29
Jul
Daga BASHIR MUDI YAKASAI Masana tarihi sun tabbatar da dalilan da suka sa ƙasashen Turai suka kasa barin Nahiyar Afirka duk da cewa sun ba su ’yancin kai, sama da shekaru 60 da suka shuɗe. Duk da cewa sun kwashe sama da shekaru 100, suna waɗari a Afirka suna wawason bayi da amfanin gona tun daga dawa, alkama, auduga da sha’ir da ma’adanai irin su zinare da murjani da azurfa da hauran giwa da jimina da gashinta da kuma turaren wuta. Da tafiya ta yi tafiya, aka gano Ɗanyen man fetur da gas da kuma dangoginsa, Turawan Yamma da na…
