Editor

9513 Posts
Me ya rage wa Matawalle da Ganduje a jihohinsu?

Me ya rage wa Matawalle da Ganduje a jihohinsu?

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammadu Bello Matawalle na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar PDP, Dauda Lawal Dare. Dauda Lawal ya samu ƙuri’u mafi rinjaye ne a zaɓen kamar yadda hukumar zaven ƙasar ta sanar. Jihar Zamfara mai fama da rikicin ’yan bindiga, a yanzu ta koma hannun jam’iyyar PDP, wanda mu ke da tabbacin da yardar Allah za ta kawo kan lamarin. Dama a shekara ta 2019, kotu ce ta bai wa Matawalle kujerar gwamna bayan da ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta bi ƙa'ida ba wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani. Gwamnan…
Read More
Wani soja ya yi kuskuren bindige mata da miji da jaririnsu a Neja

Wani soja ya yi kuskuren bindige mata da miji da jaririnsu a Neja

Daga AMINA YUSUF ALI Wani soja a Jihar Neja ya bindige mutane uku 'yan Jamhuriyar Benin har lahira a yankin Babana da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja. Ciyaman ɗin ƙararmar hukumar Borgu, Alhaji Suleiman Yarima, wanda ya tabbatar da faruwar al'amarin ya roƙi al'ummar Babana da su kasance cikin lumana a game da kisan da aka yi wa danginsu, tare da ba su tabbacin cewa rundunar sojojin Nijeriya suna kula da lamarin. Kuma ya ba wa mutanen tabbacin cewa shari'a za ta nuna ikonta. Wani shaidar gani da ido kuma mazaunin yankin da abin ya faru, Audu Alkali,…
Read More
Dole a rage kuɗaɗen da ake ba shugabannin Nijeriya

Dole a rage kuɗaɗen da ake ba shugabannin Nijeriya

Ya zama dole a rarrage kuɗaɗen albashi da na alawus-alawus na duk waɗansu zaɓaɓɓun ’yan siyasa tun daga ƙasa har sama. A nan ina nufin tun daga kansiloli har zuwa shugabannin ƙananan hukumomi, sannan da ’yan majalisar jihohi da majalisun gaba ɗayansu. Daga nan kuma sai a rarrage kuɗaɗen ’yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa. Gaskiya kullum ana cewa talakawan ƙasa suna cikin matsin rayuwa amma an ƙasa ganin yaya al’amarin yake, kuma an yi mirsisi an ki fahimtar ababen da gangan da ganganci. Gaskiyar lamari gwamnati mai ci yanzu tunda ta kama ragamar mulki a shekarar 2015, sai kawai…
Read More
Zaɓe sai haƙuri fa!

Zaɓe sai haƙuri fa!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Wasu na kuka wasu na dariya don rashin gamsuwa ko gamsuwa da sakamakon babban zaɓen Nijeriya kama daga na Shugaban Ƙasa zuwa na gwamnoni, ’yan majalisar tarayya da na jiha da a ka kammala in ka deve wajajen ƙalilan da hukumar zaɓen ta ayyana cewa zaɓe bai kammala ba. Duk abun da za a ce a zaɓe sai an samu wanda ya lashe da kuma wanda bai lashe ba. Wani abu dai shi ne kowa zai so a ce shi ya lashe. Shin zaven an yi adalci ko ba a yi adalci ba, wannan ba shi…
Read More
Ƙarancin takardun kuɗin Naira

