Yadda kyakkyawar zamantakewa ke kawo zaman lafiya

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu’amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra’ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama’a, daga vangarori daban-daban.

Babu shakka zaman lafiya da jama’a, tausayawa, tallafawa, da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuƙa, babu ma kamar wannan lokaci da jama’a ke cikin ƙunci da rashin yarda da juna, saboda kurakuran da suke zargin wasu suna yi da gangan, don cimma wata manufa ta son ran su, ko danne haƙƙin wasu.

Rashin yarda, zargin juna, hassada, kishi, zalunci, babakere, da tauye haƙƙin raunana, halaye ne da aka saba gani a zamantakewa ta yau da kullum, inda wasu ke ƙoƙarin fifita kansu da tilasta buƙatun su kan na sauran mutane, a dalilin haka kuma sai a samu turjiya da nuna rashin yarda daga wani ɓangare.

Mummunar halayya irin ta hassada na ruguza imani da mutuncin mutum, saboda kasancewarta mugun ciwon da ke nuƙurƙusar mai yin ta a cikin zuciyarsa shi kaɗai.

A taƙaice, idan aka ce HASSADA ana nufin wani yanayi da mutum zai riƙa jin wani zafi, rashin kwanciyar hankali, ko vacin rai a yayin da ya ga wani ɗan uwansa, maƙwabci, aboki ko ma dai wani na kusa da shi da Allah ya yi wa ɗaukaka, ko wani alheri da shi bai samu ba.

Wasu manazarta sun kasa hassada zuwa gida uku, inda suka nuna cewar, akwai hassada ta jin ƙyashi, yayin da mutum ya ji a zuciyarsa don me wani zai fi shi samun wani abu a rayuwa. Kamar misalin kuɗi, mulki, baiwa ko muƙami.

Haka kuma mutum ya kan ji shi ba ya son kowa ya samu wani abin alheri ko ƙaruwa sai shi kaɗai. Sai na uku wanda shi ne ya fi kowanne muni, wato mutum ya ji cewa idan dai shi ba zai samu abu ba to, gara kar kowa ma ya samu. Irin su ne suke zama ‘yan a fasa kowa ya rasa!

Mutane da yawa suna faɗawa cikin aikata hassada ba tare da sun ankara ba. Alal misali: Yawan yin magana a kan ci gaban wani ko wata. Har ya kai ga cewa, ‘Oh… su wane an haye, sai ka ce da ba teburin mu daya ba a wajen aiki, lokacin nan kuwa kayansa basu wuce kala biyar ba.’

Haka nan kuma mutum ya kan riƙa ambaton cewa, ‘Su wane an samu shiga, ji wai yanzu shi ne kaza, sai ka ce ba tare muke cin kwakwa ba.’

‘Dubi daga malami ya shigo aji sai ya fara wani iya yi wai shi a dole mai kwakwalwa.’

Yadda mutum zai gane idan ya fara nuna halayyar hassada shi ne, yawan nuna damuwa da al’amarin wani ko wata, wanda kwata kwata bai shafeka ba. Damuwa da son sanin halin da wata ko wani yake ciki. Idan ka ji mummunan labari game da wani ka ji daɗi a ranka, ko ma ka yi dariya ko shewa, idan kuma ka ji labari mai daɗi game da mutum sai ka ji ranka ya vaci, ka kasa yi masa fatan alheri, ka fara jin tsoron kar ya wuce ka a wani mataki na rayuwa. Sai ka fara kokarin kai sukarsa a wajen abokan arzikin sa, ko ƙoƙarin faɗin miyagun maganganu game da shi, ko kuma faɗin kalamai na vatanci game da shi, musamman ma idan ba a tambayeka labarinsa ba.

Hassada tana hana mai yinta samun cigaba a cikin rayuwarsa da kuma duk abin da ya sa gaba ba zai ga nasara bayyananniya a kai ba. Hassada tana rage imani kuma tana taimakawa wajen aikata shirka da fita ma daga addini ba tare da mai yin hassadar ya sani ba.

Ya kamata mutum ya yi ƙoƙarin ganin ya yaƙi wannan mummunar halayya ko kare kansa daga gare ta. Kuma gane yadda zai iya cimma haka ba wani abu ne mai wuya ba, saboda ai yin hassadar ta fi wuya! Takurawa kan mu muke yi, sai mun yi hassadar duk kuwa da mun san illarta da kuma nauyin zunubinta.

