Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

“Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi”

Daga ISHAQ IDRIS GUIBI

Gabatarwa

Harshen Ingilishi yana ɗaya daga cikin manyan Harsunan duniya, da duniya ke taƙama da shi da tinƙaho. Harshe ne da Turawan mulkin mallaka suka ƙaƙaba wa ƙasashe renon Ingilishi. Ƙasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka irin su Nijeriya. Sai dai duk da cikarsa, da batsewarsa da haɗiye wasu harsuna, da gadar wasu harsuna, da satar kalmomin wasu harsuna, yana fama da yunwar wasu kalmomi, da rikicewar kalmomi da ma’anarsu. Har zan iya cewa Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi marasa shirbici da ruɗarwa.

Wannan maƙala za ta taɓo wasu daga cikin ɓangarorin da Harshen Ingilishi ya gaza.
Yunwar Wakilin Suna
Wakilin Suna, Jam’i kuma Wakilan Suna, kalmomi ne da ke wakiltar Suna a cikin Jimla. Misali, Ni, Kai, Ke, Shi, Ita Mu, Ku, Su.

Manufa ita ce, su waɗannan kalmomi su ne sukan wakilci Suna, a inda Sunan bai samu damar fitowa ba, wani lokaci suna fitowa tare da Sunan domin fayyace Jinsin sunan ko Jam’insa.

Misali:
Malam Is’haq Ya je gidan Rediyo
Ya je gidan Rediyo.
A nan kalmar Ya ita ke wakiltar Sunan Is’haq, namiji, Tilo, na uku.
Ni — Wakilin Suna na farko tilo na wanda yake magana.
Kai —Wakilin Suna na biyu tilo na wanda ake magana da shi
Ke —–Wakilin Suna na biyu tilo na wacce ake magana da ita.
Shi —-Wakilin Suna na uku tilo na wanda ake magana a kansa namiji
Ita —–Wakilin Suna na uku tilo na wacce ake magana a kanta mace.
Mu —–Wakilin Suna Jam’i na farko na waɗanda suke magana.
Ku ——Wakilin Suna Jam’i na biyu na waɗanda ake magana da su.
Su ——-Wakilin Suna Jam’i na uku na waɗanda ake magana a kansu.

Allah Ya albarkaci Harshen Hausa da waɗannan Wakilan Suna amma Harshen Ingilishi ba shi da wadatattun Wakilan Suna haka birjik.

Misali, idan na shiga ajin da nake koyarwa, a makarantar Sakandare, ɗalibai suka mi}e suka gashe ni, a harshen Ingilishi, zan dubi ɗaliban gabaɗayansu in ce THANK YOU, YOU CAN SIT DOWN.

Manufa a nan, Kalmar Wakilin Suna ta YOU abin da ake kira da Ingilishi, PRONOUN, tana nufin duka ‘yan ajin, ko ɗaliba mace tilo, ko ɗalibi namiji tilo. Duk a harshen Ingilishi Wakilin Suna ɗaya ke wakiltarsu.

ƙarin misali:
You – Kai namiji
You – Ke mace
You – Ku maza da mata/Jam’i
You – Ku duka ‘yan aji.
Amma a Harshen Hausa idan na shiga ajin, cewa zan yi KU idan ina magana da gabaɗayan ajin.
KE idan ina magana da wata ɗaliba mace a ajin.
KAI idan ina magana da wani ɗalibi namiji a ajin.
A nan da Harshen Hausa da na Ingilishi, wanne ne ya tsere wa wani ɓangaren wadatattun kalmomi?
Ka ga duk ƙoshin Harshen Ingilishi, yana yunwar bambance KAI da KE da KU.

Rikicewar Furucin Ingilishi.
A Harshen Ingilishi akwai shirbici a furucin sautukan /C/ da /K/ da /S/ da /Ch/
Ana mayar da CA ta zama sautin KA, misali CAPITAL ko CANTEEN
Ana mayar da CH ta zama sautin KA, misali CHARACTER
An ƙyale K a matsayinta, misali KIOSK.
Ana mayar da CH ta zama sautin CH, misali CHAPTER
Ana mayar da CE ta zama sautin SE, misali SENTIMENTAL
Ana mayar da CE ta zama sautin SE, misali CENTRAL
A Harshen Hausa, idan S ce, S ce. Idan C ce, C ce. Idan K ce, to K ɗin ce. Ba sa rikiɗewa ko rikicewa.

