare su da kuma masoyanta ba, sakamakon irin rawar da ta taka a lokacin da take masana’antar. 

Jaruma Hannatu Umar ta amsa kiran mahalicci a gidan yayarta da ke unguwar Katampe a Birnin Tarayya, Abuja, kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito. 

Wani abin tava zuciya da mutuwar jarumar shi ne, ba ta tare da wata rashin lafiya bare har a yi mata zaton mutuwa, domin wani makusancinta ya tabbatar da lafiya ƙalau ta tashi daga barci, har ta yi shiri don fitowa falo da zummar yin kalaci, akan hanyar isa falon ne ta yanke jiki ta faɗi, wanda hakan ya zama sanadin tafiyar ta.

Watakila mai karatu zai ɗan sha wahalar tunawa da ko wacce ce jaruma Hannatu Umar Sani, kasancewar ta ɗan jima da barin masana’antar Kannywood, sai dai rawar da ta taka zai sa da ɗan qaramin tuni za a iya tunawa da ita.

Jarumar mai kimanin shekaru 34 da haihuwa, ta kasance ‘ya ta qarshe ga iyayenta, inda ta ke da yayye 10, kuma ta fara yin fim ne a kamfanin Lerawa Production na darakta El-Sa’eed Yakubu Lere. Sannan ta fara da fim mai suna ‘Ummi’ tare da jarumi Sani Musa Danja, kuma sun yi waqa da ta yi tashe a wancan lokaci mai suna ‘Da Soyayya Na Fito Yarinya Da Soyayya Zan Koma Gida’.

A lokacin jarumar tana da shekaru 14 da haihuwa, kuma ta shigo harkar fim ɗin ne da amincewar iyayenta, kamar yadda darakta Yakubu Lere ya faɗa a tattaunawar sa da Mujallar Fim. 

Lere ya bayyana cewa, baki da baki mahaifinta ya ba shi amanar ta a lokacin da za ta shiga fim, kuma shi ne da kansa ya ɗauke ta ya kai ta Kano, ya damqa amana ga jarumi Sani Musa Danja, wanda a lokacin babbar jaruma ta kamfanin nasu ita ce Maryam Abubakar, wadda aka fi sani da Maryam Jankunne, sai ita Hannatu ta zama ta biyu, suka kaɗe suka ciyar da kamfanin na 2-Effects Empire gaba, mallakin jarumin Sani Danja da kuma Yakubu Muhammad.

Da wannan ɗan tunin mai karatu zai iya tunawa da irin rawar da jarumar ta taka, tauraruwarta ta haska, har ma ta disashe ta dayawa daga cikin jarumai mata na wancan lokaci, kuma ta jima tana haskawa har zuwa lokacin da ayar aure ta sauka gare ta, inda ta yi aure, sai dai daga baya sun rabu da mijin ba kuma tare da sun samu ƙaruwa ba.

Marigayiyar ta yi qoqarin dawowa harkar fim, kuma jarumin da ya fi moriyar baiwar da take da ita, wato Sani Musa Danja ya ɗan yi ƙoƙarin saka ta a finafinanshi, sai dai jifa-jifa, daga baya ta koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. 

An yi jana’izar jaruma Hannatu Umar Sani a babban masallacin ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar ta Lahadi, makwancinta kuwa ya kasance a maƙabartar da ke unguwar Gudu.

Allah Ya jikan jaruma Hannatu Umar Sani da rahama, Ya kyautata tamu baya ga tata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *