Shugaba Tinubu ya rantsar da ministocinsa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Nyesom Wike da wasu 44 a matsayin ministocinsa a hukumance.

Bikin rantsarwar ya gudana ne ranar Litinin a babban zauren taron Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

An raba ministocin ne zuwa rukuni bakwai sannan aka rantsar da su rukuni bayan rukuni.

Runkunin farko da aka rantsar ya ƙunshi Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, Ƙaramar Ministar Ƙwadago Nkiruka Onyejeocha, Ƙaramin Ministan Gas a Ma’aikatar Albarkatun Fetur, Ekperikpe Ekpo, Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy da kuma Ministan Ilimi, Tahir Maman.

Sai rukuni na biyu da ya ƙunshi Ministan Lafiya da Walwala, Ali Pate, Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, Ƙaramin Ministan Mai a Ma’aikatar Albarkatun Fetur, Heineken Lokpobiri, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta, Joseph Utsev,sai Ministan Sanya Ido Kan Harkokin Noma da Wadata Ƙasa da Aabinci, Abubakar Kyari.

Sai rukuni na uku wanda yake ƙunshe da Ministan Jinƙai da Yaye Talauci, Betta Edu, Ministan Bunƙasa Wasanni, John Enoh, Ministan Sufurin Jirgin Sama, Festus Keyamo, Ministan Ayyuka, Dave Umahi da Ministan Bunƙasa Yankin Niger Delta, Abubakar Momoh.

Rukuni na huɗu kuwa, ya ƙunshi Ministan Ma’adinai, Dele Alake, Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, Ministan Sufuri, Alkali Sa’id, Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Doris Anite, sai kuma Ministan Tsaro, Mohammed Badaru.

Yayin da rukuni na biyar da aka rantsar ya ƙunshi Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Gwarzo, Ƙaramar Ministar Abuja, Mariya Mahmud, Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Dangiwa, Ministar Al’adu da Ƙirƙire-ƙirƙiren Tattalin Arziki, Hannatu Musawa, sannan Ministan Kasafi da Tsarin Tattalin Arziki, Atiku Bagudu.

Rukuni na shida ya ƙunshi Ƙaramin Ministan Ilimi, Yusuf Sunumu, Ministan Ƙafa, Shuaibu Audu, Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwala, Tunji Alausa, Ministan Yawon Buɗe-ido, Lola Ade-John da Ministar Harkokin ‘Yan Sanda, Imaan Sulaiman- Ibrahim.

Sai rukuni na bakwai kuma na ƙarshe da ya ƙunshi Ministan Harkokin Noma da Wadata Ƙasa da Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi, Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Muhammed Idris, Ministan Muhalli, Ishak Salako, Ministan Kuɗi kuma Mai Sanya Ido Kan Tattalin Arziki, Wale Edun, sai kuma Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani.

Mahalarta taron rantsarwar sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abass, Sakataren Gwamnatin Tarayya, gwamnoni da sauransu.