Editor

9513 Posts
Abba Kabir ya kafa Kwamitin Karɓar Mulki

Abba Kabir ya kafa Kwamitin Karɓar Mulki

Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya kafa Kwamitin karɓar mulki daga Gwamna Ganduje. Hakan na cikin wata sanarwar da Kakakinsa Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da yammacin ranar Jumu'a. Ga sunayen 'yan Kwamitin kamar haka: Sen. AB Baffa Bichi, PhDChairman Prof. Hafiz AbubakarMember Hon. Shehu Wada SagagiMember Hon. Umar Haruna DoguwaMember Hon. Ahmad Garba BichiMember Dr Ali Haruna MakodaMember Barr Maliki KuliyaMember Barr. Haruna Isa DederiMember Dr. Danyaro Ali YakasaiMember Engr. Muhammad DiggolMember Dr Ibrahim Jibrin ProvostMember Sheikh Aminu DaurawaMember Dr. Labaran Abubakar YusufMember Prof Sani Lawan MFashiMember Alh. Umar S. MinjibirMember Dr Danjuma MahmudMember Engr.…
Read More
Shugabancin Kano: Ba zan biya bashin da ban ci ba, cewar Gwamna mai jiran gado ga Gwamna mai barin gado

Shugabancin Kano: Ba zan biya bashin da ban ci ba, cewar Gwamna mai jiran gado ga Gwamna mai barin gado

Daga RABI'U SANUSI a Kano Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ƙin amincewarsa wajen biyan bashin da gwamnati Gwamna Abdullahi Ganduje ta ciyo bayan bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a kwanan baya wnda Hukumar Zaɓe, INEC, ta tabbatar masa. Manhaja Blueprint ta rawaito cewar Abba Kabir, ya yi zargin gwamnatni mai barin gado ta ciyo basussuka da dama domin gadar wa gwamnati mai jiran gado. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya miƙa wa…
Read More
Kotu ta haramta wa Ganduje kusantar Filin Wasan Golf na Kano

Kotu ta haramta wa Ganduje kusantar Filin Wasan Golf na Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Jihar Kano ta nuna wa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje yatsa bisa yunƙurin da gwamnatinsa ke yi na ganin ta tsaga tare da cefanar da Filin Wasan Golf mallakar jihar. Manhaja Blueprint ta ruwaito cewa, Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Zuwaira Yusuf, ta buƙaci kada wani mai ruwa da tsakin da ya kusanci wannan fili har sai lokacin da Kotun ta ayyana a matsayin ranar da za a dawo don ci gaba da sauraron ƙarar, wato ranar 5 ga Yuni bayan kuma an rantsar da sabon gwamnan jihar.…
Read More
Tashar TRT ta ƙaddamar da sashin Hausa da wasu harsuna uku

Tashar TRT ta ƙaddamar da sashin Hausa da wasu harsuna uku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kafar yaɗa labarai ta ƙasar Turkiyya, wato Turke's Public Broadcaster (TRT), ta ƙaddamar da ƙarin ɓangarori guda uku da za su riƙa yaɗa labarai cikin harshen Hausa da Swahili da Turanci da kuma Faransanci. Tashar ta TRT ta yaɗa taron masu ruwa da tsaki a harkar na nahiyar Afrika da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Istanbul babban birnin ƙasar Turkiyya. Tun da farko an ƙaddamar da tashar wacce za ta dinga kawo labarai da rahotanni bisa tsarin dokar yaɗa labarai a gaban mambobin ƙungiyar watsa labarai ta nahiyar Afirka da manyan jami’an gwamnati da…
Read More
An kashe mata biyu a cibiyar addinin Musulunci a Lisbon

An kashe mata biyu a cibiyar addinin Musulunci a Lisbon

'Yan sanda sun ce wani mahari ya kashe wasu mata biyu, bayan da ya daɓa musu wuƙa a wata cibiyar addinin Musuluci a Birnin Lisbon na Ƙasar Portugal. An kai harin ne a cibiyar addinin Musulunci ta 'Ismaili Centre' da ke birnin. 'Yan sanda sun samu nasarar harbe maharin, wanda ke riqe da sharveviyar wuƙa a ƙafa, bayan da ya yi yunqurin guduwa. Kawo yanzu dai ba a san dalilin maharin na kashe matan ba. 'Yan sanda sun ce sun samu kiran waye inda aka shaida musu cewa, an ga maharin ya shiga cibiyar da misalin ƙarfe 11 na safe…
Read More
Za mu hukunta ƙasashen da suka bijire wa yaƙi da ɗumamar yanayi – MƊD

Za mu hukunta ƙasashen da suka bijire wa yaƙi da ɗumamar yanayi – MƊD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ɗaukar wani mataki da zai fara hukunta ƙasashen da ke fitar da hayaƙi da sinadaran da ke gurɓata muhalli ba kuma tare da ɗaukar matakin da ya dace ba. A wata ƙuri’ar jin ra’ayi tsakanin ƙasashe mambobin majalisar mai cike da tarihi da aka kaɗa a ranart Laraba, da tsibirin Vanuatu ya bada shawara, ta kuma tanadi damar gurfanar da ƙasar da aka samu da saɓa wannan doka, gaban kotun duniya musamman idan wannan ƙasa ta yi kunnen ƙashi wajen bada gudunmawa a yaƙi da gurvatar muhalli. Da yake jawabi bayan kaɗa ƙuri’ar, Firaministan…
Read More
Mun gamsu da jagorancin shugabannin Kasuwar Mile-12 a Legas

Mun gamsu da jagorancin shugabannin Kasuwar Mile-12 a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Wani ɗan kasuwar gwari dake Kasuwar Mile-12 a cikin garin Legas, Alhaji Auwalu na Ubanliba kuma mai bai wa shugaban kulawa da cigaban kasuwanci ɓangaren tumatiri shawara ta musamman, Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano, ya bayyana cewar shi da sauran al'ummar kasuwar suna cigaba da gamsuwa tare da amincewa da jagorancin shuwagabanni kasuwar gaba ɗaya. Alhaji Auwalu na Ubanliba ya yi wannan tsokacin ne a kasuwar Mile-12 a lokacin da yake zantawa da Jaridar Manhaja a Legas dangane da harkokin kasuwancin tumatiri a kasuwar, inda na Ubanliba ya cigaba da cewa haqiqa Abdulgiyasu Sani Rano yana…
Read More
Zaɓaɓɓen Gwamnan Jigawa ya karɓi shaidar lashe zaɓe, ya nemi haɗin kan al’ummar jihar

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jigawa ya karɓi shaidar lashe zaɓe, ya nemi haɗin kan al’ummar jihar

Daga ABUBAKAR M. TAHEER Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi Ɗan Modi, ya nemi haɗin kan al'ummar jihar Jigawa a lokacin da yake karɓan shedar lashe zaɓe daga hukumar INEC. Gwamnan Umar Namadi wanda ya bayyana haka a Hedkwatar hukumar INEC ta ƙasa da ke Dutse, ya ce a shirye yake domin sauke dukkanin alƙawuran da ya ɗauka lokacin gudanar da kamfe ɗinsa amma dole sai al'ummar jihar sun ba shi haɗin kai da goyon baya. Da yake jawabi Baturen Zaɓe na Jihar Jigawa, Farfesa Muhammad Lawan Bashir ya hori sabin shugabannin da su zama sun sauke nauyin al'umma…
Read More
Gwamnatinmu na da sauran lokaci a Kano, Ganduje ga Abba

Gwamnatinmu na da sauran lokaci a Kano, Ganduje ga Abba

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnat Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Uamar Abdullahi Ganduje, ta yi kira ga Gwamnan jihar mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, da ya yi haƙuri tare da daina fitar da sanarwa a hukumance ta hanyar ba da shawara ga jama’a domin kada a haifar da ruɗani da bai kamata ba a jihar. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Malam Muhammad Garba, ya fitar a ranar Juma’a a matsayin martani ga umurnin da ofishin zababben gwamnan ya fitar, inda ya gargaɗi mutane, ƙungiyoyi da ƙungiyoyin da…
Read More
Matsalolin Nijeriya na hana ni barci – Sarkin Katsina

Matsalolin Nijeriya na hana ni barci – Sarkin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya bayyana cewar matsalolin da Nijeriya ke fuskanta na daga cikin abubuwan da ke hana shi bacci ido biyu rufe. Ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Birnin Katsina, lokacin da yake ƙaddamar da gidauniyarsa mai laƙabin 'Gidauniyar Mai Martaba Sarkin Katsina'. "Matsalolin Nijeriya na daga cikin abubuwan da suka dame ni, har ta kai ina rasa bacci, nakan yi kwana uku zuwa bakwai ba na bacci," inji shi. Basarken ya kuma ce matsaloli gami da ƙalubalen ƙasar nan, su ne suka haddasa masa larura ta…
Read More