29
Mar
Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta fara miƙa shaidar lashe zaɓe ga 'yan takarar da suka ci zaɓen gwamna a jihohinsu. Zaɓaɓɓun gwamnoni a jihohi 26 ne INEC ta tabbatar da nasarar da suka samu a zaɓen da ya gudana ranar 18 ga Maris, 2023. Kazalika, INEC za ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga 'yan majalisar jihohi da suka samu nasarar yayin zaɓen a jihohi 36. Sanarwar da Kwamishinan INEC, Festus Okoye, ya fitar ranar Asabar, ta ce Sashe na 72(1) na Dokar Zaɓe na 2022 ya nuna haƙƙi ne a kan INEC ta miƙa shaidar lashe…
