20
Aug
Daga BASHIR ISAH Jagoran juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani, ya bayyana cewa sai bayan shekara uku sojoji za su miƙa mulki ga farar hula a ƙasar. Ya bayyana hakan ne a jawabin kai-tsaye da ya yi wa 'yan ƙasar a talabijin ranar Asabar da daddare. Jawabin nasa na zuwa ne bayan tattaunawar da suka yi da tawagar ECOWAS ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya). Janar Tchiani ya ce a tsakanin wata ɗaya mulkin sojin zai kafa kwamitin da zai samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar. Ya ƙara da cewa, duk da dai…