Yunwar ɗafa Goshi da Munafuncinsa.
Harshen Hausa yana da ɗafe iri uku. Ɗafa goshi, da ɗafa ciki da ɗafa ƙeya. Harshen Ingilishi kuwa duk ƙoshinsa da bunƙasarsa, ɗafa goshi da ɗafa ƙeya kawai yake da su, ba shi da ɗafa ciki.

Ɗafi, wani ƙari da da ake yi wa kalma a goshinta, ko a tsakiyarta, ko a ƙeyarta.

Misalin ɗafa goshi Ba. Sai a ɗafa wa Hausa, don zama BAhaushe.
Ɗafa ciki kuwa, misali Wa, sai a ɗafa ta a cikin Dutse, wato DuWAtsu
Ɗafa ƙeya kuma, sai a ɗafa yayya a ƙeyar kalmar ƙi, ta zama ƙiYAYYA.
A Ingilishi kuwa, za a yi ɗafa goshin IN a kalmar available domin zama Inavailable da ke nufin korewar AVAILABLE. Available na nufin AKWAI, INAVAILABLE kuma na nufin BABU.
Saboda haka kamata ya yi duk kalmar da aka ɗafa mata IN a goshinta ta zama ta KOREWA ce wato babu abin ko kuma ba zai yiwu ba.
Idan ka lura da kyau da motoci tankokin ɗaukar man fetur, za ka ga an rubuta a bayan tankin INFLAMABLE daga FLAMEABLE da FLAME.
Flame na nufin wuta ko gobara ko harshen wuta.Flameable kuma na nufin wuta na iya tashi. Maimakon ɗafa goshin IN ɗin ya kore tashin wutar, wato ya nuna wutar ba za ta tashi ba, ko kuma babu wutar kamar yadda ɗafen ya yi aiki a INAVAILABLE, sai ga shi yana nuna yiwuwar gobarar.
In ka ce INCONSISTENCE korewa ce
In ka ce INCOMPETENCE korewa ce
Amma idan ka ce INFLAMABLE ba korewa ba ce.
Wannan matsala ce ga Harshen Ingilishi, saboda ba ya magana ɗaya tamkar munafuki. Nan ya ce kaza, a can ya canza.
A Ingilishi ne za a ce He KICKED the bucket. Maimakon a fassara Jimlar da ya SHURI bokiti, sai aka ce a’a wai ana nufin ya MUTU ke nan.
A Ingilishi ne za a ce COCKTAIL PARTY, maimakon a fassara jimlar da dabdalewa ta BINDIN ZAKARA, sai aka ce a’a dabdalewar ce kawai ake nufi idan ka halarta da ƙyar ka ga ko ƙeyar Zakara a wajen ballantana bindinsa.
A Ingilishi ne za a ce:
He who sings is a Singer
He who teaches is a Teacher
Amma me za ka cewa
He who prays?
Idan ka ce a Prayer ka rikito.
Me ya sa a Ingilishi za a iya cewa:
A vegeterian eats vegetables
Amma ba za a iya cewa
A humanitarian eats humans ba?
Kalmar OVERLOOK da ta OVERSEE akasin juna ne a Ingilishi.
Overlook na nufin ka kawar da idonka daga abu.
Oversee na nufin ka sa idonka akan abu.
Alhali da kalmar LOOK da ta SEE duk ma’anarsu ɗaya.
Wannan ai shirme ne.
A Ingilishi ne a yau za a ce maka ‘The weather is as hot as HELL today’
A gobe a ce maka ‘The weather is as cold as HELL today’
Fassarar HELL dai Jahannama kenan. Me ya ha]a COLD wato tsananin sanyi da zafin jahannama kuma? Yaushe sanyi ya zama jahannama? Wannan sai a Ingilishi.
A Ingilishi akwai MANKIND amma babu WOMANKIND alhali Woman ke haihuwar Man.

Kammalawa
Waɗannan su ne kaɗan daga cikin ɗinbin matsalolin da suka dabaibaye harshen Ingilishi da ya sanya a kullum ba mu iya shi ba, kuma ɗalibanmu ke ta fa]uwa jarabawarsa. Shi yake hana yawancin ‘ya’yanmu shiga jami’a. Munafikin Harshe, ga ƙoshi ga kwanan yunwa.

Ishaq Idris Guibi, malami ne a Sashen Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kaduna
[email protected]
08023703754/08104884633