Editor

9513 Posts
Yarjejeniya 11 da Faransa ta ƙulla da ƙasashen Afirka da ta mulka

Yarjejeniya 11 da Faransa ta ƙulla da ƙasashen Afirka da ta mulka

Daga AMINA YUSUF ALI A lokacin da Ƙasar Faransa ke shirin bayar da mulki ga ƙasashen Afrika da ta mulka, ta ƙulla wasu yarjeniyoyi guda 11 tsakaninta da ƙasashen, waɗanda a yanzu ke zama tarnaƙi ga ɗorewar ɗiyaucinsu. Da ma akwai yarjejeniyar da ta haramta ƙasashen rainon Faransa guda 14 ikon haɗin gwiwa na sojoji da wata ƙasar kuma an haramta musu ikon sayen kayan yaƙi a wata ƙasa ta Turai ba tare da sahalewar ƙasar Faransa ba.  Wasu daga cikin ƙasashen Afirka da Faransa ta raina sun haxa da: Mauritania, Senegal,  Mali,  Guinea, Ivory Coast,  Burkina Faso, Benin, Nijar,…
Read More
Yaƙi na shirin ɓarkewa tsakanin ECOWAS da Nijar

Yaƙi na shirin ɓarkewa tsakanin ECOWAS da Nijar

*Ƙungiyar ECOWAS ta umarci dakarunta su yi shirin ko-ta-kwana*Tinubu ya aike da malaman Musulunci Nijar don shiga tsakani*Mu na bin Nijar bashin Naira Biliyan huɗu na lantarki, inji Nijeriya Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daga dukkan alamu matuƙar al’amura ba su sauya ba, yaƙi yana shirin varkewa tsakanin Ƙungiyar Tattalin Arziki ta Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ƙarƙashin jagorancin Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, da sojojin da suke riqe da madafun iko a Ƙasar Nijar bayan sun kifar da halastacciyar gwamnatin dimukraɗiyya a ƙarƙashin jagorancin Mohamed Bazoum, wanda sojojin suka hamɓarar. Hakan ya biyo bayan yadda shugabannin Ƙasashen ECOWAS…
Read More
Likitoci sun janye yajin aiki

Likitoci sun janye yajin aiki

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NARD) ta janye yajin aikin da take gudanarwa tare da ba da tabbacin mambobinta za su koma bakin aiki a wannan Asabar ɗin. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Orji ne ya bayyana haka a ranar Juma'a. “…mun janye yajin aiki. Za a ci gaba da aiki gobe (Asabar) da ƙarfe 8 na safe. Za mu waiwayi matsayar da aka cim ma nan da makonni biyu," in ji Orji a cikin wani gajeren saƙo da ya aike wa jaridar News Point Nigeria. Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da likitocin suka dakatar da aniyarsu…
Read More
An yi jana’izar waɗanda suka rasu a iftila’in masallaci a Zariya

An yi jana’izar waɗanda suka rasu a iftila’in masallaci a Zariya

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum 10 ake fargabar sun riga mu gidan gaskiya sannan da dama sun jikkata sakamakon rikitowar wani ɓangare na ginin Babban Masallacin Zariya da ke Kaduna. Da yake tabbaar da aukuwar iftila'in da ya auku a ranar Juma'a, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce lamarin ya faru ne da la'assariyar wannan rana. Ya ce, “Tun farko, jiya mun lura cewa bangon ginin ya tsage inda aka fara shirin ɗaukar injiniyoyin da za su yi aikin gyara kafin daga bisani wannan iftila'in ya auku." Bayan miƙa ta'aziyya ga 'yan uwan waɗanda suka rasu a hatsarin,…
Read More
AU ta mara wa ECOWAS baya game da ƙudurorinta kan juyin mulkin Nijar

AU ta mara wa ECOWAS baya game da ƙudurorinta kan juyin mulkin Nijar

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU) ƙarƙashin jagorancin Moussa Faki Mahamat, ta ce tana goyon bayan matakan da ECOWAS ta ɗauka kan Jamhuriyar Nijar ɗari bisa ɗari. AU ta bayyana goyon bayan nata ne ga ƙoƙarin da ECOWAS ke yi wajen maido da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar Nijar wadda a yanzu take hannun sojojin juyin mulki. Faki Mahamat ya nuna damuwarsa dangane da rashin kulawar da hamɓararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum ke fuskanta a hannun sojojin da ke riƙe da shi. Cikin sanarwar bayan taron da AU ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Agusta, shugaban ƙungiyar…
Read More
Gwamnan Zamafara ya ƙaddamar da shirin tsaftace muhalli na ZAYOSAP

Gwamnan Zamafara ya ƙaddamar da shirin tsaftace muhalli na ZAYOSAP

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ƙaddamar da shirin tsaftace muhalli na Zamfara Youth Sanitation Programme’ (ZAYOSAP) domin tsaftace babban birnin Jihar Zamfara da kewaye. Bikin ƙaddamar da shirin ya gudana ne ranar Juma'a a tsohon ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Gusau. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan ya jaddada cewa shirin yana daga cikin shirye-shiryen da gwamnatinsa ta ke da su domin tabbatar da tsaftar muhalli da kiyaye yaɗuwar cututtuka a jihar. Wata sanarwar manema labarai da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce an ƙirƙire shirin ne…
Read More
’Yan bindiga sun kashe mutane 21 a Jihar Filato

’Yan bindiga sun kashe mutane 21 a Jihar Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe mutane 21 a Baton da Rayogot da ke gundumar Heipang a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato. Rwang Tengwong, sakataren yaxa labarai na Ƙungiyar Berom Youth Movement, BYM, wata ƙungiyar al’adu da zamantakewa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Jos. Mista Tengwong ya ce harin da aka kai kan al’umomin ya faru ne da ƙarfe 1:26 na safiyar ranar Alhamis, kuma ya yi sanadin jikkata wasu mutane bakwai. Tengwong, wanda ya yi tir da hare-haren…
Read More
Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumar NAYES da sauran hukumomin tsaro a Nasarawa – G.M Labaran Maina

Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumar NAYES da sauran hukumomin tsaro a Nasarawa – G.M Labaran Maina

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Janaral Manaja na hukumar tsaro na gwamnatin jihar Nasarawa wato Nasarawa Egency For Youth Empowerment Scheme (NAYES) a turance, Abdullahi Labaran Maina ya yi kira na musamman ga jami’an hukumar ta NAYES a jihar baki ɗaya su tabbatar suna cigaba da kasancewa jami’an hukumar nagari a duk inda suke gudanar ayyukansu a faɗin jihar. Janaral Manajan, Abdullahi Labaran Maina ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a ofishinsa dake hedikwatar hukumar ta NAYES a garin Lafiya babban birnin jihar ranar Talata na makon nan da ake ciki. Ya…
Read More
Rufe kan iyakokin Nijeriya ya jawo durƙushewar kasuwanci da masana’antu a Arewa – Ɗanpass

Rufe kan iyakokin Nijeriya ya jawo durƙushewar kasuwanci da masana’antu a Arewa – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Rufe kan iyakokin ƙasar nan ya taimaka wajen kassara harkokin kasuwancin al'ummar Arewacin ƙasar nan musamman ma jihar Kano da take cibiyar kasuwanci. Fitaccen ɗan kasuwa ɗaya daga cikin dattawan Arewa, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ne ya bayyana hakan a Kano, inda ya ce sai da suka ja hankalin tsohon shugaban qasa Muhammad Buhari akan kar a rufe kan iyakokin nan na Arewa, suka kuma yi kira akan a buɗe bayan an rufe amma ba a ji ba sai ga shi kasuwanci ya shiga halin ha'ula'i a Kano da Arewa bakiɗaya. Ya yi nuni da…
Read More
Yadda makarantu 79 a Misau ta Jihar Bauchi ke fuskantar ƙarancin malamai

Yadda makarantu 79 a Misau ta Jihar Bauchi ke fuskantar ƙarancin malamai

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Aƙalla makarantu guda 79 ne dake cikin Ƙaramar Hukumar Misau ta Jihar Bauchi suke fuskantar matsanancin ƙarancin malamai masu koyarwa, inda kowacce ɗaya daga cikin waɗannan makarantu take da malami guda ɗaya tal dake karantar da dukkanin darussan ilimi a makarantar sa. Wannan furuci mai ban tsoro da firgitarwa ya fito ne daga bakin Darakta mai kula da lamurran makarantu na Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Bauchi, Korijo Buba Umar a yayin zaman wani zauren tattaunawa na 'yan jaridu na kwanaki biyu da Hukumar Kula da Asusun Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta…
Read More