Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga 22 a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kashe aƙalla ‘yan bindiga 22 a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari a Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito ce wa ‘yan bindigar waɗanda galibinsu yaran riƙaƙƙen ɗan bindigar nan ne da aka kashe Abdulkareem Boss, an kashe su ne ranar Litinin, a wani hari ta sama da dakarun rundunar ‘Hadarin Daji’ mai yaqi da ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar ta kai.

Wata majiya mai ƙarfi a rundunar sojin ta shaida wa PRNigeria cewa an kai harin ne a kan tsaunukan da ‘yan bindigar ke ɓoye, bayan samun bayan sirri da ke nuna cewa suna kitsa wani hari domin yin garkuwa da matafiya a kan hanyar Jibiya zuwa Katsina.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun addabi al’umomin yankin, inda suke yin garkuwa da mazaunan wasu yankuna a ƙaramar hukumar Ƙanƙara.

Harin wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga da dama, ya kuma lalata sansanonin ‘yan bindigar.

A cikin watan Agustan 2022 ne dai rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kashe fitaccen ɗan bindigar nan mai suna Abdulkareem Boss tare da wasu daga cikin yaransa a wani hari ta sama da rundunar ta ƙaddamar kan maɓoyarsu a dajin Ruga da ke Jihar Katsina.

An zargi Abdulkareem da kitsi wani mummunan hari da ya yi sanadin kashe wani babban baturen ‘yan sanda a ƙaramar hukumar Dutsinma ranar 5 ga watan Yulin 2022.

Mai maganar da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya tabbatar da harin na ranar Litinin, ya ce babban hafsan sojin sama na ƙasar, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya umarci dakarun sojin saman ƙasar da su haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin kakkafe duka ‘yan ta’addan da kuma maɓoyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *