Editor

9513 Posts
Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

(Ƙarshen wannan tambaya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai tava fashi ba, sai da na yi shakara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarashe ni, idan na qiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi. To da iyaye suka fara zancen ba mu…
Read More
Zaɓen Shugaban Ƙasa: Jega da Mabari za su jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Laberiya

Zaɓen Shugaban Ƙasa: Jega da Mabari za su jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Laberiya

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙarfafa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta tura tawagar haɗin gwiwa zuwa ƙasar Laberiya domin bincike kan shirye-shiryen da ƙasar ta yi gabanin gudanar da babban zaɓe a ƙasar. Ya zuwa ranar 10 ga watan Oktoban 2023, Laberiya za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar ƙasar. Majiyarmu ta ce tawagar da ECOWAS ta tura ƙasar, za ta yi aikinta ne daga 23 zuwa 29 ga Yuli, kuma ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Nijeriya (INEC), Farfesa Attahiru Jega da Ambasada Calixte Mbari jigo a ƙungiyar Ƙaɗin Kan Afirka (AU). Sauran…
Read More
Ina jerin sunayen ministocin Tinubu na gaskiya?

Ina jerin sunayen ministocin Tinubu na gaskiya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA An yi ta tafka muhawara a Nijeriya da ganin jerin sunayen sabbin ministoci a yanar gizo da lamarin ya juye zuwa jita-jita bisa ga dukkan binciken da a ka gudanar. Wannan dai ba shi ne karo na farko da jerin sunayen ke fitowa ba. Duk da a na sa ran shugaba Tinubu zai miƙa sunayen ministocin sa ga Majalisar Dattawa nan ba da daɗewa ba; amma waɗanda su ka bayyana zuwa yanzu sun zama tamkar na fatan alheri ne ko yada farfaganda da wasu ke yi don tallata sunayen wasu gwanayen su. Ma’ana kamar a bugi…
Read More
Magance matsalar rashin tsaro a Filato da sauran jihohi

Magance matsalar rashin tsaro a Filato da sauran jihohi

A kwanakin baya ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gurfanar da waɗanda suka aikata kisan gilla a wasu sassan jihohin Filato da Binuwai. Shugaban ya kuma bayyana tashe-tashen hankula a jihohin biyu a matsayin abin takaici. Baya ga haka, ya kamata jami’an tsaro su dakatar da tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan. Mummunan hare-haren da aka kai a Jihohin Filato da Binuwai sun haddasa asarar rayuka da lalata gidaje. Tun a ranar 15 ga watan Mayu ne aka fara zubar da jini a…
Read More
Napoli ta yi wa Osimhen tayin Naira biliyan shida duk shekara

Napoli ta yi wa Osimhen tayin Naira biliyan shida duk shekara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Zakarar gasar Seria A a kakar da ta gabata Napoli, ta yi wa ɗan wasan gabatanta Victor Osimhen tayin kwantiragin shekaru biyu, inda za ta riƙa biyan shi Yuro miliyan 6 da dubu ɗari biyar kwatankwacin Naira biliyan shiga da miliyan ɗari biyar a duk shekara. Ɗan wasan da ke da ragowar kwantaragin shekaru biyu da ƙungiyar, ya buƙaci ta riƙa biyan sa Yuro miliyan 7 a duk shekara. Osimehen mai shekaru 24 ya taimakawa Napoli wajen lashe gasar Seria A karon farko a cikin shekaru 33, inda ya zura ƙwallaye 26 a cikin wasanni 32…
Read More
Ɗangote zai haɗe kamfanoninsa na gishiri, shinkafa da kuma na sukari a waje guda

Ɗangote zai haɗe kamfanoninsa na gishiri, shinkafa da kuma na sukari a waje guda

Daga AMINA YUSUF ALI NASCON kamfanin samar da gishiri a ƙarƙashin rukunin kamfanonin Ɗangote yana shawarar haɗewa tare da wasu kamfanonin abinci guda biyu daga cikin rukunin kamfanonin nasu. Wato kamfanin shinkafa da na sukarin Ɗangote. Za a tattauna a kan wannan al'amari a samar masa matsaya a taron kwamitin daraktocin kamfanonin da za a gudanar nan gaba a cikin wannnan watan. Wannan haɗaka da ake sa ran yi tana zuwa ne watanni 31 bayan babban kamfanin da yake hamayya da kamfanin Ɗangoten, BUA Group, ya ba da sanarwar yin wannann haɗaka ta haɗe kamfanoninsa na shinkafa, sukari, fulawa, man…
Read More
Gwamnatin Kano ta naɗa sabbin shugabannin ma’ikatu da hukumomin lafiya

Gwamnatin Kano ta naɗa sabbin shugabannin ma’ikatu da hukumomin lafiya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗin shugabannin wasu ma’aikatu da hukumomin lafiya don tafiyar da su yadda ya kamata. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai da yammacin Laraba,Sanarwar ta ce naɗin na su ya fara aiki ne nan take. Waɗanda aka naɗa ɗin sune kamar haka: Dr. Mansur Mudi Nagoda, Executive Secretary, Hospital Management Board (HMB); Dr. Nasir Mahmoud, Executive Secretary, Kano State Primary Healthcare Management Board (SPHMB); Farfesa Salisu Ibrahim Ahmed, Executive Secretary, Private…
Read More
Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga 22 a Katsina

Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga 22 a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kashe aƙalla 'yan bindiga 22 a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari a Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar. Jaridar PRNigeria ta ruwaito ce wa 'yan bindigar waɗanda galibinsu yaran riƙaƙƙen ɗan bindigar nan ne da aka kashe Abdulkareem Boss, an kashe su ne ranar Litinin, a wani hari ta sama da dakarun rundunar 'Hadarin Daji' mai yaqi da 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar ta kai. Wata majiya mai ƙarfi a rundunar sojin ta shaida wa PRNigeria cewa an kai harin ne a kan…
Read More
HOTUNA: Gwamna Abba ya miƙa wa Abba El-Mustapa takardar naɗi

HOTUNA: Gwamna Abba ya miƙa wa Abba El-Mustapa takardar naɗi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa wa jarumi a masana'antar Kannywood, Abba El-Mustapha, takardar naɗin da ya yi masa kwanan nan. Gwamna Abba ya naɗa El-Mustapha ne a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr Abdullahi Baffa Bichi shi ne ya miƙa wa El-Mustapha takardar a madadin Gwamna Abba. Ga ƙarin hotunan yadda taron miƙa takardar ya kasance:
Read More
An samu game da shugabancin Majalisar Nasarawa

An samu game da shugabancin Majalisar Nasarawa

Daga BASHIR ISAH 'Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun zaɓi Rt. Hon Ibrahim Balarabe Abdullahi (APC- Umaisha/Ugya) a matsayin Shugaban Majalisar jihar ta bakwai. Kazalika, 'yan majalisar sun sun zaɓi Hon Abel Yakubu Bala (PDP- Nassarawa Eggon ta Yamma) a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar. Muƙaddashin akawun majalisar, Hon Ibrahim Musa, shi ne ya sanar da hakan yayin rantsar da mambobin majalisar ta bakwai a Lafia, babban birnin jihar. Akawun majalisar ya ce an rantsar da mambobin majalisar ne daidai da damar da Gwamnan Abdullahi Sule na jihar ya bayar wanda ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasa.
Read More