Na farko, mutum ya yi ƙoƙarin cire kansa a kan duk wasu al’amuran da ba su shafe shi ba. Kuma ya yi ƙoƙari ya mayar da hankalinsa a kan inganta rayuwarsa. Sannan ya kiyaye kansa daga qananan gulmace-gulmace. Son iyawa ko son ba da shawara a inda ba a nemi taimakonsa ba. Mutum ya kuma kasance yana yi wa zuciyarsa addu’ar tsarkakuwa daga dukkanin miyagun ayyukan da ka iya gurvata ta.

Wannan baƙar halayya ta hassada na da nasaba da yadda mutum kan nuna son kansa fiye da maslahar sauran jama’a. Mutane masu son kansu suna haifar da damuwa, ƙunci da ƙiyayya mai yawa, saboda sun fifita son zuciyarsu a kan amfanin da jama’a da dama za su samu. A kan abu ƙalilan da wani yake kwaɗayin samu sai ya rusa jin daɗin da ƙoƙarin da wasu suka daɗe yana yi.

Mun sha jin ƙorafe-ƙorafe daga mutanen da aka tauye wa haƙƙi ko aka zalunta, sakamakon son zuciyar da wani ya nuna musu, don kawai ya samu damar da zai yi abin da ya dace amma ya kasa, saboda zarmewa da son zuciya.

Akwai mutanen da za ka riƙa yi musu kallon manya ana girmama su saboda matsayin da suke da shi, ko arzikin da Allah ya ba su, har ma ka ji ana yi musu kirari, don kwaɗayin samun wata alfarma daga wajensu. Sai dai da a ce za ka samu jin abin da waɗanda ke ƙarƙashin sa ko iyalinsa suke faɗa, ba za ka so ka sake kallon sa da martaba ba. Saboda halinsa na rashin fitar da haƙƙin waɗanda suka yi masa ƙwadago da gumin su, sauke nauyin iyali da ‘yan uwa da ke kansa. Yana ganin idan ya cire wani abu daga arzikin sa to, zai rage masa jin daɗi, ko zai bayar a inda ba a san zafin su ba.

Yana yi wa mutane wahala su sadaukar da wani ɗan yanki na jin daɗin su, walwala ko damar da suke da ita don wani ya amfana. Sai ka ga ana ta fama da wani a cikin motar haya kan ya ɗan gyara zamansa domin kowa ya ji daɗin zama, amma mirsisi sai ya qi, saboda tunanin idan kowa ya zauna da kyau shi ba zai sake yadda yake so ba. Haka ma ko a gaban ubangiji wajen sauke farali, za ka ga wani ya yi babakere a waje ana roƙon sa ya gyara zama ko tsayuwar cikin sahu, amma yana ganin za a takura masa shi ba zai yarda ba.

A duk yayin da mutane suka fahimci wane yana da halin rowa, son kai da rashin sassauci a harkokin rayuwar to, yana zama abin ƙyama da yi wa kaffa kaffa. Kyautatawa da nuna halin kwarai suna sanya ƙaunar mutum a zuciyar abokan zamansa da sauran ‘yan uwa.

Sau da dama an sha samun asara mai yawa ta rai ko ta dukiya, da ɓacin rai mai tsanani, saboda wani ya kasa haƙuri a samu yadda ake so ko ya yi abin da ya kamata daga ɓangarensa, don yana ganin ba shi ne zai amfana ba, ko kuma idan ya yi haka zai takura.

E, ba an ce lallai mutum ya riqa takurawa kansa don jin daɗin wasu ba ne, amma kyautatawa tana da amfani, kuma akwai alheri da ke bin bayan sadaukarwa ta tsakani da Allah. Ba kowanne lokaci ne yin abin da ya kamata ke zama takura ba, sauke nauyi ne. Kai ma wani lokaci za ka nemi wani abu daga wajen wani, wanda ka ke ganin ya kamata ya yi maka, idan bai yi ba kai ma ba za ka ji daɗi ba.

Mutane masu son zuciya ba sa tava samun wadata da gamsuwa da rayuwar su, ko da kuwa sun samu damar yin duk abin da suke so, saboda ko da yaushe tunanin su ba ya wuce jin daɗin kansu ta hanyar ƙuntatawa wasu.

Don haka kirana ga mai karatu shi ne a guji fifita son rai, domin an ce son zuciya bacin zuciya!

Allah ya taimake mu!