Jaruman matan Arewa

Daga AYSHA ASAS

Duk da kasancewar mata masu rauni, waɗanda aka halicce su a ƙarƙashin ikon namiji, wannan ba ya shafi ɓangaren kasancewar su masu ilimi da kuma kaifin basira ba.

Da yawa daga cikin maza kan yi wa mata gurguwar fahimta a baya, su na kallonsu irin kallon da manya ke yi wa yara ƙanana, don haka suke ganin ba ta yadda mace zata iya yin abinda namiji ya yi bare ma har ta fi shi.

Mace halitta ce da aka yi ta ƙarƙashin ikon namiji, sai dai tana tattare da baiwa da dama da ba kasafai ake samu a tare da namiji ba. Masana sun tabbatar da cewa, mace na da kaifin basira da lokuta da dama ta rinjaye ta namiji, haka kuma akwai wasu baiwa da aka ware musamman domin mata, waɗanda ba kasafai ake samun su a wajen maza ba, kamar misali, baiwar iya yin mabambantan ayyuka a lokaci guda.

Abin nufi a nan shi ne, idan mace ta samu dama, za ta iya yin kwatankwacin abinda namiji ya yi ko ma fiye, amma fa a ɓangaren abinda ya shafi basira. Wannan ne ya sa ake iya samun mata a cikin kowanne lungu da saƙon da maza suka shiga.

Da wannan ne shafin Gimbiya ya ware wannan satin don kawo maku wasu daga cikin matan Arewa da suka yi abin gani, suka zama kallabi tsakanin rawuna, takai suka taka rawar gani da duniya ta san da su a matsayin jaruman matan Arewa. Idan kun shirya, zan ce a sha karatu lafiya:

Amina J Muhammed

Ɗaya daga cikin matan Arewa da ta cancanci a kira ta da jaruma, macen da ta kafa tarihi a duniya, macen Arewa ta farko da ta taka matsayin da ta taka. Hajiya Amina Muhammed, mataimakiyar Sakatre Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya. ‘Yar Arewa da ta fito daga Jihar Jigawa.

Kafin ta kai ga wannan matsayi, Hajiya Amina ta yi zama minista ta ƙasa, inda ta riƙe muqamin Ministar Muhali ta Ƙasa, wanda hakan na nufin ta ja ragamar ƙasarmu mai albarka a ɓangaren kula da sha’anin muhalinmu.

Muqamin minista da ta riƙe kuwa ya biyo bayan wasu muƙamai daban-daban da ta riƙe a vangarorin ilimi da sha’anin al’umma.

Da wannan za mu iya cewa, Amina Muhammed ta cancanci ta shiga jerin jaruman mata da Arewa take alfahari da su, ko ince ya kamata ta yi alfahari da ita fiye da saura, kasancewar a duk inda ta shiga, tana ratsawa ne da tambarin da ke nuna ita ‘yar Arewa ce, wato dai shigar gargajiya da har yau matsayinta bai sa ta ajiyeta ba.

Pauline Tallen

Mace ta farko a tarihin Arewacin Nijeriya da ta tava riƙe muƙamin mataimakiyar gwamna, ‘yar asalin Jihar Filato da ta taɓa riƙe muƙamin ƙaramar ministar kimiya da fasaha a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Pauline na ɗaya daga cikin matan da suke da jarumtar fitowa gogayya da maza wurin neman abinda aka fi sani da kujerar maza, wato ta fito takarar gwamna, duk da cewa, bata samu nasara ba. Sannan ta riqe muƙamin ministar harkokin mata a gwamnatin da ta shuɗe.

Zainab Bulkachuwa

Mace ta farko da ta zama shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Nijeriya. Hajiya Zainab ta fito daga Arewa a garin Nafaɗa da ke cikin Jihar Gombe.

Za mu iya cewa, Hajiya Zainab ta zama zakaran gwajin dafi a ɓangaren shari’a, domin kafin nan ta taɓa riƙe muƙamin Cif Majistare kafin ta tafi Babbar Kotu a sheakarar 1987.

Ba anan ta tsaya ba, Hajiya Zainab ta taɓa riƙe muqamin Babbar Mai Shari’a ta babar kotun Jihar Gombe. Kafin ta zama mai shari’a a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Birnin Tarayya, Abuja.

Da wannan kawai na san mai karatu ma idan na bar shi da hisabin wannan baiwar Allah, zai iya tabbatar da ta cancanci a kira ta da jarumar Arewa.

Maryam Aloma Mukhtar

Ita ce mace ta farko da aka fara kira Mai Shari’a a Babban Kotun Jihar Kano, kuma Mai Shari’a mace ta farko a Kotun Ƙoli ta Ƙasar Nijeriya.

‘Yar asalin Jihar Adamawa da sunanta ya fito a matsayin ta farko a muƙamai da dama da mata suka tava riƙewa.

Tabbas Maryam Aloma ta cancanci jinjina kuma ta zama jarumar Arewa da ta kafa tarihi. Mai karatu zai amince da hakan idan ya bi tarihinta daki-daki, ya ga irin salon rawar da ta taka mai matuqar burgewwa, kamar zama Alƙalin Alƙalai, da sauran su.

