Magance matsalar rashin tsaro a Filato da sauran jihohi

A kwanakin baya ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gurfanar da waɗanda suka aikata kisan gilla a wasu sassan jihohin Filato da Binuwai.

Shugaban ya kuma bayyana tashe-tashen hankula a jihohin biyu a matsayin abin takaici. Baya ga haka, ya kamata jami’an tsaro su dakatar da tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan.

Mummunan hare-haren da aka kai a Jihohin Filato da Binuwai sun haddasa asarar rayuka da lalata gidaje. Tun a ranar 15 ga watan Mayu ne aka fara zubar da jini a cikin yankunan Ƙaramar Hukumar Mangu daga bisani kuma ya bazu zuwa wasu aananan hukumomi da wasu sassan jihar Benuwai.

A cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar, kimanin mutane 130 ne aka kashe, an ƙona gidaje 1,000 a rikicin da ya shafi ƙauyuka 22.

Sai dai wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta ‘Gideon da Funmi Para-Mallam Peace Foundation’, sun bayyana cewa aƙalla mutane 346 ne aka kashe a cikin watanni uku a ƙananan hukumomi takwas na jihar da rikicin ya shafa.

Ƙananan hukumomin da abin ya fi shafa sun haxa da Bokkos, Mangu, Barkin Ladi, Riyom, Jos ta arewa, Jos ta kudu; Mikang ɗan Bassa. Aqalla mutane 17 aka kashe a Bokkos, Mangu 234; Barkin Ladi 39; Riyom 36; Jos ta Arewa 5; Jos ta Kudu 9; Mikang 5 da ɗaya a majalisar Bassa. Baki ɗaya, kimanin gidaje 6,603 ne harin ya shafa.

A tsakanin 17 ga Afrilu zuwa 10 ga Yuli, 2023, akwai mutum 18,751 a sansanonin ’yan gudun hijira 14 da ke jihar. Daga cikin 18,751 da ke sansanin ’yan gudun hijira, akwai zawarawa 2,081 da marayu 6,066 ’yan tsakanin shekaru 0-5. Tsofaffi sun kai 1,057, yayin da matasa da marayu manya suka kai 828.

Hakazalika, Jihar Binuwai na fama da hare-haren da makiyaya masu kisa ke kaiwa. Sakamakon hare-haren da makiyayan ke kaiwa, jihar na da ’yan gudun hijirar da suka kai miliyan 2.5. A watan Afrilu, rikicin makiyaya ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 200 a jihar.

Gwamnan jihar na wancan lokacin, Samuel Ortom, wanda ya koka kan matsalar rashin tsaro, a ranar 8 ga Afrilu ya bayyana cewa an kashe sama da mutane 134 a cikin kwanaki biyar kacal.

Harin baya-bayan nan da makiyayan suka kai Akpuuna tare da rufe ƙauyukan ƙaramar hukumar Ukum da ke jihar ya yi sanadin mutuwar mutane 24. Da alama lamarin ya tilasta wa gwamnan, Rev. Fr. Hyacinth Alia, ya umurci jami’an tsaro da su kamo waxlɗanda ke da hannu a rikicin.

Muna Allah wadai da zubar da jini a yankin Arewa ta tsakiya. Haka kuma, matsalar rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas na ƙaruwa. Mummunar aiwatar da dokar zama-a-gida ta mako-mako da masu tayar da ƙayar baya suka yi ya haifar da kashe-kashe da lalata rayuwar mutane.

Buƙatar a gaggauta sakin jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biyaara (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, ya ƙara tsananta tashe-tashen hankula a yankin a ’yan kwanakin nan.

Ba tare da faɗin wasu kalmomi da yawa ba, dokar zama-a-gida na mako-mako ya lalata tattalin arzikin yankin Kudu maso Gabas, inda galibin kasuwancin ke ƙaura zuwa wasu shiyyoyin.

A kwanakin baya ne mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya ƙiyasta asarar da yankin ya yi na rashin tsaro a cikin shekaru biyu da suka wuce sama da Naira Tiriliyan huɗu. Rashin tsaro a yankin ya janyo masa asarar jari da dama.

Muna kira ga gwamnatin Tinubu da ta ɗauki matsalar rashin tsaro a yankin Arewa da Kudu maso Gabas a matsayin wata matsala da ke buƙatar magancewar gaggawa, wacce ta kamata a kula da ita cikin gaggawa.

Ya wuce abin da gwamnonin Kudu maso Gabas za su iya tunkarar su kaɗai. Babu shakka abin da ya shafi yankin ma zai iya shafar sauran sassan ƙasar. Ya kuma umarci jami’an tsaro da su tunkari matsalar tsaro a yankin Arewa da Kudu maso Gabas domin a samu zaman lafiya.

Don haka ya kamata Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya umarci dakarun sojin Nijeriya da su ƙara ƙaimi a yankin Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma da yankin Kudu maso Gabas inda shugaban ƙungiyar IPOB, Simon Ekpa, ya kafa dokar tilastawa mitane zaman dirshan a gida.

A gaggauta gurfanar da waɗanda ke da hannu wajen kashe-kashen a Binuwai, Filato da Kudu maso Gabas. Taɓarɓarewar rashin tsaro a yankunan biyu ya tsananta. Duk da haka, ya kamata jami’an tsaro su kasance da isassun kayan aiki domin aiwatar da komai cikin tsari.