Zubar da jini a Arewa: Ya kamata mu farka!

Abin da ya ke faruwa a kasar nan har wasu su ke daukarsa tamkar wasa, ko abin nishaɗin da za a zauna a bakin layi a tattauna cikin raha, ko da rabin kwatankwacinsa ya ke faruwa a wata ƙasar wacce ke da cikakkun mutane masu hankali da sanin ciwon kai, da wuya su yarda a kai wani lokaci ba su sauke duk wani shugaba da ke da hannu ko sakaci a cikin abin ba.

A yanzu haka mutanen da ke kallon labaran halin da muke ciki suna nan suna mamakin ko mu waɗanne irin mutane ne?

Ta yaya za a zo har cikin gida kashe dan Adam bai yi laifin komai ba, ko a ɗauke shi kamar dabba a ɗaure shi a daji, ‘yan uwanshi da danginshi suna tallar ɗan takarar da ba mamaki yana kan mulki tazarce yake nema, yana cikin waɗanda suka kasa taɓuka komai a halin da ƙasa take ciki

Ba su tunanin matsalar da ta kashe makwabcinsu yau ita ce matsalar da za ta dawo ta kashe su gobe, masifar da ta hana ‘ya’yan wasu zuwa makaranta yau ita ce masifar da za ta hana ‘ya’yansu zuwa makaranta gobe, mutane da hannunsu suna shuka matsalolin da za su hallaka kansu da kansu.

Ba wanda ya hana kowa ya tallata ɗan siyasa, domin wasu hanyar cin abincinsu kenan.

Amma kafin mutum ya jefa ƙuri’a ko ya tallata ɗan takara, ya kamata ya fara fara kallon goben ‘ya’yansa da ‘yan uwansa.

Kada motar da za a ba ka ko babur ko wasu ‘yan kuɗi da ba su kai sun komo ba su sa ka jefa al’ummarka cikin masifar da motoci goma ko babura ɗari ba za su fitar da su ba.

Jinin da ake ta zubarwa yau kana ganin ba wata matsala ba ce kwanansu ne ya ƙare, ƙaddararsu kenan, ta yiwu jinin da za a zubar gobe naka ne

Ya rage naka ka ceci rayuwarka ta hanyar kawar da makaman da ke kashe wasu, domin idan suna nan su ne makaman da za su hallaka ka gobe

Shafi’u Dauda Giwa, marubu ci ne, kuma manazarci a kan al’amurran siyasa. Ya rubuto daga jihar Kaduna.