25
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da rabon tallafin kayan abinci ga marasa galihu da kuma al’ummomin da tashin hankali ya shafa iya tsawon mulkinsa. Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri yayin da ya ke ƙaddamar da rabon kayan tallafin na Gwamnatin Tarayya ga gidajen dubu 100,000. Zulum ya ce yayin da Gwamnatin Tarayya ta samar da gidaje 100,000, gwamnatinsa na samar da ƙarin gidaje 300,000 don su zama gidaje 400,000. Ya bayyana cewa lamarin Borno ya sha bamban saboda wasu yankunan da…
