Kasuwancin littattafai a onlayin babban cigaba ne – Zulaihat Rano

Ta bincike da tunasarwar manyan marubuta nake samun hikimar rubutu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Daga cikin marubutan Hausa da suka ci kasuwar littattafai tun zamanin adabin kasuwar Kano ke tashe, kuma yanzu suka dawo suka rungumi tsarin rubutun onlayin, akwai marubuciya Zulaihat Haruna Rano, daga Jihar Kaduna, wacce ta yi rubuce-rubuce da dama, masu ilimantarwa da nishaɗantarwa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da ita game da inda ta sa alqiblar rubutunta da kuma hasashenta kan cigaban harkar rubutun adabi, musamman yanzu da abubuwa suke komawa yanar gizo. Ga yadda hirar ta su ta kasance. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

ZULAIHAT RANO: Sunana Zulaihat Haruna Rano. Ni marubuciya ce, kuma ina sana’ar sayar da katin waya da data.

Ki ba mu tarihinki a taƙaice?

An haifeni ne a garin Kaduna, Unguwar Rimi a shekarar 1994, ni ce ‘ya ta uku a wajen iyayena, amma a yanzu ba ni da yayye da muke uwa ɗaya uba ɗaya, sai ƙannai da nake da su maza da mata. Na yi makarantar firamare ta L.E.A da ke Unguwar Kudu, daga nan na shiga qaramar sakandire wato JSS Unguwar Rimi, sai kuma na shiga makarantar sakandire ta ƴan mata ta GGSS Kabala Costain Kaduna, wacce take a Unguwar Kabala, kuma a nan na haɗa karatuna na sakandire. Sai dai a nan karatuna ya tsaya ban samu na cigaba ba, sai dai niyya nan gaba, in sha Allahu.

Ko za ki gaya mana yadda aka yi ki ka fara tunanin zama marubuciya?

Alhamdu Lillah! A gaskiya ban tava kawo cewar zan zama marubuciya ba, duk da kusan ‘yan unguwarmu da waɗanda nake mu’amala da su, sun san ni da mayatan karanta littattafai, ko tafiya nake yi a kan hanya za ka iya samuna da littafi a hannu. Sannu a hankali sai na ji a raina cewa kamar zan iya yin rubutu, ai kuwa cikin ikon Allah sai na fara yin rubutu ba tare da tuntuvar kowa ba. Idan na rubuta sai na ba ƙawayena su karanta tun suna yi mini dariya har suka koma ba ni ƙwarin gwiwa.

Yaya farkon rubutunki ya kasance? Wa ya fara taimaka miki?

Gaskiyar magana da kaina na shiga harkar rubutu. Bayan na gama rubuta littafina na farko, akwai wani abokina shi ne wanda yake ƙara mini qwarin gwiwa domin shi ne ma wanda ya haɗa ni da wani mutum mai yin aikin buga littafi, na manta sunansa yanzu, amma dai sunan kamfaninsa Sauƙi Press. Shi ne kuma ya haɗa ni da marubuciya Halima Abdullahi K/Mashi.

Daga lokacin da ki ka fara rubutu zuwa yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa? Ko za ki iya kawo sunayensu, da taƙaitaccen bayani game da wasu daga ciki?

Na rubuta littattafai guda shida. A ciki akwai ‘Rayuwar Nana Asma’u’, ‘Rayuwa Kenan’, ‘Ni’eema’, ‘Sangarta’, ‘Burina’, ‘Kyakkyawar Alaƙa’.

Shi littafin ‘Burina’, labari ne a kan wani saurayi da budurwa, inda shi saurayin ya kasance ɗan masu kuɗi ne, ita kuma budurwar sun kasance talakawa. Mahaifin tauraron labarin mutum ne mai tausayin marasa ƙarfi, yayin da a ɓangaren mahaifiyarsa kuma ta kasance ta tsani talaka da talakawa, shi ya sa da aka aura masa ‘yar talakawa suka riƙa gana mata azaba.

Shi kuwa littafin ‘Sangarta’, labari ne a kan wata sangartacciyar yarinya, wacce mahaifinta ya shagwaɓata. A kanta babu abinda mahaifinta ba ya iya wa, zai iya vatawa da kowa matuƙar ran Ameesha zai yi fari, ciki kuwa har da mahafiyarta da ‘yan’uwanta. Irin son da yake mata ne ya yi dalilin da abokin mahaifinta ya sanya aka bugeta da mota har ta samu ciwon mantuwa.

Littafin ‘Kyakkyawar Alaƙa’ kuwa labari ne na wasu masoya biyu, Ummu Salmah da Yarima Hafiz. Labari ne da aka gina shi a kan tsarin gidan sarauta. Duk ƙaunar da Yarima ke nunawa Salmah sai da wata hatsabibiya mai suna Nuwaira ta yi nasarar raba su, don kawai ta mallaki Yarima. Salmah ta sha wahala sosai, kafin Allah Ya sanyaya lamarin.

Daga ina ki ke samun hikimar yin rubutunki?

Ta hanyar bincike, da kuma tunasarwa daga manyan marubuta.

Menene sirri samun ɗaukakar ki a harkar rubutu?

(Dariya) Shi sirrin samun ɗaukaka ai ba ta wuce addu’a, ta iyaye da kuma wanda muke yi.

Wanne abu ne ya taɓa faruwa da ke a harkar rubutu wanda ba za ki manta da shi ba?

Gaskiya abubuwan da suka faru da ni ta hanyar rubutu waɗanda ba zan manta da su ba suna da yawa sosai, ta dalilin rubutu na je wajen da ban tava tunani ba, na haɗu da mutanen da kafin na gansu sai na sha wahala, amma dalilin rubutu a yanzu babu wani shamaki tsakanin mu. Ko wannan hirar da muke yi da kai ma ai ba abu ne da zan iya mantawa ba.

Yaya alaƙarki take da masu karatun ki, ta yaya ki ke fahimtar yadda suke bibiyar littattafanki?

Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanina da su, domin ina bibiyar sharhin da suke yi mini a duk lokacin da na yi fitar da rubutuna, ina ƙoƙarin yin gyara domin su fahimci abinda na ke son isar masu.

Yaya ki ke ganin canjin da aka samu na kasuwancin littattafai daga shaguna zuwa onlayin, shin hakan cigaba ne ko ci baya?

Gaskiya kasuwancin littattafai a online babban cigaba ne, saboda a yanzu duk abinda ka gani an fi mayar da hankali a onlayin fiye da kasuwa, mutum na kwance a gadonsa zai karanta littafin duk marubuciyar da ya ke so ba tare da ya sha wahala ba.

Wacce gudunmawa mata marubuta suke bayarwa ga gyara zamantakewar auratayya da kare haƙƙoƙin mata ƴan’uwansu?

Gudunmawar na da yawa, saboda gaskiya dalilin rubutu an samu gyara auratayya, sannan kuma akwai wuraren da da yawa ba su san mutunta ‘ya’ya mata ba, su a ganinsu ‘ya’ya mata an haifesu ne kawai domin bautar gidan uba da na gidan miji, amma yanzu Alhamdulillah! An samu sauyi sosai, musamman yadda aka bar ‘ya’ya mata suna karatu da kuma sana’o’i.

Wacce riba za ki ce kin taɓa samu wacce ki ke alfahari da ita a harkar rubutu?

Akwai su da yawa fa! Idan na ɗaga kai na dubi tarin shaidar karramawa da na samu ina tsananin jin daɗi kuma ina alfahari da rubutu.

An daina ganin rubutunki a ƴan shekarun baya bayan nan, kin yi ritaya ne ko hutu ki ke yi?

E! Ba shakka hutu na tafi, amma fa shi ma hutun bai samu a yadda na tsara ba, domin duk da haka ina rubuta gajerun labarai. Amma a yanzu ina sa ran in sha Allahu zan cigaba da rubuta wasu littattafai na guda biyu da ban ƙarasa ba, ‘Ban Za Ci Haka Ba’, da kuma ‘Zavina’. Duk da na san wasu daga cikin makaranta littattafai na sun manta da labarin, amma na tabbatar idan na dawo rubuta shi zai ƙayatar.

Wanne bambanci ake samu tsakanin marubucin da ya fara manyanta da mai ƙananan shekaru, wajen salon rubutunsu?

To! A wannan gavar ba na ganin cewar akwai bambanci tsakaninsu, saboda ina ganin shi fikirar rubutu, Allah ne Ya ke bai wa mutum, walau mai ilmi ko marar ilmi.

Ta yaya za a bambanta rubutun mai ilimi da na marar ilimi? Shin tilas ne marubuci ya zama mai ilimi?

E, to shi mara ilmi zai iya rubuta komai don a ganin shi daidai ne, shi kuwa mai ilmi sai ya duba da kyau ya kuma zurfafa ilminsa don ganin ya dace ya rubuta ko bai dace ba.

Shin kin gamsu da yadda ake samun yawaitar sabbin matasan marubuta masu ƙarancin shekaru?

E, ta wani ɓangaren na gamsu, amma ta wani ɓangaren ban gamsu ba, saboda a cikin sabbin marubuta masu ƙananan shekaru da za ka tambaye su, menene dalilin fara yin rubutunsu za su iya ce maka sun ga ana yi ne, babu mamaki ma ba su taɓa yin bincike ba, shi ya saka suke yin rubutu kara zube. Idan kuma wani ya yunƙura da niyyar yi masu gyara sai su hau kan shi da rashin kunya, saɓanin wanda suka mallaki hankalinsu kafin su shiga su kan fara bincike.

Shin kina ganin idan aka samu haɗin kan da ake buƙata daga ƙwararrun da ke cikin marubuta, za a samu wata damar da kowa zai ci moriyarta?

Ko shakka babu! Ai duk abinda kake gani a duniya ya samu cigaba to, idan ka bibiya za ka taras haɗin kai shi ne abu na farko, idan akwai haɗin kai komai zai iya samuwa, kuma na tabbatar da za a samu babban rabo a gaba.

Shin kina ganin shigowar gwamnati cikin harkar rubutu zai kawo wani cigaba ga inganta harkar rubutun adabi?

Zan so gwamnati ta shiga harkokin rubutu, na tabbata harkar adabi zai bunkasa, ta yadda ba a yi zato ba, yanzu ma kusan abinda ya kawo taɓarɓarewar harkar akwai rashin samun ɗauki daga gwamnati, amma da za ta shigo za a samu sauƙi sosai daga wasu abubuwan.

Kin taɓa shiga wata babbar gasa ta marubuta?

Na shiga gasanni biyu, akwai Gasar BBC Hausa Hikayata da aka shirya a shekarar 2021, na shiga da labarina mai taken ‘Buɗaɗɗiyar Wasiƙa,’ ban samu nasara ba, amma dai an ba ni shaidar karramawa. Sai kuma Gusau Institute ta shekarar 2022, da na shiga da labarina mai taken ‘Ciwon ‘Ya Mace’, shi ma ban yi nasara ba, amma na samu shaidar karramawa.

Menene babban burinki nan gaba a rayuwa?

Ina da burika masu yawa da nake son Allah Ya cika mini su, amma muhimmi a ciki shi ne a ce watarana na biyawa mahaifiyata kuɗin zuwa Saudiyya, domin ta je ta sauke farali.

Wacce shawara ki ke da ita ga mata marubuta?

Shawarata ga marubuta ba ta wuce na ce a duk lokacin da mutum zai yi rubutu to, ya tabbatar da ya yi bincike kafin ya fara ba. Sannan mu yi ƙoƙari mu rubuta abin da zai zame mana hujja a duniya da lahira. Mu tsaftace alƙalamin mu, ko domin ya amfani ‘yan baya. Idan kina da sha’awar shiga harkokin rubutu to, kafin ki fara ki nemi masana don su ɗora ki a kan turba.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Himma ba ta ga rago.

Mun gode.

Yawwa. Ni ma ina godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *