25
Jul
Daga BASHIR ISAH An gurfanar da dakataccen Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, a Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a Legas bisa zargin laifuka biyu da suka haɗa da mallakar bindiga da alburusai ba bisa ƙa'ida ba. Majiyarmu ta ce jami'an DSS ne suka shigo da Emefiele ɗin kotun da safiyar ranar Talata. Zaman kotun ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Nicholas Oweibo. Tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Joseph Daudu, shi ne ya jagoranci tawagar lauyoyin da ke kare Emefiele ɗin. Kodayake dai Emefiele ya musanta tuhumar da ake yi masa, inda ya ce bai aikata…
