Editor

9513 Posts
Ma’aikatun ministoci:Yadda Tinubu ya shammaci ’yan Nijeriya

Ma’aikatun ministoci:Yadda Tinubu ya shammaci ’yan Nijeriya

*Malagi da sauran ministoci za su sha rantsuwa ranar Litinin*A karon farko Kano ba ta da babban minista*Ɗan Kudu ya zama Ministan Abuja bayan shekaru masu yawa*Tsohon gwamna ya zama ƙaramin minista*Wataƙila Gawuna ya samu kujerar babban minista daga Kano Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Laraba, 16 ga Agusta, 2023, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya shammaci masu lura da al’amuran yau da kullum da sauran al’ummar ƙasar bayan da ya sanar da ma’aikatun da sababbin ministocinsa za su jagoranta. Shugaba Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin, 21 ga Agusta, 2023. Ministocin da za…
Read More
Za mu kai ziyarar ba-zata ga bankunan da ake zargi da cinikin Dala ta haramtacciyar hanya – Gwamnnan CBN

Za mu kai ziyarar ba-zata ga bankunan da ake zargi da cinikin Dala ta haramtacciyar hanya – Gwamnnan CBN

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi barazanar gurfanar da bankunan da suke cinikayyar Dala ba bisa ƙa'ida ba. Wato ta haramtacciyar hanya. Sannan kuma a gurfanar da wannan banki da ya karya doka a gaban kuliya. Gwamnna riƙon ƙarya na CBN, Folashodun Shonubi, shi ya bayyana haka a wata lacca da aka gabatar a kan samar da mafita ga tattalin arzikin Nijeriya, wanda aka yi a Abuja. Taron ya mai da hankali a kan yadda za a katange shigar da kuɗaɗen gwamnati zuwa haramtacciyar hanya tare da shigar da su inda ya dace don kawo cigaban…
Read More
An gudanar da taron nema wa ƙasa zaman lafiya a Legas

An gudanar da taron nema wa ƙasa zaman lafiya a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Majalisar fadar Mai martaba Sarkin Guragun Jihar Legas ƙarƙashin jagorancin, Alhaji Amadu Abubakar Gaya, wanda kuma shine Shugaban Majalisar Sarakunan Guragun Legas sun gudanar ta taron yi wa Nijeriya addu'ar ƙarin zaman lafiya da yalwar arziki. Mahalarta taron sun haɗa da manyan malaman addinin Musulunci na Jihar Legas da sarakunan Guragu na jnguwanni daban-daban da waɗansu sarakunan al'ummar Hausawa da sauran na kasassu mazauna cikin garin Legas da kewayenta.Taron ya gudana ne a kan titin Oko Baba Abeokuta st Ibitimeta dake cikin garin Legas. Bayan malamai sun kammala gudanar da addu'o'in nema wa Nijeriya da…
Read More
Gwamnatin Kano za ta karɓo wani tallafi da gwamnatin Ganduje ta daƙile – Hon. Sawaba

Gwamnatin Kano za ta karɓo wani tallafi da gwamnatin Ganduje ta daƙile – Hon. Sawaba

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Mai bai wa Gwamnan Kano shawara na musamman kan namun daji da gandu daji, Hon. Ahmad Halliru Sawaba ya ce gwamnatin jihar Kano za ta yi ƙoƙari wajen ganin ta dawo da tallafin da wata cibiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta so ta kawo wa al'ummar Jihar Kano don tallafa masu a harkar kiwon kaji amma gwamnatin da ta gabata ta daƙile. Ya bayyana haka ne a yayin wani taro da mai bai wa gwamna shawara kan jam'iyyun gama kai Jamilu Abba ya yi da ƙungiyoyi a safiyar ranar Talata. Ya ce irin wannan tallafi…
Read More
Yawaitar matatun mai a Nijeriya ba za su kai ga rage farashin mai ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Yawaitar matatun mai a Nijeriya ba za su kai ga rage farashin mai ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ajuri Ngelale, babban mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin jama’a ya ce ƙarin matatun mai a Nijeriya, ba zai haifar da rage farashin man fetur ba. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi kwanan nan ta hanyar Labaran TVC. A cewarsa, sau da yawa mutane suna cewa idan matatun ƙasar suna aiki, man zai yi arha ga ‘yan Nijeriya a fanfo, amma babu wani abu da zai wuce gaskiya. Ya ce: “Wannan tatsuniya ce, ba ta faruwa a ko’ina a duniya, ko da a ce muna…
Read More
​Gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen bunƙasa dimukraɗiyya a Nijeriya – Shettima

​Gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen bunƙasa dimukraɗiyya a Nijeriya – Shettima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu ta ci gaba da jajircewa wajen ƙara bunƙasa dimokuraɗiyya a ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dole ne dukkan ‘yan Nijeriya su haɗa kai don raya dimokuraɗiyyar ƙasa. Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu shugabannin ƙungiyar masu bada shawara ta jam’iyyu (IPAC) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. A cewar mataimakin shugaban ƙasar, “Namu ƙasa ce ta matasa, tsarin dimokuraɗiyya na matasa kuma dole ne a samu fahimtar juna,…
Read More
Taiwo Awoniyi: Yadda birkila ɗan Nijeriya ya koma buga Firimiyar Ingila

Taiwo Awoniyi: Yadda birkila ɗan Nijeriya ya koma buga Firimiyar Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Lokacin da koci Steve Cooper ke ƙoƙarin gina harsashin Nottingham Forest don tsira a gasar firimiya, ya yi duban tsanaki inda ya ga ya dace ya ɗauko ɗan wasan farko wanda ya kasance tsohon mai aikin birkila. Kuma tabbas Taiwo Awoniyi ya saka masa, yayin da ɗan Nijeriyar ya taimaka wurin nasarar da Forest ta samu na farko a kakar bara, wadda ta doke West Ham 1-0 da cin Arsenal 1-0, hakan ya sa ta ci gaba da zama a gasar Firimiya a watan Mayu. Hakan ya zo ne saura mako ɗaya a ƙarƙare wasannin bara,…
Read More
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 28, sun kuɓutar da mutum 82 a mako guda

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 28, sun kuɓutar da mutum 82 a mako guda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya a ranar Alhamis ta ce dakarunta sun kama jimillar masu aikata laifuka 114 da suka haɗa da ’yan ta’adda 92, da ’yan bindiga 6, da kuma masu satar mai 7 a cikin makon da ya gabata a yayin farmakin da suka kai kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da sauran masu aikata laifuka a faɗin ƙasar. Sojojin sun kuma ceto sama da mutum 82 da aka yi garkuwa da su daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su tare da kashe 'yan ta'adda sama da 28 a cikin wannan lokaci. Manjo…
Read More
Matsalar tsaro: Gwamnoni sun shiga ganawar gaggawa da Ribadu

Matsalar tsaro: Gwamnoni sun shiga ganawar gaggawa da Ribadu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta gudanar da taron gaggawa a sakatariyar ƙungiyar da ke Abuja a daren Laraba, inda Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, ya halarci taron. Duk da cewa an hana ’yan jarida su ba da labarin buɗe taron, ajandar da aka raba wa gwamnonin sun nuna cewa batutuwan da suka shafi harkokin tsaro na jihohi da na ƙasa ne zai sa a gaba a tattaunawar. Sauran abubuwan da aka jera domin tattaunawa sun haɗa da tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya cire, da…
Read More
Mun shirya tsaf don tunkarar Nijar – Dakarun ECOWAS

Mun shirya tsaf don tunkarar Nijar – Dakarun ECOWAS

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Manyan hafsoshin dakarun ECOWAS sun ce a shirye suke su tura sojoji, don mamaye Nijar da nufin dawo da mulkin dimokuraɗiyya a faɗin ƙasar. Bayan da jami'an tsaron shugaban Ƙasar suka karɓe mulki daga hannun shugaba Mohamed Bazoum, ƙungiyar ECOWAS ta bada wa'adin kwanaki 7 ga sojojin ƙasar da su maido da shugaban ƙasar ko kuma su fuskanci takunkumi, ciki har da yiwuwar ɗaukar matakin soji. Sai dai gwamnatin mulkin sojan ta yi kunnen uwar shegu kan maganar ECOWAS ta kuma yi tir da tsoma bakin ƙasashen waje. Bayan haka, ƙungiyar ta yankin ta buƙaci hafsoshin…
Read More