Editor

9513 Posts
Mourinho ya musanta yunƙurin tunzura shugabannin Roma

Mourinho ya musanta yunƙurin tunzura shugabannin Roma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Roma, Jose Mourinho ya musanta yunƙurin tunzura shugabannin ƙungiyar da wani hoto a shafinsa na Instagram amma ya ce abubuwa ba su daidaita ba. A hoton ana iya ganin Mourinho mai shekaru 60 da ma’aikatansa suna rungumar wani abin da ba a gani bayan Roma ta gaza ɗauko sabon ɗan wasan da zai maye gurbin Tammy Abraham wanda ke ɗauke da rauni. An saka hoton ne a ƙarshen atisayen da ƙungiyar Roma ta yi a ƙasar Portugal mako ɗaya da ya wuce. An ɗauke ɗan wasan gaban Ingila Abraham, mai shekara 25, jim kaɗan bayan…
Read More
‘Yan bindiga sun sace Sarkin Gurku a Jihar Nassarawa

‘Yan bindiga sun sace Sarkin Gurku a Jihar Nassarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Nassarawa ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun ɗauke Sarkin Gurku da iyalinsa. Rundunar ta ce da misalin ƙarfe goma na dare, maharan, waɗanda ake zargin masu satar mutane ne ɗauke da bindigogi suka kutsa fadar mai martaba Sarkin Gurku, mai daraja ta ɗaya, Alhaji Jibrin Mohammed, bayan sun kaikaici lokacin da aka watse daga fada, wadda ke da tazarar kilomita goma da marabar Gurku da ke jikin babbar hanyar da ta tashi daga Abuja ta dangana da Keffi, inda suka tafi da shi da mai ɗakinsa. Kakakin rundunar…
Read More
Wolves ta sallami kocinta Lopetegui

Wolves ta sallami kocinta Lopetegui

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Wolves Julen Lopetegui ya bar ƙungiyar, inda tsohon kocin Bournemouth Gary O'Neil zai maye gurbinsa. Wolves ta ce, ta daɗe da fahimtar cewa Lopetegui, mai shekaru 56, yana son barin ƙungiyar. Ƙungiyar ta kuma ce dukkan vangarorin biyu sun amince da savanin ra'ayi kan wasu batutuwa kuma sun amince cewa kawo ƙarshen kwantiraginsa cikin aminci shi ne mafita mafi kyau". Wolves ta sanar da barin kocin ɗan Sifaniya kwanaki uku kafin a fara gasar firimiya, inda za su kara da Manchester United ranar Litinin. Kulob ɗin ya ce, "an ci gaba da tattaunawa a cikin…
Read More
Idan kina so mijinki ya dinga ganin ƙimarki

Idan kina so mijinki ya dinga ganin ƙimarki

Tare Da AMINA YUSUF ALI Muna tafe da bayani a kan yadda mace ita ma za ta samar wa kanta girma da ƙima a wajen mijinta. Domin a baya mun yi magana aka girmama miji. To kada mu ɗauka namiji ne kaɗai yake buƙatar ƙimantawa da darajtawa a gidan aure. Ita ma mace tana buƙatar a ƙimanta ta. Da wannan nake cewa, a sha karatu lafiya. Kamar yadda muka yi matashiya, ita girmama juna a gidan aure tana da matuƙar muhimmanci. Mace da namiji kowa na buƙatar girmamawa daga ɗanuwansa. Kuma girmama juna tsakanin ma'aurata yana sa zaman auren ya…
Read More
Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

"Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi" Daga ISHAQ IDRIS GUIBI Gabatarwa Harshen Ingilishi yana ɗaya daga cikin manyan Harsunan duniya, da duniya ke taƙama da shi da tinƙaho. Harshe ne da Turawan mulkin mallaka suka ƙaƙaba wa ƙasashe renon Ingilishi. Ƙasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka irin su Nijeriya. Sai dai duk da cikarsa, da batsewarsa da haɗiye wasu harsuna, da gadar wasu harsuna, da satar kalmomin wasu harsuna, yana fama da yunwar wasu kalmomi, da rikicewar kalmomi da ma’anarsu. Har zan iya cewa Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi marasa shirbici da ruɗarwa.…
Read More
Wakilcin Tarauni: Kotu ta maye gurbin Yarima da Kawu

Wakilcin Tarauni: Kotu ta maye gurbin Yarima da Kawu

Daga BASHIR ISAH Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe mai zamanta a Kano, ta tsige ɗan Majalisar Wakilai na ƙasa mai wakiltar Mazaɓar Tarauni, Honorabul Muktar Umar Yarima na Jam'iyyar NNPP bayan da ta same shi da laifin amfani da takardar bogi. Kotun ta ce takardar shaidar kammala makarantar firamare da Yarima ya gabatar ta jabu ce kamar yadda ta bayyana a zaman shari'ar da ta yi a ranar Alhamis. Don haka Kotun ta buƙaci hukumar zaɓe INEC da ta bayyana ɗan takarar Jam'iyyar APC a mazaɓar, Honorabul Hafizu Ibrahim Kawu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen sannan ta miƙa masa shaidar…
Read More
Jaruman matan Arewa

Jaruman matan Arewa

Daga AYSHA ASAS Duk da kasancewar mata masu rauni, waɗanda aka halicce su a ƙarƙashin ikon namiji, wannan ba ya shafi ɓangaren kasancewar su masu ilimi da kuma kaifin basira ba. Da yawa daga cikin maza kan yi wa mata gurguwar fahimta a baya, su na kallonsu irin kallon da manya ke yi wa yara ƙanana, don haka suke ganin ba ta yadda mace zata iya yin abinda namiji ya yi bare ma har ta fi shi. Mace halitta ce da aka yi ta ƙarƙashin ikon namiji, sai dai tana tattare da baiwa da dama da ba kasafai ake samu…
Read More
Juyin mulki a Nijar ya tono gara daga rami

Juyin mulki a Nijar ya tono gara daga rami

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wata sabuwar fitina da ke ƙoƙarin kunno kai a Afirka, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a ranar 26 ga watan Yuni, shi ne tasirin yaƙin cacar baka tsakanin Rasha da Amurka, sakamakon yaƙin Ukraine da Rasha da manyan ƙasashen duniya suke hassalawa. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ya kira wani taron gaggawa inda suka tattauna kan yadda za a ɓullowa wannan juyin mulki da ke neman durƙusar da mulkin Dimukraɗiyya a yankin. Daga cikin ƙudirorin da taron…
Read More
Zubar da jini a Arewa: Ya kamata mu farka!

Zubar da jini a Arewa: Ya kamata mu farka!

Abin da ya ke faruwa a kasar nan har wasu su ke daukarsa tamkar wasa, ko abin nishaɗin da za a zauna a bakin layi a tattauna cikin raha, ko da rabin kwatankwacinsa ya ke faruwa a wata ƙasar wacce ke da cikakkun mutane masu hankali da sanin ciwon kai, da wuya su yarda a kai wani lokaci ba su sauke duk wani shugaba da ke da hannu ko sakaci a cikin abin ba. A yanzu haka mutanen da ke kallon labaran halin da muke ciki suna nan suna mamakin ko mu waɗanne irin mutane ne? Ta yaya za a…
Read More