28
Mar
Wani dattijo mai shekara 85 ɗan ƙasar Saudiyya mai kuma sha’awar aure-aure da tara ’ya’ya, ya sake ɗaura aure da wata matar a karo na 11 domin ya cike gurbin ta huɗu. Mutumin mai suna Ali Al Balawi ɗan ƙasar Saudiyya ya sake ƙara auren ne a karo na 11 da wata mace ’yar ƙasar da ba a bayyana sunanta ba. An ɗaura auren ne a garin Tabbuka da ke Arewa maso Yammacin ƙasar. Ali na da mata uku da kuma ’ya’ya 38, wanda suka ƙunshi maza 18 da mata 20 da kuma jikoki 88, ya kuma ƙara auren ne…
