Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a ƙarni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari’a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane.

Lokacin da Ahmed Baba ya rayu:

An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu a wani masallaci da ya yi suna.

Bayan ya nuna adawa da mamaye birnin Timbuktu a shekarar 1591 da sarkin Maroko, Ahmed Al-Mansur ya yi, an tasa ƙeyar Baba zuwa Maroko. Lokacin zamansa na shekaru 12, ya ci gaba da harkokin addinin Islama. Ahmed Baba ya koma birnin Timbuktu a shekarar 1608, inda ya rasu a shekarar 1627.

Abin da aka san Ahmed Baba da shi:

Lokacin rayuwarsa an san shi da rubuta yarjeniyoyi na shar’ia da ke da dangantaka da addinin Islama ta hanyar rayuwar Musulmai da addininsu. Yau sunan Ahmed Baba na da dangantaka da tunanin lokacin da birnin Timbuktu ya ke tsakiyar tashe.

Tunanin Ahmed Baba:

Ahmed Baba ya yi ƙoƙarin ganin mutanen da suka fito daga ƙabilu daban-daban sun rayu da juna a birnin Timbuktu a lokacin. Yana ganin ilimi zai kawo ƙarshen bambancin ƙabilanci. ‘Yan Maroko da suka kama Baba duk da sun yi masa ɗaurin talala, sun ɗauke shi a matsayin malami na gani na faɗa.

Cece-kucen da ke kewaye da Ahmed Baba:

Game da batun bauta, Ahmed Baba ya rubuta cewa Musulmai ba za su zama bayi ba ko daga ina suka fito bisa asalin mutum ko launin fata. A lokacin bayi sun kasance rukuni mai muhimmanci na ciniki a birnin Timbuktu. Ya fahimci dokokin addinin Islama a lokacin ta hanyar da ake gani mai cike da gagarumin sauyi, saboda nuna duk masu imani a matsayin suna da matsayi guda a wajen Allah. Amma, Ahmed Baba bai yi tir da cinikin bayi ba, bisa rubutun ya dace a yi cinikin bayi da ba Musulmai ba.

Ahmed Baba ya shahara saboda sanin da ya ke da shi da kuma basira, ya nuna bajinta kan adawa da mamaya daga Maroko waɗanda suka kame garinsa na Timbuktu.

Lokacin da ya ke zaman hijira a Maroko, Ahmed Baba ya tuna da gida: “O kai ne mai zuwa Gao, ka yi haka ta bin Timbuktu sannan ka fadi suna ga abokaina. Shaida musu gaisuwa daga wanda ya ke waje, wanda ya ke ganin qasa da abokai, da ‘yan uwa gami da makwabta.”

Babbar makarantar koyar da addinin Islama da bincike da ke birnin Timbuktu, tana ɗauke da rubuce-rubuce kimanin 30,000 kuma na zama ɗaya daga cikin matattara mafi muhimmanci ta Islama da ke qunshe da littattafai da kayayyakin tahirin wadda aka saka sunan Ahmed Baba sannan wani ɓangare na duniyar Mercury. An ɗauki Ahmed Baba a matsayin gwarzo a ƙasar Mali yanzu haka.