Editor

9513 Posts
Makon gobe Majlisa za ta fara tantance sunayen ministocin Tinubu

Makon gobe Majlisa za ta fara tantance sunayen ministocin Tinubu

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta ce ya zuwa ranar Litinin mai zuwa za ta fara tantance sunayen mutum 28 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike mata wanda yake neman naɗa su muƙaman ministoci. Mai magana da yawun Majalisar, Sanata Adeyemi Adaramodu (APC-Ekiti), shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Majalisar ta Dattawa. Adaramodu ya ce duk da dai Litinin ba ranar zaman majalisar ba ce, amma la'akari da muhimmancin da ke tattare da aikin "ya sa muka dakatar da dokokinmu domin fara aikin tantancewar Litini mai zuwa." Ya ƙara…
Read More
Zan ƙarasa ayyukan Kwankwaso da Ganduje ya ƙi yi – Gwamna Abba

Zan ƙarasa ayyukan Kwankwaso da Ganduje ya ƙi yi – Gwamna Abba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na ci gaba da ayyukan da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fara a lokacin yana gwamnan jihar amma gwamnatin da ta shuɗe ta Abdullahi Ganduje ta yi watsi da shi. Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano Marwan Ahmad ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishinsa ranar Alhamis. Ya bayyana buqatar sake dawo da ayyukan a matsayin hanyar da ta dace don samar da guraben ayyukan yi ga matasa a jihar domin kame masu tada zaune tsaye a cikin…
Read More
Henderson ya koma Al-Ettifaq ta Saudiyya

Henderson ya koma Al-Ettifaq ta Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kyaftin ɗin Liverpool, Jordan Henderson ya koma Al-Ettifaq mai buga babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya. Ɗan ƙwallon tawagar Ingila, mai shekara 33 ya amince da ƙunshin yarjejeniyar fam miliyan 12 har da ƙarin tsarabe-tsarabe. A sakon ban kwana da ya yi wa Liverpool, ya ce zai bar ƙungiyar inda ya yi kaka 12, wadda ya lashe firimiya da Champions League a ita da sauran nasarori. Henderson yana Liverpool tun bayan da ya koma Anfield daga Sunderlandn kan fam miliyan 20 a watan Yunin 2011. Ya buga karawa 492 da cin ƙwallo 33 da bayar da…
Read More
Matawalle ka iya zama ƙalubale ga gwamnatin Tinubu

Matawalle ka iya zama ƙalubale ga gwamnatin Tinubu

Daga ALI MUHAMMAD Bayan shekaru 4 da aka shafe ana gurzuwa cikin masifa mara adaɗi, a lokacin da Matawalle yake ayyuka kamar na 'yan ta'adda marasa imani ko 'yan fashi a gefen filin Sahara, yana varnatar da dukiyar jihar Zamfara yayin da jihar take qara kasancewa abar tausayi kuma maƙasƙanciya, bai kamata a ce an yi wa Matawale sakayyar mugun mulkinsa da kujerar minista ba. Matawalle ya yi iƙirarin an kashe kimanin Naira biliyan 3 a kan tsaro da sayen kayan aikin kyamarar tsaro. Mecece alaƙar Matawalle da kamfanin haɗa magungunana ’’dot.com‘’ wanda aka ba wa kwangilar Naira biliyan guda…
Read More
Kasuwancin littattafai a onlayin babban cigaba ne – Zulaihat Rano

Kasuwancin littattafai a onlayin babban cigaba ne – Zulaihat Rano

"Ta bincike da tunasarwar manyan marubuta nake samun hikimar rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Daga cikin marubutan Hausa da suka ci kasuwar littattafai tun zamanin adabin kasuwar Kano ke tashe, kuma yanzu suka dawo suka rungumi tsarin rubutun onlayin, akwai marubuciya Zulaihat Haruna Rano, daga Jihar Kaduna, wacce ta yi rubuce-rubuce da dama, masu ilimantarwa da nishaɗantarwa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da ita game da inda ta sa alqiblar rubutunta da kuma hasashenta kan cigaban harkar rubutun adabi, musamman yanzu da abubuwa suke komawa yanar gizo. Ga yadda hirar ta su ta kasance.…
Read More
Ministoci: Sunan mawallafin jaridun Blueprint, Manhaja ya leƙo a sunayen da Tinubu ya miƙa wa Majalisa

Ministoci: Sunan mawallafin jaridun Blueprint, Manhaja ya leƙo a sunayen da Tinubu ya miƙa wa Majalisa

Daga BASHIR ISAH Sunan mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya leƙo a rukunin farko na sunayen da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawan don tabbatar da su a muƙaman ministoci. Tinubu ya miƙa sunayen ga majalisa ne ta hannun Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Hon Femi Gbajabiamila, a ranar Alhamis. Sunayen mutum 28 Tinubu ya miƙa wa majalisar da suka haɗa da: Abubakar Momoh, Ambasada Yusuf Maitama, Tukur, Arch. Ahmed Dangiwa, Barr. Hannatu Musawa da Chief Uche Nnaji. Sai kuma Dr. Berta Edu, Dr. Dorris Aniche Uzoka, Nyesom Wike, Badaru Abubakar, Nasiru Ahmed…
Read More
Kotu ta yi watsi da buƙatar DSS ta neman ci gaba da tsare Godwin Emefiele

Kotu ta yi watsi da buƙatar DSS ta neman ci gaba da tsare Godwin Emefiele

Daga BASHIR ISAH Wata Babbar Kotu mai zamanta a birnin tarayya, Abuja, ta yi watsi da ƙarar da hukumar tsaro ta DSS ta shigar inda take buƙatar kotu ta tsawaita mata damar ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Godwin Emefiele. A ranar Laraba 25 ga Yuli, DSS ta shigar da ƙarar tata a kotun, inda ta yi iƙirarin cewa ta samo ƙarin hujjar da za ta yi amfani da ita a kan Emefiele a gaban kotu. Sai dai, Kotun ta yi watsi da ƙarar ta DSS saboda rashin hurumin sauraron ƙarar. Alƙalin kotun, Hamza Muazu, ya…
Read More
Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dattawa sunayen ministocinsa

Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dattawa sunayen ministocinsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dattawa sunayen waɗanda yake so ya naɗa ministoci don neman amincewarta. Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, shi ne ya gabatar da sunayen ga majalisar a ranar Alhamis. Daga jerin sunayen da aka habatar wa majalisar har da na wasu tsoffin gwamnoni da sauransu. Ga jerin sunayen kamar haka: Abubakar MomohYususf Maitama TukurAhmad DangiwaHannatu MusawaUche NnajiBetta EduDr. Diris Anite UzokaDavid UmahiEzenwo Nyesom WikeMuhammed Badaru AbubakarNasir El RufaiEkerikpe Ekp[oNkiru OnyejiochaOlubunmi –Stella OkoteteUju KEnedy OhaneyeBello Muhammad GoronyoDele AlakeLateef FagbemiMohammad IdrisOlawale EdunWaheed AdebanwpImaan Suleman IbrahimProf Ali PateProf Joseph UsevAbubakar KyariJohn…
Read More
Sojoji sun kifar da gwamnatin Bazoum

Sojoji sun kifar da gwamnatin Bazoum

Daga BASHIR ISAH Sojoji a ƙasar Nijar sun yi wa Shugaban Ƙasar, Mohamed Bazoum, juyin mulki ranar Laraba da daddare sa'o'i bayan da masu tsaronsa suka tsare shi a fadarsa. A jawabin da ya yi wa 'yan ƙasa kai tsaye a tashar talabijin ta ƙasar, Colonel-Major Amadou Abdramane ya bayyana cewa, “sojoji da sauran hukumomin tsaro sun yanke shawarar jawo ƙarshen gwamnatin da kuka sani. “Wannan ya biyo bayan ci gaba da taɓarɓarewar tsaron ƙasar da kuma rashin walwala da ingancin tattalin arziki," in ji shi. Sojojin sun ce an rufe iyakokin ƙsar, sannan an kafa dokar hana zirga-zirga a…
Read More