27
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Operation Hadin Kai ta sojin Nijeriya da ke yaki da Boko Haram ta gudanar da gasar karatun Al-Kur’ani ta matasa a yankin Monguna na Jihar Borno. Muhammad-Nur Mustapha, wanda ya zama gwarzon gasar, ya samu karramawa da kyautar kujerar zuwa aikin Umrah. Wanda ya zo na biyu kuma, Zaharadeen Yusuf ya samu kyautar kuɗi Naira 300,000 sai Mohammed Ali da ya zo na uku da aka ba wa kyautar kuɗi Naira 200,000. Sauran wadanda suka samu karrmawa sun haxa da wanda ya fi iya ƙira’a da dai suransu. Babban Limamin Monguno, Alhaji Liman Kaumi, ya…
