Editor

9513 Posts
Gwamnati ta sake maka Emefiele a kotu kan zargin laifuffuka 20

Gwamnati ta sake maka Emefiele a kotu kan zargin laifuffuka 20

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta sake maka tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele a kotu inda take tuhumarsa da aikata laifuka 20. Wannan na zuwa ne bayan shigar da buƙatar janye ƙarar "mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya" da gwamnatin ta shigar da fari kan Emefiele ɗin a Babban Kotun da ke zamanta a Legas. Daraktan sashen shigar da ƙararraki (DPP) a Ma'aikatar Shari'a ta Ƙasa, Mohammed Abubakar, ya sahaida wa alƙalin kotun, Nicholas Oweibo, cewar buƙatar janye ƙarar daga ɓangaren gwamnati ta taso ne domin ba da damar zurfafa bincike.…
Read More
Sai bayan mutuwar babana da aurena ne na samu aka bar ni yin harkar fim – Ummi Tarore

Sai bayan mutuwar babana da aurena ne na samu aka bar ni yin harkar fim – Ummi Tarore

"Har yanzu Ina fuskantar ƙalubale a harkar fim" Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Aisha Adam Muhammad da aka fi sani da Ummi Tarore wata matshiyar da ta ke tashe a masana'artar fim ta Kannywood, a tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji tarihinta da kuma yadda a ƙasa da shekaru biyu ta yi finafinai fiye da 25. Ku biyo mu don jin yadda hirar za ta kasance: MANHAJA: Gabatar mana da kanki. UMMI TARORE: Sunana Aisha Adam Muhammad da aka fi sani da Ummi Tarore, an haife ni a shekarar 2002 a Jos, amma a Kano muke…
Read More
Ina mamakin yawaitar mutuwar auren jarumai mata – Pete Edochie

Ina mamakin yawaitar mutuwar auren jarumai mata – Pete Edochie

Daga AISHA ASAS Shahararren jarumin da ya ga jiya, ya ga yau, Pete Edochie, ya bayyana kaɗuwarsa kan yadda auren jarumai mata ke mutuwa ba ƙyaƙyautawa. Jarumin ya yi wannan ƙorafin ne a wata tattaunawa da ya yi a shirin nan na ‘WithChude’, inda ya bada misali da auren jaruma Chioma Akpotha, jaruma Ireti Doyle da kuma jaruma Tonto Dikeh, waɗanda igiyoyin aurensu suka tsinke. "Idan ka je masana'antarmu a yanzu, za ka tarar mafi yawan matanmu da suka yi aure a shekaru biyu zuwa uku baya, auren ya mutu. Na kuma yi matuƙar kaɗuwa da jin mutuwar auren Chioma…
Read More
Asalin Birnin Timbuktu

Asalin Birnin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tombouctou ko kuma Timbuktu, birni a na ƙasar Mali da ke cikin wurare masu daɗɗaɗen tarihi na duniya, saboda haka ne ma a shekarar 1988, Cibiyar Al'adu, Ilimi da Kimiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta saka shi a sahun wurare mafi tasiri a duniya. Kaburan waliyai da ɗimbin littatafan tarihi a Timbuktu sun ɗaukaka sunan birnin da ke arewacin ƙasar Mali. Daga Timbuktu zuwa Bamako babban birnin ƙasar Mali akwai kimanin kilomita dubu ɗaya.Tairihi ya nuna cewar Abzinawa ne suka kafa wannan gari a cikin ƙarni na 11, yanzu muna ƙarni na 21, kenan Tombouctou…
Read More
Makamashi: Tallafin man fetur

Makamashi: Tallafin man fetur

Tare Da BASHIR MUDI YAKASAI Ga Malam Bahaushe, ma’anar tallafi yana fassara karin maganar nan da ke cewa,”hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka”. Ma’ana, dukkan wani abu na alheri ba ya yiwuwa sai da kama-kama na jama’a, kamar yadda ake yi a lokacin bukukuwa, inda ake yin ajo a tara wa ma’aurata kuɗi, domin tafiyar da biki cikin nishaɗi da walwala. Haka ake tallafa wa mai rauni a cikin jama’a lokacin faɗuwar damina, inda jama’ar gari suke zuwa gonaki, domin tallafawa tun daga sassabe zuwa shuka, noma har izuwa furfure, idan kuma kaka ta yi, a tallafa wajen kwasar amfanin…
Read More
Alaƙar jinin al’ada da zamantakewar aure

Alaƙar jinin al’ada da zamantakewar aure

Daga AISHA ASAS Allah S.W.A ya faɗa a cikin littafi mai tsarki “suna tambayar ka game da haila (al’ada) ka ce masu ƙazanta ne, su nisance mata har sai sun yi tsarki.” A wannan ayar mata suke fakewa suka haramta ko sumbatar mazajensu. A cewar su ko hannu ya haramta miji ya riƙe na matar sa har sai ta yi tsarki. Uwar gida ki sani a lokacin da ki ke al’ada saduwa kawai aka haramta maku. Da yawa mazaje masu mata ɗaya sukan shiga mawuyacin hali a lokacin da matansu ke al’ada wanda kaɗan ne daga cikinsu ke iya riƙe…
Read More
An buƙaci daraktoci su ɗauki aikinsu da muhimmanci a Kano

An buƙaci daraktoci su ɗauki aikinsu da muhimmanci a Kano

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye mni, ya yi kira ga daraktocin sashen wayar da kai na ma'aikatun gwamnati da hukumomi a jihar da su zama masu himma matuƙa wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a kansu. Halilu ya yi wannan kira ne yayin taron fahimtar juna da tsakaninsa da daraktoci da kuma hukumomin da lamarin ya shafa. Ya ce dalilin taron shi ne, don saka wa jami'an ƙaimi da kuma yaba musu dangane da irin ƙwazon da suke yi wajen aiwatar da harkokin gwamnati a ma'aikatunsu mabambanta. Ya ƙara da cewa,…
Read More
Ƙungiyoyin mata sun yi kiran a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai

Ƙungiyoyin mata sun yi kiran a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ƙungiyoyin addini masu zaman kansu na mata sun yi kira da a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai da ƙananan yara a ƙasar. Shugabannin Ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya; Sakatariyar Katolika ta Nijeriya; Ƙungiyar Matan Kirista ta Nijeriya; da kuma Cocin 'Redeemed Christian Church of God' sun yi wannan kiran ne a lokacin ziyarar da su ka kai na bada shawarwari ta hanyar Cibiyar Sadarwa da Tasirin zamantakewa, ga mata a wasu yankuna, tare da kira da a inganci abincin da mata ke ci domin su samu damar bai wa jarirai abinci mai gina…
Read More
Kamfanin Blueprint ya yi rashi

Kamfanin Blueprint ya yi rashi

Daga BASHIR ISAH Kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja ya yi rashin ma'aikaci mai suna Malam Ado Musa wanda aka fi sani da Fancy. Marigayi Musa na aiki da kamfanin Blueprint ne a ofishinsa na shiyyar Kano da ke Tabloid. Ya rasu ne sakamakon fama da rashin lafiya, inda ya bar mahaifinsa da mata biyu da kuma 'ya'ya 12. Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne mai kula da rarraba jaridun Blueprint a ofishin kamfanin na Kano wanda ya ba da gudunmawarsa matuƙa wajen tabbatar da jaridun na karaɗe sassan jihar Kano. Mahaifin marigayin ya bayyana ɗansa a matsayin mai ƙwazo wanda…
Read More
Za a riƙa ƙara farashin fetur bayan tashin Dala – IPMAN

Za a riƙa ƙara farashin fetur bayan tashin Dala – IPMAN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD  Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta bayyana cewa, farashin man fetur zai cigaba da hauhawa a Nijeriya bayan da kuɗin Dala ke ƙara tashi. A wata hira da manema labarai, Shugaban IPMAN na Ƙasa, Chinedu Okoronkwo, ya ce, farashin man fetur ɗin zai cigaba da ƙaruwa muddin Dalar Amurka ta tashi a kasuwar canji. Ya ce, “ya kamata ’yan Nijeriya su fahimci cewa, idan aka cire tallafin man fetur, gwamnati ba ta ƙayyade farashi ba, sai dai yadda kasuwa ta kama. Ana sayen kayan man ne a daloli. Dala tana kusa da Naira 890…
Read More