26
Jul
"Matsalar aure da na shiga ta sa ni kafa ƙungiyar taimakawa mata" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Masu hikimar magana na cewa, ciwon 'ya mace na ’ya mace ne. Kuma abu namu maganin a kwaɓe mu. Wannan duk maganganu ne na azanci da ake jingina su ga mata. Duk kuwa da cewa da ake yi mata ba su cika son junansu ba, ko nuna goyon gaba da tausayawa 'yan uwansu mata ba. Amma wannan zargin bai cika zama gaskiya ba, domin kuwa ana samun mata da ke nuna tsananin tausayawa da tallafawa ga 'yan uwan su, sakamakon wata jarabawar rayuwa da…