Farfesa Ruƙayya Rufa’i

Farfesa Ruƙayya dai bata buƙatar gabatarwa, matsayinta kawai na farfesa ma zai tabbatar maka da kogin ilimi ce ita, ‘yar Arewa da ke kishin al’ummarta. Ministar Ilimi a zamanin mulkin Goodluck Johathan.

A ɓangaren gudunmuwa ga Arewa, Farfesa Ruƙayya ta bayar da muhimmiyar gudunmuwa a cigaban ilimi a Arewa da ma Nijeriya bakiɗaya. Sannan tsayawa bayyana rawar da ta taka a ilimin ‘ya’ya mata wani dogon zance ne.

Yar asalin Jihar Jigawa ce da ta taimaki ɗimbin mutane da iliminta, musamman ma mata. Ta riƙe muƙamin Kwamishiniyar Harkokin Lafiya ta jihar Jigawa. Bayan ta zama farfesa ce ta sake riqe muƙamin Kwamishiniyar Ilimi da Kimiyya da Fasaha, duk dai a mahaifar tata Jigawa.

Ba a iya nan ta tsaya ba, Farfesa Rukayya Rufa’i ta zama Ministar harkokin Ilimi ta ƙasa a shekarar 2010, wanda za mu iya cewa, duniya ta sheda irin namijin ƙoƙari da jarumar matan Arewa, Farfesa Rukayya Rufa’i ta yi.

Farfesa Zainab Alƙali

Jajirtacciyar marubuciya macen Arewa da ke rubutu cikin harshen Ingilishi, wadda ta yi amfani da hikima wurin sarrafa alqalaminta wurin kai koken matan Arewa, kasancewar rubutunta ya fi karkata kan rayuwar matan Arewa da kuma muhimmancin ilimin ‘ya mace.

Madalla da samun irin su Farfesa Zainab Alƙali, madalla da zama ɗaya daga cikin matan da suka fito daga Arewacin Nijeriya.

Saudatu Usman Bungudu

Ɗaya daga cikin matan Arewa jarumai akwai Hajiya Saudatu Usman, ‘yar asalin Jihar Zamfara a Ƙaramar Hukumar Bungudu. Ta taka muhimmiyar rawa wurin samar da cigaba ga matan Jihar Zamfara, wanda har ya kai ta riqe muƙamin Ministan Harkokin Mata da Ci gaban Tattalin Arzikin Najeriya.

Duk da cewa Hajiya Saudatu bata ɗauki tsayin lokaci a wannan matsayi ba, kasancewar shekara ɗaya tal ta samu yi a kujerar ta Ministan Harkokin Mata da Ci gaban Tattalin Arzikin Najeriya, amma ta yi abin gani da ya dace mu sanya ta a jerin matan Arewa jarumai.
Kafin nan, ta tava riqe muƙamin Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ƙananan yara ta Jihar Zamfara, inda ta tsaya tsayin daka wurin yin mai yi wa kan kare haƙƙoƙin mata da ƙananin yara, musamman ma abinda ya shafi cin zarafi ta fuskar fyaɗe.

Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq minista ta farko da ta fara shugabantar sabuwar Ma’aikatar Jinkai da Ci gaban Al’umma da Kare Afkuwar Bala’i a Nijeriya, wadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa.

Kafin wannan, Hajiya Sadiya ta yi zama Kwamishiniyar Hukumar da ke Kula da ‘Yan Ci Rani da ‘Yan Gudun Hijira. Kuma ta yi zama Ma’aji ta Jam’iyyar APC ta ƙasa.

‘Yar Jihar Zamfara ce da ta yi gwaninta a ɓangarori da dama, musamman ma a fagen tausayin talakawa da bayar da taikmako ga waɗanda suka cancanta.

Zainab Shamsuna Ahmed

‘Yar asalin Jihar Kaduna Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ta shiga jerin jaruman Arewa ne da muƙaman da ta riqe da kuma irin jajirccewar da ta yi.

Hajiya Zainab ta riƙe muƙamai masu dama, waɗanda suka haɗa da; darakta a kamfanin zuba jari na Nijeriya, ƙaramar ministar kuɗi, shugabar hukumar NEITI da kuma Ministar Kuɗi ta Ƙasa a ƙarƙashin mulkin Muhammadu Buhari.

Hadiza Bala Usman

Hajiya Hadiza Bala Usman ta yi fice wurin fafutukar kare haqqin mata. Mai karatu zai amince da zance na idan ya yi waiwaye lokacin da iftila’in da ya sauka ga yara ‘yan matan Chibok, inda ta yi ruwa da tsaki wurin ganin an yi yadda ya kamata ga ‘yan matan.

Ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa gangamin ‘BringBackOurGirls’, gangamin da ya yi tasiri matuƙa.

Hajiya Hadiza Bala Usman ta riqe muƙamin shugabar Hukumar Kula da Tasoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya, wato NPA. Macen Arewa kuma ɗaya daga cikin jaruman matan Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *