Editor

9513 Posts
Chana ta yi fatali da buƙatar gwamnatin Buhari ta neman rancen Naira Tiriliyan 10.1

Chana ta yi fatali da buƙatar gwamnatin Buhari ta neman rancen Naira Tiriliyan 10.1

Daga AMINA YUSUF ALI Bankin Exim na ƙasar Chana ya kore buƙatar Nijeriya na neman rancen Naira tiriliyan 10.12 (Wato Dalar Amurka $22,798,446,773). Wannan rance dai majalisar dokoki ta amince wa Buhari ya yi shi, a kwanakin baya. Wannan rance dai an yi nufin a yi amfani da kuɗin wajen gudanar da aikin zamanantar da layin dogo/ gadar jirgin ƙasa ta Kano zuwa Kaduna.  Amma sakamakon kasawar Nijeriya wajen biyan basussukan, da kuma tasirin annobar COVID-19 a kan aikin, Bankin Exim na ƙasar Chana ya janye tallafinsa.  Haka, majalisar wakilai a zamanta na ranar Talata 28 ga Maris, 2023, ta…
Read More
PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu ƙusoshinta

PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu ƙusoshinta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar PDP na Ƙasa (NWC) a ranar jiya Alhamis, ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu jiga-jiganta. Mambobin da aka soke dakatarwarsu sun haza da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose; Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim; Farfesa Dennis Ityavyar, Dakta Aslam Aliyu da Ibrahim Shema. Hakan na cikin wata sanarwar ne mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar na ƙasa, Debo Ologunaba. Ya ce, an ɗauki matakin hakan ne yayin taron na NWC a ranar Alhamis, inda mamabobin jam'iyyar suka yi tattaunawa mai zurfi kan abubuwan da…
Read More
Ma’aikatar Jinƙai ta sake horar da ma’aikata ƙwarewar aiki

Ma’aikatar Jinƙai ta sake horar da ma’aikata ƙwarewar aiki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ma’aikatar Kula da Harkokin Jinƙai, Magance Bala’o’i da Cigaban Al’umma ta Nijeriya, a ranar Alhamis, ta gudanar da wani taron ƙarawa juna da kuma horar da mambobinta na ɓangaren shirye-shirye, da suka haɗa da jin daɗin jama’a da cigaba al’umma a cikin ma’aikatar, don ba su damar samun sabbin ƙwarewa da ilimin da zai iya inganta aikinsu da rayuwarsu. Da ya ke jawabi a wajen taron a Abuja, Babban Sakataren Ma’aikatar, Dakta Nasir Sani-Gwarzo, wanda ya samu wakilcin mataimaki na musamman kan harkokin aiki, Malam Mohammed Dauda, ya ce ƙwarewa da ilimin da ma’aikatan ma’aikatar suka…
Read More
INEC ta ware Naira biliyan uku don yaƙi a kotunan zaɓe

INEC ta ware Naira biliyan uku don yaƙi a kotunan zaɓe

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ware Naira Biliyan Uku, don kare sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisar Dokoki Ta Ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023, da na gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jiha na ranar 18 ga Maris, 2023. Idan za a iya tunawa dai, 'yan takara da dama da suka faɗi zaɓen Shugaban Ƙasa da ma jiha sun shigar da ƙararraki a kotunan zaɓe, don ƙalubalantar sakamakon waɗancan zaɓuɓɓuka da kuma neman a soke su.   A yanzu haka dai akwai ƙararraki fiye da guda 100 a ƙasa waɗanda fusastattun 'yan takarkarun…
Read More
‘Yan sandan sun kama mutum 14 kan laifuka mabambanta a Kano

‘Yan sandan sun kama mutum 14 kan laifuka mabambanta a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda, ta yi nasarar cafke wasu ɓata-gari kan zargin aikata laifuffuka daban-daban. Bayanin haka na ƙunshe ne a sanarwar da ta fito daga Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa a ranar Alhamis. Sanarwar ta ce waɗanda aka kaman sun haɗar da 'yan fashi da makami, masu safarar migayun ƙwayoyi da ɓarayi tare da 'yan sara-suka, ƙarƙashin jagorancin CSP Bashir Musa Gwadabe. Ta ƙara da cewa CP Mamman Dauda ya ja daga da dukkan masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da sace-sace da sauran laifuka.…
Read More
Zaɓen 2023: Jerin sunayen alƙalan da aka zaɓa don sauraren ƙararraki kan zaɓuɓɓukan da aka gudanar

Zaɓen 2023: Jerin sunayen alƙalan da aka zaɓa don sauraren ƙararraki kan zaɓuɓɓukan da aka gudanar

Daga BASHIR ISAH Biyo bayan kammala zaɓukan 2023, an zaɓo alƙalai daga sassan ƙasar nan waɗanda za su saurari ƙararraki masu nasaba da zaɓukan. Mahaja ta fahimci an zaɓo alƙalan ne daga manyan kotunan jihohi da na tarayya da kuma kotun ma'aikata ta ƙasa. Ga cikakken sunayen alƙalan kamar haka: ABIA 1.Justice C.O. Onyeabo 2.Justice Ory Zik-Ikeorha 3.Justice C.H. Ahuchaogu 4.Justice A.O. Chijioke 5.Justice K.C.J. Okereke 6.Justice L.T.C. Eruba 7.Justice Benson Anya 8.Justice Nweke Philomena 9.Justuce A.O. Phoeba 10.Justice C.K. Nwankwo ADAMAWA 1.Justice H.N.H. Joda 2.Justice B.I. Ladukiya 3.Justice Musa Usman 4.Justice K.L. Samuel 5.Justice A.J. Balami 6.Justice K.Z.U. Modibbo…
Read More
Zargin gwamnatin riƙon ƙwarya: Jam’iyyu sun nemi a yi ’yar ƙure

Zargin gwamnatin riƙon ƙwarya: Jam’iyyu sun nemi a yi ’yar ƙure

*PDP da APC na son DSS ta kama sunaye*Cikin LP ya ɗuri ruwa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan tawagar ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyun APC da PDP sun ƙalubalanci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kamo kuma ta bayyana masu shirya gudanar da gwamnatin riƙon ƙwarya a Nijeriya. Majalisar a wata tattaunawa daban-daban da jaridun Nijeriya a ranar Laraba, 29 ga Maris, 2023, a Abuja, ta ce yunƙurin gudanar da gwamnatin riƙon ƙwarya ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar, inda ta ce, ya kamata a gano waɗanda suka shirya maƙarƙashiyar (sunansu) tare…
Read More
Ni na kashe Ummita amma ba da gayya ba, inji Ɗan Chana

Ni na kashe Ummita amma ba da gayya ba, inji Ɗan Chana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan ƙasar Chanan nan mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 da ake tuhuma da laifin kashe budurwarsa (Ummita) a jiya Alhamis ya tabbatar wa wata babbar kotu a Kano cewa ya dava wa budurwarsa ‘yar Nijeriya mai suna Ummukulsum Sani wadda aka fi sani da Ummita wuƙa, amma ba da niyyar kashe ta ba, a cewarsa. Wanda ake tuhumar, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, na ci gaba da gurfana ne a gaban kotun bisa laifin kisan kai. Frank da lauyan masu gabatar da ƙara ke yi masa tambayoyi, Darakta mai…
Read More
Kwamandan ISWAP ya kashe mataimakinsa saboda harin da sojoji suka kai musu

Kwamandan ISWAP ya kashe mataimakinsa saboda harin da sojoji suka kai musu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani Kwamandan ƙungiyar ISWAP, Abu Muhammed, ya kashe mataimakinsa, Abu Darda, bisa laifin yin sakacin da ya kai sojoji suka kai musu hari suka karkashe masa mayaƙa a sansanoninsu. An kai musu harin ne a sansanoninsu da ke ƙauyukan Mukdolo da Bonei wanda ya kai ga kashe mayaƙa 41, ciki har da Abu-Zahra Munzir. A rahoton da aka tattaro cewa kwamandan da ya fusata ya kashe Abu Darda a gaban sauran mayaƙan a ƙauyen Kajeri Dogumba da ke ƙaramar hukumar Mafa a jihar Borno. Majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa Abu…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe jaririn da aka haifa a wajensu, sun saki mahaifiyarsa a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe jaririn da aka haifa a wajensu, sun saki mahaifiyarsa a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ’yan bindiga da suka yi garkuwa da wata mata mai juna biyu a Ƙaramar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna sun sake ta bayan sun kashe jaririn da ta haifa a sansaninsu. Rahotanni sun ce maharan sun saki matar ce mai suna Shamsiyya Mustapha, wacce aka sace tare da mijinta da kuma ’yarsu mai shekara 16 a ƙauyen Janjala da ke Ƙaramar Hukumar ta Kagarko, ranar 5 ga watan Fabrairu. Sai dai daga bisani maharan sun saki mijin matar bayan karɓar kuɗin fansa Naira miliyan biyu da sabon babur da kayan abinci, amma suka ci…
Read More