Wakilcin Tarauni: Kotu ta maye gurbin Yarima da Kawu

Daga BASHIR ISAH

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe mai zamanta a Kano, ta tsige ɗan Majalisar Wakilai na ƙasa mai wakiltar Mazaɓar Tarauni, Honorabul Muktar Umar Yarima na Jam’iyyar NNPP bayan da ta same shi da laifin amfani da takardar bogi.

Kotun ta ce takardar shaidar kammala makarantar firamare da Yarima ya gabatar ta jabu ce kamar yadda ta bayyana a zaman shari’ar da ta yi a ranar Alhamis.

Don haka Kotun ta buƙaci hukumar zaɓe INEC da ta bayyana ɗan takarar Jam’iyyar APC a mazaɓar, Honorabul Hafizu Ibrahim Kawu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen sannan ta miƙa masa shaidar lashe zaɓen nan take.

Idan za a iya tunawa, yayin babban zaɓen da ya gabata Baturen Zaɓen na shiyyar Tarauni, Garba Galadanchi, ya bayyana Yarima na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓe da ƙuri’u 26,273, yayin da Kawu na jam’iyyar APC ya rufa masa baya da ƙuri’u 15,931.

Sai dai daga bisani Kawu ya shigar da ƙara kotu inda ya ƙalubalanci nasarar da Yarima ya samu inda ya yi iƙirarin an tafka maguɗi a zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *