Juyin mulki a Nijar ya tono gara daga rami

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wata sabuwar fitina da ke ƙoƙarin kunno kai a Afirka, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a ranar 26 ga watan Yuni, shi ne tasirin yaƙin cacar baka tsakanin Rasha da Amurka, sakamakon yaƙin Ukraine da Rasha da manyan ƙasashen duniya suke hassalawa.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ya kira wani taron gaggawa inda suka tattauna kan yadda za a ɓullowa wannan juyin mulki da ke neman durƙusar da mulkin Dimukraɗiyya a yankin.

Daga cikin ƙudirorin da taron ya cimma akwai batun cewa matuƙar sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar ba su sake tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum da mayar da shi kan kujerarsa cikin wa’adin makonni biyu ba, ƙasashen ƙungiyar za su ɗauki dukkan matakan da suke ganin sun dace ko da ya haɗa da amfani da ƙarfin soja, domin mayar da shi kan kujerarsa.

Tare da tabbatar da ganin an kama sojojin da ke da hannu a wannan juyin mulki don a hukunta su. Sannan har wa yau qungiyar ta sanar da rufe iyakokin ƙasar ta sama da ta ƙasa tsakanin dukkan ƙasashen ƙungiyar, wanda ya haɗa har da dakatar da sufurin jiragen sama daga cikin ƙasar zuwa wajenta, ko daga waje zuwa ciki. Da kuma dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasar Nijar da mambobin ƙungiyar ta ECOWAS, da dakatar da duk wani tallafi da ƙasar ke samu daga ’yan ƙungiyar.

Sai dai bayan fitar da waɗannan ƙudirori da aka gabatar da su ga shugabannin juyin mulkin ta hannun shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya na ƙasar Chadi, gamayyar shugabannin ƙasashen Gini, Mali, da Burkina Faso, waɗanda su ma sojoji ne da suka yi juyin mulki a qasashen su, sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa suna masu nuna goyon bayansu ga shugabannin sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, suna jaddada aniyarsu ta kare ’yancin ƙasar da jama’arta. A fakaice sun ƙalubalanci shugabannin ƙasashen Afirka kan matakan da suka yi barazanar ɗauka.

Abin takaici ne ƙwarai ganin yadda tasirin rikicin Rasha da Ukraine ya fara gangarowa yana shafar siyasar ƙasashen Afirka, bayan ƙalubalen tattalin arziki da rikicin ya haifar wa ƙasashen. Kuma lallai idan har ba a yi aiki da hankali ba, ƙasashen Amurka da Rasha za su mayar da ƙasashen Afirka sansanin yaƙin da ba su samu damar gwabzawa gaba da gaba a ƙasashen su ba. A dalilin haka za su halaka mana mutane, kuma su lalata mana ƙasa, su sace dukiyar mu su ƙara gaba.

Abin mamaki, a yayin wata zanga zangar nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulkin, an rawaito wasu ‘yan ƙasar ta Nijar sun ɗaga tutar Rasha suna bayyana amincewarsu da ita, yayin da aka kai hari kan ofishin jakadancin ƙasar Faransa da ta nuna rashin amincewa da wannan juyin mulki, har ma aka sa wuta kan wani sashi na ginin ofishin.

A yayin haɗa wannan rubutu, tuni ƙasashen Faransa, Amurka da Italiya sun fara kwashe wasu ’yan ƙasashen su da ke aiki a Nijar ɗin, don gudun vallewar rikici a ƙasar. Wannan mataki nasu na zuwa ne biyo bayan watsi da buƙatun ƙungiyar ECOWAS da sojojin suka yi.

A yayin da ake sa ran babban wakilin ƙungiyar ECOWAS mai shiga tsakani, kuma tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar zai tafi Nijar ɗin domin ganawa da shugabannin sojojin a Nijar, tuni Nijeriya ta datse wutar lantarki da ta ke samarwa ƙasar, abin da ya fara jefa al’ummar ƙasar cikin wani mawuyacin hali, musamman game da abin da ya shafi masu sana’o’i da kasuwanci.

Abin da ke nuna alamun idan ba Allah ne ya kiyaye ba, akwai alamun ɓallewar rikici a ƙasar, da ke da tsohuwar alaƙa mai ƙarfi tsakanin ta da Nijeriya ta fuskar al’adu, tarihi, da cinikayya. A kan haka ne ita ma marubuciya Rahama Abdulmajid mai sharhi kan harkokin siyasa da zamantakewa ta wallafa wani dogon nazari da ta yi a shafinta na Facebook, domin ankarar da ’yan Nijeriya da shugabanni game da ƙalubalen da hakan zai iya haifarwa. Na kawo sharhin nata a nan ƙasa, domin dacewar hakan ta fuskar ilimi da amfanin da za mu ƙaru da shi daga bayananta.

Da farko dai haɗin kan ƙasashen Gini, Mali Burkina Faso da Nijar ba wani abin tashin hankali ba ne, idan aka yi la’akari da cewa suna barazana ne ga ƙasashe 11 da ke da goyon bayan sauran ƙasashen AU kusan 30.

Abu na biyu kada a manta cikin kasashe 11 nan fa akwai muƙa-muƙan ƙasashe irin Nijeriya wadda ba kawai ƙarfin tattalin arziki ta fi sauran ba, har ma da katafaren ƙarfin soji, inda a cikin shekaru 10 da suka gabata matsalolin rashin tsaro da Nijeriyar ta fuskanta ya tilasta ta sake ƙarfafa sojojinta da sabbin makamai da dabarun da kusan babu wata ƙasar Afirka da ta same su a wannan shekarun idan ka ɗauke ƙasar Masar. Sai kuma kasancewar ita Nijeriyar ta fi su kusa da Nijar sannan tana cike da fushin kashe ahalinta da sojojin ƙasashen Burkinan suka yi, dama girma kawai ta ci.

Abu na uku shine ƙarfin soji da tattalin arzikin waɗannan ƙasashen na iya barinsu da cika baki ne zalla. Babban misalin da zai nuna naƙasun kasashe ukun da ke mara wa sojojin Nijar baya shine ko a lokacin da suke zaman ƙalau idan aka buƙaci gudunmuwar sojojin Afirka wajen wanzar da zaman lafiya dukkansu ukun basa iya haɗo sojojin da suka haura 900, shi ma da siɗin goshi ga rashin kayan aiki, sai uban sabbin kayan kaki na soja (Camouflage).

Abu na huɗu, tambaya ce. Waye ya ce musu su Rasha ke buƙata? Ƙasashen da Rasha ke matuƙar buƙata a Afirka ta Yamma suna cikin ƙasashe 11 da suka saura, su ke da abinda za su iya bai wa Rashan dangin kuɗin hayan soja ko diflomasiyya su kuma waɗannan ƙasashen suna ƙarƙashin mulkin farar hula ne da ke mara wa Rasha baya a yaqin Ukraine da abin da ta fi buƙata wato qarfin tattalin arziki da kasuwanci ba karɓar sadakar makamai a lokacin da ita ma tana buƙata a gida ba.

Abu na biyar shi ne shugabannin ƙasashen da ake son fafatawar da su za su yi faɗan a mutu ne, don kare mulkinsu na farar hula domin idan suka ji tsoron barazanar ƙananan ƙasashen suna nufin bai wa sojojin nasu ƙasashen damar yi musu rashin daraja?

Haramun giya a gidan liman! Ba za su bar hakan ta faru ba, ko da kuwa hakan na nufin su saye Rasha da abinda babu a Bukina Faso, Mali, da Gini, hasali ma ƙasar Senegal kaɗai na iya zane waɗannan maƙwabtan nata ta bar Nijeriya ta ji da Nijar ɗin su.

Abu na shida shi ne sojojin ƙasashen da suka janyo wannan matsalar har aka yi musu koran kare daga su Mali ɗin suna nan suna watangaririya a wannan yankin da kayan aikinsu da asirin ƙasashen na gaske, da ba don ma cutar munafurci da ke damun Faransa ba da lallai ta nuna musu iyakarsu, amma yanzu ga dama ta samu a munafurce za ta bai wa qasashen da ke gaba da tsofaffin masu masaukin baƙinta asirin lagon waɗannan ƙasashen da ta sani don a musu haddi.

Abu na bakwai shi ne, ƙasashen da kan taya Rasha hayagaga irinsu China duk basu da haja da muradu a waɗannan ƙasashe masu fama da buƙatu, don haka za su zamo masu sasanta rikici ne a fili, sannan masu sayar da fasaha ga me kuɗin saye.

Waɗannan kaɗan ne daga ababen da ka iya bai wa ƙasashen ECOWAS dariya da wannan barazanar ta miskinan qasashen Gini, Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar. Amma ni damuwata biyu jal suke.

Na ɗaya, barazanar na iya sanya a mai da lamarin yaƙi don kare mutuncin manyan ƙasashe daga qananan ƙasashe, domin ba fa za su ja da baya a ce sun ji tsoron waɗannan ƙasashen ba ne, kazalika ba za su bari barazanar ta bai wa sojojin ƙasashen su ƙwarin gwiwa ba ne.

Na biyu, turawa na kiran yaƙin Ukraine da alamomin Yaƙin Duniya na 3, wanda kowa ya san a yaƙin duniya na ɗaya da na biyu lokacin Afirka na matsayin babbar baiwar turawa, masu yaqin sun yi amfani da sojojin Afirka a matsayin sulke da garkuwar kare ƙirjin ubangijin Afirka bature daga harsashi kafin ya shiga Jamus ya rusa masu bore.

A wannan karon da yake Afirka na da je-ka na-yi kan ‘yanci dama ce ta samu na su rago hayaniyar yaƙin a yankinsu, su kawo shi wajen tsofaffin bayin su, kuma su je hutun rabin lokaci. Kuma za su sami wannan damar ne a sauƙaƙe ta hannun sojoji masu bore, ko juyin mulki.

Ba ma fatan ganin yaƙi ya valle tsakanin Nijeriya da Nijar, ko wasu ƙasashen Afirka, saboda kuwa ita fitina idan ta tashi ba a san iya inda za ta tsaya ba, kuma ba a san wanda za ta shafa ba. Muna da ‘yan uwa, masoya, surukai, da abokan zumunci da dama a Nijar, ba za mu so ganin wani abu ya shafe su, ko kuma ƙasar su ba.

Kamar yadda mawaƙin nan marigayi Shatan Nijar Abdou Gawo Filinge ke faɗa ne cikin wata waƙarsa ta Nijeriya da Nijar duk ɗai suke, da muke ji tun muna yara, inda yake cewa ‘Abin da yat taɓa hanci idanu fa ruwa sukai.’