Ina jerin sunayen ministocin Tinubu na gaskiya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

An yi ta tafka muhawara a Nijeriya da ganin jerin sunayen sabbin ministoci a yanar gizo da lamarin ya juye zuwa jita-jita bisa ga dukkan binciken da a ka gudanar. Wannan dai ba shi ne karo na farko da jerin sunayen ke fitowa ba.

Duk da a na sa ran shugaba Tinubu zai miƙa sunayen ministocin sa ga Majalisar Dattawa nan ba da daɗewa ba; amma waɗanda su ka bayyana zuwa yanzu sun zama tamkar na fatan alheri ne ko yada farfaganda da wasu ke yi don tallata sunayen wasu gwanayen su. Ma’ana kamar a bugi juji ne don a ji kukan gwazarma ko kuma a ce dabarar kar a manta wane da wane da a ke ganin sun ba da gudunmawa ga tallata ɗan takarar APC ɗin har ya maye gurbin tsohon shugaba Buhari.

Abun da ya fito fili a sunayen da a ka yayata da ba sunan wanda ya fitar da sanarwar kamar yadda a ke gani a bayanai masu tushe daga daraktan labaru na ofishin sakataren gwamnati Willie Bassey ko ma kakakin shugaba Tinubu wato Dele Alake; ba sunayen tsoffin ministocin gwamnatin da ta shuɗe ta shugaba Buhari.

Ba ma wani muƙarrabi na kusa cikin sunayen da haƙiƙa ba a san wanda ya ƙirƙiro sunayen ba amma ba mamaki jami’an ayyukan sirri za sui ya ganowa kuma su ɗau mataki ko su kyale bisa ga tasiri ko rashin tasirin hakan ga tsaro ko muradun ƙasa. Rashin ganin sunayen ma’abota tsohuwar gwamnati a jerin ne ya ƙara ƙarfafa tunanin masu ganin sabon zubi za a yi, kamar yanda muƙarrabin shugaba Tinubu wato Ibrahim Kabir Masari ya haskawa Muryar Amurka a wata zanatawa ta musamman.

Kazalika an ga wasu jihohin irin Zamfara na da sunayen ministoci biyu tsohon gwamna Bello Matawalle da Sanata Kabir Marafa, haka ma mai rubutun voyen ko masu rubutun sun warewa jihar Edo ministoci biyu wato Adams Oshiomhole da Farfesa Osunbor inda a ɗaya vangaren kuma su ka cikawa tsohon ƙaramin ministan kwadago Festus Keyamo burin zama babban ministan ƙwadago.

Abun nufi a nan an ga Keyamo lokacin bankwanan majalisar zartarwa ta gwamnatin tsohon shugaba Buhari ya na nuna ƙirƙiro ofishin ƙaramin minista ya sabawa tsarin mulki. Kazalika hakan tamkar ya na hana wanda a ka naɗa a matsayin ƙaramin minista aiki kai tsaye sai ta hanyar babban ministan sa kamar dai ya na aiki ne ƙarƙashin babban minista.

Aƙalla an ga sunan madugun gwamnoni 5 da su ka yi wa PDP bara’a ko ɗan takarar jam’iyyar Alhaji Atiku Abubakar wato tsohon gwaman Ribas Nyesom Wike a matsayin ministan ‘yan sanda.

Wasu tsoffin gwamnonin APC ma waɗanda ba za a yi mamaki ba in sun shiga jerin irin Nasiru Elrufai, Abdullahi Umar Ganduje da Abubakar Badaru sun fito a fatar, inda ba mamaki a ka saka matar tsohon gwamnan Kebbi Zainab Bagudu a matsayin ministar kiwon lafiya don likita ce mai yaƙi da cutar kansa.

Hakanan Aisha Dahiru Binani da ke ƙalubalantar ayyana gwamna Umar Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa ta fito a jerin; yayin da shi ma Jamilu Isiaka gwamna na kamfanin wuta na KEDCO ya shiga a matsayin ƙaramin ministan ma’adinai.

A dandalin manhajar WHATSAPP na kasuwar sayar da shanu ta Maliya a jihar Nasarawa an taya shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hote Bello Bodejo murnar zama ƙaramin ministan ayyuka na musamman.

Na zanta da ɗaya daga waɗanda sunayen su su ka fito a jerin ministoci a matsayin ƙaramin minista inda ya tabbatar min cewa abun da na gani shi ya yi tsammanin samu kamar yadda wani jigon gwamnati ya yi ma sa albishir. Don haka na yi ma sa fatar alheri da jiran sanarwa mai sahihanci ta fito don ganin tabbacin matsayar wannan bawan Allah.

Na kuma buga waya wajen wani daga cikin ’yan jerin da ya ce daga wajen mutane ya ji labari inda a ka yi ta bugo ma sa waya da hakan ya sa sai da ya kashe wayar sa don ya huta. Duk da labarin ba tabbaci amma shi ma bai nuna ɓacin rai ba don ya ɗauka hakan fatar alheri ne gare shi.

A gaskiya a yadda yanayin Nijeriya ya ke b azan yi mamaki ba in na sake ganin jerin wasu sunayen da wasu mutanen daban don su ma kar kasuwa ta tashi ta bar su da tarin rumfuna ko kuma a ce kar mota ta tashi ta bar su a tasha.

Ɗan kwamitin gudanarwa na APC Dattuwa Ali Kumo ya ce ba buƙatar gaggawa daga waɗanda su ka yaxa bayanan marar sa tushe amma jerin haƙiƙa na tafe “An tsara lokaci zuwa nan da wata biyu (nan ba da daɗewa ba) za a fito da jerin sunayen na gaskiya”

Za a jira a ga waɗanda za su zama ministocin gwamnatin Tinubu da a ka ce ‘yan siyasa za su ci gajiya kuma za a yi la’akari da gudunmawa daga jiha ko shawarar gwamnoni maimakon yadda tsohon shugaba Buhari ya naɗa ministocin sa bisa ga waɗanda ya sani ko ya gamsu ya yi aiki da su.

Ko wane tsari shugaba Tinubu zai ɗauka za a yi fatan ya ɗau wakilan da ke da goyon bayan jama’a daga gida waɗanda ke da tausayin jama’a a zuciyar su don wajen aiwatar da manufofi su riqa kaucewa ra’ayin kashin kai ko tsaurin ra’ayin ilimin boko ko wayewar yawace-yawace a duniya.

Wannan jerin sunaye ya fito ne jim kaɗan bayan ƙungiyar ECOWAS ta yi taro inda ta zaɓi shugaba Tinubu ya zama shugaban ƙungiyar. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban ƙungiyar raya tattalin arziki ta Afurka ta yamma ECOWAS ko CEDEAO. Wannan shi ne karo na farko da shugaban ya fita zuwa wani taro a Afurka tun hawan sa karaga a ranar 29 ga watan Mayu.

A taron ƙungiyar na 67 a babban birnin Guninea Bissau wato Bissau an tabbatarwa Tinubu zama shugaban ECOWAS inda ya karvi mulki daga shugaban ƙasar Umaro Mokhtar Sissoco Embalo wanda ya kammala wa’adin sa.

Tinubu ya ba da tabbacin ɗaukar matakan shugabanci don shawo kan ƙalubalen tsaro a yankin.

Tinubu ya ce zai haɗa kai da shugabannin yankin don cimma muradun kafa ƙungiyar ta ECOWAS wacce ke da helkwata a Abuja. Wasu daga muradun da a ka sani akwai inganta tattalin arzikin bai ɗaya a yankin da zai kai ga kirkiro takardar kuɗi iri ɗaya mai suna ECO.

A lokacin da a ke jiran fitowar jerin sunayen ministoci, shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ƙarin mataimaka 20 da su ka shafi ayyukan sa na yau da kullum har ma da ɓangaren dafa abinci.

Waɗanda a ka naɗan akwai sanannun fuskoki a kamfen irin Ibrahim Kabir Masari da ya samu kujerar babban mai taimakawa kan siyasa. In ba a manta ba Masari ne ya zama mataimakin ɗan takara na farko kafin sauyawa zuwa mataimakin shugaban ƙasa na yanzu Kashim Shettima.

Yayin da kakakin Tinubu a kamfen Tunde Rahman ya zama babban mataimaki kan labaru shi kuma ɗan jarida Abdulaziz Abdulaziz ya zama babban mai taimakawa kan jaridun takarda.

Sauran sun haɗa da na kula da baki, tsara lamuran gida da ma ɗaukar hoton bidiyo da na kati.

Ba mamaki fuskokin ‘yan kudu sun fi rinjaye a mataimakan in an duba shugaban daga kudu ya ke.

A halin da a ke ciki tuni wasu su ka fito da kamfen na adawa da yiwuwar naɗa wasu daga waɗanda su ka fito a jerin na yanar gizo da baiyana dalilan su na kyamar mutanen da hakan ba ya rasa nasaba da abubuwan da su ke ganin sun aikata bas u gamsar da su ba lokacin da su ke riqe da madafun ikon musamman wasu daga gwamnonin da su ka sauka kwanan nan. Amma fa kowa ba zai rasa magoya bayan sa ba don karkataccen wani gwanin wani ne.

Naɗa ministoci dai haƙƙin shugaban ƙasa ne da kan zaɓi sunaye ya tura majalisa ita kuma ta tantance. Duk wanda majalisa ya zama ba ta gamsu da shi ba sai dai ta dawo da sunan sa wajen shugaban ƙasa in ya so ya yi ƙarin bayani ko ya sauya wani. Haƙiƙa ingancin ministoci na da tasiri ainun ga irin abun da gwamnati za ta iya tavukawa.

Kun ga ai mutanen da za su zama membobin majalisar zartarwa da za su riƙa zama da shugaban ƙasa su na tattaunawa kan makaomar ƙasa ai ya dace a tanatnce su sosai kafin naɗa su. Idan an naɗa wanda burin sa tara abun duniya ko kuma wanda bai kware ba kuma ba ya son ma kwarewar don girman kai sai a kammala ’yan shekarun hudu a na kame-kame da ɗora laifi ga karayar arziki da sauran matsalolin ƙasa da ƙasa.

Kammalawa;

Nijeriya a yanzu na son zuba ido kan duk wanda a ka naɗa wani mukami ko kawai a ce an damkawa mutum amana in ya ci sai an je lahira ba. Nauyi ya rataya kan shugaba bisa rantsuwar da ya yi zai tabbatar da gaskiya ya zama jagora nagari mai bin ayyukan duk waɗanda ya ɗauka don taya shi gudanar da gwamnati ba wannan dan Sarki ne ko ƙanin Waziri ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *