Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta

Tare Da AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Sunana……….daga……….. Na samu number daga hannun……..Dalilina na neman ki dai shi ne, abokina ne shi, na sanar da shi matsalar da nake tare da ita, sai ya ba ni number ki ya ce, na ma ki magana, wai kwanaki ma ke kin ka kashe matsalarsa da mai ɗakinsa. Wato mata nake da ita, kuma har ga Allah Ina masifar san ta, wannan ya sa nake kishinta ƙwarai da gaske.

Ban rage ta da komai ba, duk abinda na mallaka zata iya iko da shi. Kuma ta vangaren kwanciyar aure daidai gwargwado ina duba buƙarta, har littafai da videos da ake yi na yadda za a gamsar da iyali nake ɗan bibiya duk saboda ita. Ina kula da ƙarfin gabana dan kar na gaza mata. Amma a ‘yan watanni uku baya, na dawo gida ba zata, dan lokacin tashi kasuwa bai yi ba, shi ne na tarar da matata da wani abokina suna kwance a gadona yana amfani da ita.

Da idona biyu na gan su hajiya Aisha ba wani ya sanar da ni ba, amma abinda ya ba ni mamaki duk zafin kishin da nake da bai sa na hau kansu ba, Ban shaƙe wuyan shegen abokin nawa ba. Asalima har ture ni ya yi lokacin da yake ƙoƙarin guduwa daga ɗakin. Dalilin nemanki dai shi ne, yanzu haka matata na cikin gidana, duk da cewa zuciyata ta yi mata tsana mai tarin yawa, na ƙyamace ta, ko hannunta ba na son riƙewa, kai in kai zancen ƙarshe har raina na tsani zama da ita, na cire ta a layin matan da nake so, ba ni da buri sai na ta bar min gidana, Dan ba zan iya zaman aure da ita ba, amma fa na kasa sakin ta, na kasa yi mata masifa kan abinda ta aikata.

Abinda ya ƙara ɗaure min kai jiya shi ne, ta same ni ɗakina ta nuna buƙatar na kusance ta, duk da zuciyata ta tsani haka, amma haka na yi, amma cikin tursasawa, yanda na ji tamkar wanda aka aza wa bindiga ko ya yi, ko a harbe shi. Abin kullum damuna yake yi, wallahi na tsani zama da ita, kuma har yanzu da nake turo miki wannan ‘audio’ na tsani zama da ita, kuma Ina so na sake ta ko raina zai daina raɗaɗi, sai dai wallahi na kasa. Jiya fa bayan mun gama har takarda na ɗauko da biro, wai tunda ban iya furtawa, na rubuta, sai na nemi abin rubutawar ma sama da ƙasa na rasa.

AMSA:

Tun daga farko zan soma da hukuncin matarka a Musulunci, wato macen da ta yi zina da aurenta. Akwai hukunci biyu mabambanta da ke cikin Al’ƙur’ani mai tsarki, wanda har yau muna karanta su, wanda wani lokacin sukan rikita ɗaliban ilimi, musamman waɗanda suka haɗu da malamai masu son kai a karatunsu. Aya ta farko a cikin suratul Nisa’i, aya ta 15, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, “kuma waɗanda suka je wa alfasha daga matanku, to, ku nemi shaidar mutane huɗu daga gare ku a kansu.

To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidaje har mutuwa ta karɓi rayukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.” Wannan ayar tana magana kan hukucin matan da suka aikata zina, wato a rufe su a cikin gida ba za su fita ba, har sai hukuncin Allah ya tabbata a gare su.

Aya ta biyu a cikin suratul Nur, aya ta 2, Allah maɗaukaki ya ce, “Mazinaciya da mazinaci, to, ku yi bulala ga kowane ɗaya daga gare su, bulala ɗari. Kuma kada tausayi ya kama ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kuna yin imani da Allah da Ranar Lahira. Kuma wani yankin jama’a daga muminai, su halarci azabarsu.”

Abin tambaya anan shi ne, wacce ce ya kamata a yi aiki da ita wurin yanke hukunci a wannan zamani da muke ciki? Abinda aka tabbatar shi ne, aya ta farko wadda ta ke cikin suratul Nisa’i ita ce ayar da ta fara sauka, kuma ita ce aka shafe ta, ma’ana zuwan wannan aya ta suratul Nur da kuma wadda ta yi bayani kan hukuncin mace da ta yi zina da aurenta, aka ce a jefe ta har sai ta mutu, su ne suka shafe ayar farko.

Dukka wannan hukunci yana kasancewa ne a hannun alqali na Musulunci, idan aka kama ta ta yi ko wani ya ganta ya gabatar da shedu huɗu ƙwarara, sannan alƙalin zai yanke ma ta hukuncin kisa ta hanyar jifa. Amma idan ya kasance ta aikata babu wanda ya ganta, to malamai da dama sun tafi kan ta yi tuba ga ubangiji, tare da niyyar ba zata sake komawa kan zinar ba. sun kafa hujja da ƙissar wanda yakawo kansa wurin manzon rahma kan ya zo ya fallasa kansa, wato ya yi zina, sai manzon rahma ya kawar da kansa, ya sake komawa ɓangaren da ya juya, ya sake maimaitawa, har dai lokacin da annabi ba shi da zaɓi sai na yanke hukunci kansa.

Idan mun fahimci karatun sosai za mu gane cewa, zinar matar aure bai raba auren da ke kanta ba, matuƙar ba mijin ne ya buƙaci sakin ta ba. Don haka ɗan’uwa babu abinda ya tava auren ka da matarka a Musulunce.

Magana ta gaba, shin ka tambaye kanka ko me ya sa Allah Ya nuna maka wannan ɗanyen aikin da matarka take aikatawa? Ababe ne biyu zuwa uku; na farko, aya a cikin littafi mai tsarki ta ce, “mazinaci ba ya aure sai mazinaciya ‘yar’uwarsa, mazinaciya ba mai aurenta sai mazinaci, an haramta hakan tsakanin muminai.”

Duk da cewa wasu malamai sun fassara ayar da kafin aure na daga abinda ku ka gani na hallayar waɗanda za ku aura. Yayin da wasu suka fassara ta da duk abinda ka yi sai an yi ma.

Ala kulli halin dai zancen shi ne, idan ka san kana aikata kwatankwacin abinda matarka take yi, to ka kalli wannan a fuskar ishara, wato ka aikata kuma an aikata ma, don haka ka tuba don kar a ci gaba da yi ma abinda ka ke yi.

Magana ta biyu, yakan yiwu tsare kanka ne ka yi, Allah Ya lurar da kai abinda matarka ta ke aikatawa don ba ka tare da haƙƙinta, wannan ma yana da kyau ka tuna godiya ga mahaliccinka ta hanyar ganin ba ka cutatar da ita fiye da yadda ta cutar da kai ba, ma’ana idan ka yanke hukuncin sakin ta, ka sake ta ba tare da tozarci ba, idan kuwa kana da buqatar ɗaukar mataki, to ya zama ka kai ga alqali ba ka yi a karan kanka ba, sai dai yafiya shi ne mafi alkhairi gare ka.

Idan mun koma kan dalilin da ya sa ka nemi shawara, wato zancen kasa sakin matarka, in har na fahimce ka da kyau, sakin ta ka ke da muradi, amma wani abu da ba ka san ko mai ye ba na taka ma birki. A nan ma matsalar tana da fuska biyu.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *