13
Aug
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wolverhampton ta sanar da naɗa tsohon kocin Bournemouth, Garry O'Neil, a matsayin wanda zai horar da ita. Tuni ya amince da kwantiragin kaka uku, ya kuma maye gurbin Julen Lopetegui. An sanar da raba gari tsakanin ƙungiyar da Lopetegi a Molineu ranar Talata, kwana uku kafin fara kakar firimiya ta 2023/24. O'Neil ya ja ragamar Bournemouth zuwa mataki na 15 a teburin firimiya a bara, daga baya ta kore shi ranar 19 ga watan Yuni. Mai shekara 40, shi ne kocin Wolves na hudu cikin shekara biyu. Zai fara aiki ranar Litinin, lokacin da Wolves za…
