Editor

9513 Posts
Shugaban Man City ya zama mataimakin shugaban Daular Larabawa

Shugaban Man City ya zama mataimakin shugaban Daular Larabawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta naɗa mamallakin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City da ke Ingila, Sheikh Mansour bin Zayed a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Ƙasar. A cikin wata sanarwa da Kamfannin Dillancin Labaran ƙasar na Wam ya wallafa, ƙasar ta ce attajirin ya ɗare kujerar ce a matsainsa na shugaban gwamnati. Shugaban Ƙasar ne dai ya sanar da amicewar naɗin, inda ya ce matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Ƙolin Ƙasar na naza Sheikh Mansour a matsayin. Kafin naɗin nasa dai, attajirin shi ne Mataimakin Fira Ministan ƙasar. Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasar ya ayyana sunan…
Read More
Kano: Abba Kabir ya naɗa Sanusi Bature matsayin Babban Sakataren Yaɗa Labarai

Kano: Abba Kabir ya naɗa Sanusi Bature matsayin Babban Sakataren Yaɗa Labarai

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗa fitaccen ɗan jaridar nan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a matsayin Babban Sakataren Yaɗa Labaran sa. Naɗin na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamitin sabon gwamnan ya fitar a ranar Alhamis a madadin zaɓaɓɓen gwamnan. Sanarwar ta ce Gwamnan ya bayyana Sanusi Bature Dawakin Tofa a matsayin wanda ya cancanta sakamakon ƙwazonsa, haƙuri da kuma biyayya. Dawakin Tofa wanda ya kasance fitaccen ɗan jarida mai ƙwarewar aiki ta shekaru 19 a fagen aikin jarida, kuma yana cikin masu bada gudunmuwa mai…
Read More
Raɗɗa ya karɓi shaidar lashe zaɓen gwamnan Katsina

Raɗɗa ya karɓi shaidar lashe zaɓen gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC, ta ba wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa takardar shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar a ranar Alhamis. Kwamishinan hukumar zave mai wakiltar Jihohin Kano, Katsina da Jigawa, Farfesa A. A Zuru ne ya miƙa shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓen gwamnan da mataimakinsa da kuma 'yan majalisar dokoki na jihar su 31. Da yake jawabi, Dr. Dikko Raɗɗa, ya gode wa Allah bisa nasarar da ya samu na lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023. Ya kuma yaba wa hukumar zaɓe mai…
Read More
Ku kira ni da  ‘Malam Dikko Raɗɗa’ maimakon ‘Your Excellency’ – Raɗɗa

Ku kira ni da ‘Malam Dikko Raɗɗa’ maimakon ‘Your Excellency’ – Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana dalilin da ya sa ba ya so a kira shi da kalmar ban girma, wato 'Your Excellency' bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar. Raɗɗa ya bayyana cewar ba ya son a kira shi da 'Yallaɓai har zuwa ƙarshen wa'adin mulkinsa da zai fara ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa. "Ba na son a kira ni 'Excellency' saboda za a iya kiran mutum kaɗai da 'Excellency' ne bayan ya kammala mulkinsa. "A wannan lokacin ne mutane za su tabbatar na cancanci a…
Read More
Tinubu na buƙatar addu’a don samun nasarar gudanar da mulki – Masari

Tinubu na buƙatar addu’a don samun nasarar gudanar da mulki – Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewar zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na buƙatar samun ƙarin addu'o'i daga 'yan Nijeriya, domin samun damar gudanar da mulki cikin nasara. Masari ya bayyana haka ne a Fadar Gwamnatin Jihar, lokacin da yake jawabi a wurin taron buɗa-baki wanda aka shirya albarkacin watan Ramadan. A cewar Masari, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar kan shirya irin wannan taron don yin addu'o'i lokacin watan Ramadan. Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN), ya ambato Masari yana cewa, "An shirya taron wannan shekarar domin yin godiya ga Allah kan nasarar da…
Read More
HOTUNA: Yadda masoya suka yi dandazo wurin karɓar shaidar lashe zaɓen Abba Kabir

HOTUNA: Yadda masoya suka yi dandazo wurin karɓar shaidar lashe zaɓen Abba Kabir

A ranar Laraba Hukumar INEC ta miƙa wa 'yan takarar da suka lashe zaɓen gwamna a jihohinsu shaidar lashe zaɓen gwamnan da ya gudanar ranar 18 ga Maris, 2023. Haka ma lamarin ya kasance a Jihar Kano, inda ɗan takarar Jam'iyyar NNPP, Abba Kabir da Mataimakinsa, Aminu Abdussalam, suka karɓi shaidar lashe zaɓe a matsayin gwamna da mataimakinsa daga hannun INEC. Masoya daga sassan jihar suka fito don nuna goyon baya da murnar ga Gwamnan Kano mai jiran gado da mataimakinsa yayin da suka karɓi shaidar lashen zaɓen. Ga ƙarin hotunan irin wainar da aka toya daga Sani Maikatanga:
Read More
Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna a jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya taya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, murna. Ta cikin wani sako na murya da mai magana da yawunsa, Hassan Musa Fagge, ya saki a manhajar WhatsApp a ranar Laraba, Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida addu’ar Allah Ya sa ya zama shugaba nagari. A cewar Gawuna, tun bayan da hukumar zaɓe, INEC, ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen, jam’iyyar APC…
Read More
Buhari ya rantsar da Arase a matsayin Shugaban PSC

Buhari ya rantsar da Arase a matsayin Shugaban PSC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, Solomon Arase, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Harkokin 'Yan Sanda (PSC). Buhari ya rantsar da Arase ne gabanin zaman Majalisar Zartawa ranar Laraba a Abuja. Rantsarwar na zuwa ne bayan tabbatar da cancantarsa da Majalisar Dattawa ta yi watanni biyu da suka shuɗe. Buhari ya miƙa sunan Arase ga Majalisar Dattawa don neman yardarta kan naɗin daidai da sassa na 153 (1) da 154 (1) na kundin tsarin mulkin ƙasa wanda aka yi wa kwaskwarima. Arase, mai shekaru 65 da haihuwa, ya yi…
Read More
Zaɓen 2023: Waɗanne abubuwa ne suka fi ɗaukar hankalin masu zaɓe?

Zaɓen 2023: Waɗanne abubuwa ne suka fi ɗaukar hankalin masu zaɓe?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Komai aka sa masa lokaci zai zo ya wuce, in da rai da nisan kwana. Babban Zaɓen 2023 da ake ta dakon zuwansa ana ta shirye-shirye a matakai daban-daban ya zo ya wuce, cikin lumana da kwanciyar hankali, duk da ƙalubalen tsaro da aka fuskanta nan da can. An yi nasarar kammala zaɓen Shugaban Ƙasa da na ’yan Majalisar Ƙasa, yayin da aka yi na Gwamna da na ’yan Majalisar Jiha. Sai dai duk da kasancewar an yi zaɓe cikin lumana a mafi akasarin jihohin ƙasar nan musamman a nan Arewa. Ba za a rasa wasu…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Abba Kabir ya karɓi shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Da Ɗumi-ɗumi: Abba Kabir ya karɓi shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Jihar Kano, ta miƙa wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar ƙarƙashin jam'iyyar NNPP shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar. Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Abdulsalam Gwarzo sun karbi satifiket ɗin ne ranar Laraba a babban ofishin INEC da ke Kano. Cikin waɗanda suka halarci taron miƙa shaidar, akwai Shugaban hukumar zaben na Kano, Ambasada Zango Abdu, Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda da dai sauran jiga-jigan jam'iyyar NNPP na ciki da wajen jihar.
Read More