17
Aug
Daga BASHIR ISAH Hedikwatar Tsaro (DHQ) da ke Abuja ta bayyana cewa, sojoji 36 'yan bindiga suka kashe a Jihar Neja. A ranar Lahadin da ta gaba 'yan bindiga suka yi wa sojoji kwanton-ɓauna a hanyar Zungeru zuwa Tegina inda suka kashe sama da sojoji 20. Sai dai mai magana da yawun babban ofishin tsaro na ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, ya ce askarawa 36 ne suka mutu a harin. Buba ya bayyana haka ne a wajen taron manema labarai na mako-mako da ya shirya inda ya yi ƙarin haske game da adadin sojojin da 'yan bindigar suka kashe da…
