Editor

9513 Posts
Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a ƙarni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari'a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane. Lokacin da Ahmed Baba ya rayu: An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu…
Read More
Ba za mu yi ƙarya don kare muradun gwamnati ba – Ministan Labarai

Ba za mu yi ƙarya don kare muradun gwamnati ba – Ministan Labarai

Daga BASHIR ISAH Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Muhammad Idris Malagi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa ba ta buƙatar sharara ƙarya don kare muradun gwamnati, "za mu riƙa faɗin komai yadda yake", in ji shi. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki bayan rantsar da shi da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi a ranar Litinin. Ya ce ma'aikatarsa da gwamnati za su zama masu gaskiya wajen bada bayanai. Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta kasance mai ƙoƙarin yin gyara a duk inda ta yi kuskure. Haka nan, ya ce nan ba da daɗewa…
Read More
Shugaba Tinubu ya rantsar da ministocinsa

Shugaba Tinubu ya rantsar da ministocinsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Nyesom Wike da wasu 44 a matsayin ministocinsa a hukumance. Bikin rantsarwar ya gudana ne ranar Litinin a babban zauren taron Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. An raba ministocin ne zuwa rukuni bakwai sannan aka rantsar da su rukuni bayan rukuni. Runkunin farko da aka rantsar ya ƙunshi Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, Ƙaramar Ministar Ƙwadago Nkiruka Onyejeocha, Ƙaramin Ministan Gas a Ma'aikatar Albarkatun Fetur, Ekperikpe Ekpo, Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy da kuma Ministan Ilimi, Tahir Maman. Sai rukuni na biyu da ya ƙunshi…
Read More
Rundunar ‘yan sanda ta haramta zanga-zanga a Kano gabanin yanke hukuncin zaɓen gwamna

Rundunar ‘yan sanda ta haramta zanga-zanga a Kano gabanin yanke hukuncin zaɓen gwamna

Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta haramta kowane irin nau'i na zanga-zanga a faɗin jihar. Da yake sanar da wannan doka a jihar a ranar Litinin, Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Husaini Gumel, ya ce dokar ta fara aiki nan take. A cewar Kwamishinan, bayanan sirri sun nuna jam'iyyun NNPP da APC a jihar na shirin gudanar da zanga-zanga dangane da zaman kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar. Idan ba a manta ba, Jam'iyyar APC a Kano ta shigar da ƙara kotu inda take ƙalubalantar bayyana NNPP da hukumar zaɓe INEC ta yi a matsayin wadda ta lashe…
Read More
Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta

Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta

Tare Da AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sunana……….daga……….. Na samu number daga hannun……..Dalilina na neman ki dai shi ne, abokina ne shi, na sanar da shi matsalar da nake tare da ita, sai ya ba ni number ki ya ce, na ma ki magana, wai kwanaki ma ke kin ka kashe matsalarsa da mai ɗakinsa. Wato mata nake da ita, kuma har ga Allah Ina masifar san ta, wannan ya sa nake kishinta ƙwarai da gaske. Ban rage ta da komai ba, duk abinda na mallaka zata iya iko da shi. Kuma ta vangaren kwanciyar aure daidai gwargwado ina duba…
Read More
DSS ta cafke Manajan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

DSS ta cafke Manajan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Hukumar tsato ta DSS ta tsare Manajan Jirgin ƙasan a Abuja-Kaduna na Kaduna, Pascal Nnorli, biyo bayan takardar sanarwar gargaɗin yiwuwa kai wa jirgin hari da ta bayyana. Majiya mai tushe daga Hukumar Jirgin Ƙasa ta Nijeriya ta shaida wa jaridar News Point Nigeria an tsare Manajan ne tare da Manajan Ayyuka na hukumar, Victor Adamu da kuma wasu ma'aikatan hukumar. Blueprint Manhaja ta rawaito a makon jiya DSS ta yi gargaɗin tsaro ga hukumar inda ta ce ta bankaɗo shirin 'yan bindiga na yiwuwar kai harin kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna kowane lokaci. Cikin sanarwa mai dauke da sa hannun…
Read More
FUGA Gashuwa ta yi sabbin mataimakan Shugabar Jami’ar

FUGA Gashuwa ta yi sabbin mataimakan Shugabar Jami’ar

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Hukumar Zartaswar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa a Jihar Yobe (FUGA) a, taronta na 44 a ranar Jummu'a, a ƙarƙashin shugabar jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, ta amince da naɗin Dokta Ibrahim Ahmed Jajere da Dokta Mohammed Attai Yakubu a matsayin Mataimakan Shugabar Jami’ar; na ƙwararru da na sha'anin gudanarwa. A cikin wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar, Malam Adamu Saleh ya fitar ta ce, Hukumar Zartaswar ta amince da naɗin mataimakan shugabar jami’ar guda biyu ne a ƙarƙashin doka Sashe na 4 na dokokin Jami’o’i mai lamba 11 na shekarar 1993,…
Read More
Muna so matasa su karkato ga sana’o’in gargajiya – Sarkin Askar Jihar Filato

Muna so matasa su karkato ga sana’o’in gargajiya – Sarkin Askar Jihar Filato

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A yayin da sana'o'in gargajiya daban-daban ke samun koma baya, saboda sauye sauyen zamani da rashin samun tallafin hukumomi. An fara ganin farfaɗowar wasu tsofaffin sana'o'in Hausawa na iyaye da kakanni da ke ƙoƙarin jawo hankalin matasa ga raya al'adunsu na gado, don samun abin dogaro. Harkar wanzanci na daga cikin waɗannan sana'o'in da daruruwan matasa ke cin abinci a cikinta, sakamakon sabbin jinin shugabanni da aka samu da ke ƙoƙarin inganta sana'ar da kuma ƙara kusantar da ƙungiyar raya harkar wanzanci ga gwamnati, don kawo wa sana'ar cigaba. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, ABBA ABUBAKAR…
Read More
Litar fetur: Za a ƙara wa barkono zafi

Litar fetur: Za a ƙara wa barkono zafi

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Gaskiya ba a ɗaukar raɗe-raɗi ko jita-jita kan ƙarin farashin man fetur da wasa don yadda ƙarin ke neman zama ruwan dare game duniya a Nijeriya. Ko ma’aikata sun tafi yaji don fusata da ƙarin farashi tamkar yaji za a ƙara wa yaji. In dai ba gwamnati za ta ɗau wasu matakai masu tasiri na kawo sassauci ba ta hanyar sa ido kan yadda farashin ke tafiya ɗawainiya ce kawai za a yi ta sha. Ai tun da gwamnati ta cire dukkan tallafin fetur ba wata dabara ta yanzu-yanzu da ta wuce zuba ido kan…
Read More
Matasan Nijeriya, kada ku karaya!

Matasan Nijeriya, kada ku karaya!

Kwanan nan, ƙasashen duniya sun yi bikin murnar ranar matasan duniya. Ranar 12 ga watan Agusta ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar matasa ta duniya a shekarar 1999, kuma ita ce bikin shekara-shekara na rawar da matasa maza da mata ke takawa a cikin al'umma. Yana ba da damar wayar da kan jama'a game da ƙalubale da matsalolin da ke fuskantar matasan duniya Kowace shekara, Ranar Matasa ta Duniya ta kasance wani jigo na musamman wanda ke magance matsalolin ƙalubale da matasa ke fuskanta. Taken ranar matasa ta duniya a shekarar 2023 shi ne ‘Green Skills for Youth: Towards…
Read More