Napoli ta yi wa Osimhen tayin Naira biliyan shida duk shekara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Zakarar gasar Seria A a kakar da ta gabata Napoli, ta yi wa ɗan wasan gabatanta Victor Osimhen tayin kwantiragin shekaru biyu, inda za ta riƙa biyan shi Yuro miliyan 6 da dubu ɗari biyar kwatankwacin Naira biliyan shiga da miliyan ɗari biyar a duk shekara.

Ɗan wasan da ke da ragowar kwantaragin shekaru biyu da ƙungiyar, ya buƙaci ta riƙa biyan sa Yuro miliyan 7 a duk shekara.

Osimehen mai shekaru 24 ya taimakawa Napoli wajen lashe gasar Seria A karon farko a cikin shekaru 33, inda ya zura ƙwallaye 26 a cikin wasanni 32 da ya yi mata a kakar da ta gabata, lamarin da ya sa manya ƙungiyoyi a Turai ke ta zawarcinsa.

Toh sai dai mai horar da ƙungiyar Rudi Garcia ya tabbatar da cewar, Osimhen ba zai bar ƙungiyar a kakar da za a fara ba.

A ranar Laraba ne ake saran ɗan wasan na Nijeriya ya koma atisayi ta re da sauran ’yan wasan ƙungiyar, a shirye-shiryen tun karar kakar da ake daf da farawa.