Ƙarancin takardun kuɗin Naira

Ƙarancin Naira na cigaba da shafar ’yan Nijeriya da ’yan kasuwa duk da cewa Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bin umarnin da Kotun Ƙoli ta yanke na cewa tsofaffin takardun kuɗin Naira za su ci gaba da yaɗuwa a kasuwa har zuwa ƙarshen shekara. Taɓarɓarewar sha'anin kuɗin dai na ci gaba da ƙaruwa duk da umarnin da CBN ya baiwa bankuna na ci gaba da fitar da tsoffin takardun kuɗi kamar yadda Kotun Ƙoli ta yanke. Wani bincike da masana da ƙungiyar masu tunani na CBN suka yi na sake fasalin manufofin Naira da kuma tasirinsa ga ’yan ƙasa da…
Read More
Aikata rashawa: Za mu cafke wasu gwamnoni da zarar sun sauka daga kan mulki – EFCC

Aikata rashawa: Za mu cafke wasu gwamnoni da zarar sun sauka daga kan mulki – EFCC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa, ta kammala shirye-shiryen kama tare da hukunta wasu gwamnonin da wa’adin mulkinsu ke ƙarewa waɗanda ake zargi da ayyukan rashawa. Hakazalika, EFCC ɗin bayyana shirinta na kama wasu gurɓatattun masu riƙe da muƙaman gwamnati bayan miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Shugaban EFCC, Mista Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka ranar Alhamis yayin tattaunawa da manema labarai. Sai dai Bawa bai bayyana sunaye ko kuma yawan waɗanda suke shirin kamawa ba da zarar sun sauka daga kan mulki. A sane cewa a bisa…
Read More
‘Yan Shi’a sun koka da ci gaba da tsare Sheikh El-Zakzaky

‘Yan Shi’a sun koka da ci gaba da tsare Sheikh El-Zakzaky

Daga SANI AHMAD GIWA Ƙungiyar Harkar Musulunci a Nijeriya, wato Shi'a, ta sake kokawa kan ci gaba da tsare shugabansu, Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky. A cewar ƙungiyar, shugabansu ba shi da cikakkiyar lafiya a lokacin da yake tsare, wanda shi ne babban dalilin da ya sa suka fara muzaharar 'Free Zakzaky' a Abuja. Idan dai ba a manta ba, duk da wasu hukunce-hukuncen da kotuna suka yanke na bayar da umarnin sakin jagoran da matarsa ​​Zeenat Ibraheem ba tare da wani sharaɗi ba, gwamnatin Buhari na ci gaba da tauye musu haqqinsu ta hanyar sanya musu takunkumin tafiye-tafiye tare da…
Read More
Mutum 21 sun mutu a hatsarin mota a hanyar a Maiduguri

Mutum 21 sun mutu a hatsarin mota a hanyar a Maiduguri

Daga ABUBAKAR M. TAHEER Wata mota ƙirar Hummer mai laba JMA 59 XA, wadda ta taso daga garin Hadejia zuwa Maiduguri ta yi haɗari wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum 21. Lamarin ya faru ne a garin Udubo da ke Ƙaramar Hukumar Gawama, Jihar Bauchi, bayan da tayar gaban motar ta fice, hakan yasa direban motar rikicewa nan take ta doke mutane huɗu dake gefen titi ta kuma kama da wuta. Bayan zuwan jami'an 'yan sanda wurin, sun ɗauki mutum huɗu da suka ji raunuka da gawarwakin mutum 21 zuwa FMC da ke Azare. Daga nan ne aka kwashi…
Read More
Mbappe ya zama kaftin ɗin tawagar Faransa

Mbappe ya zama kaftin ɗin tawagar Faransa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Watanni uku bayan shan kayenta a wasan ƙarshe na kofin Duniya, tawagar ƙwallon ƙafar Faransa ta buɗe wani sabon babi a duniyar ƙwallo, inda da dama daga cikin ‘yan wasanta suka yi ritaya, lamarin da ya bai wa Kylian Mbappe damar zama kyaftin ɗin tawagar don tunkarar wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai na EURO 2024. Yayin wasan ƙarshen dai ƙarƙashin gasar kofin Duniya da ta gudana a Ƙatar anga yadda Argentina ta doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan tashi wasa 3 da 3. Babban koma baya ga tawagar…
Read More
Majalisa za ta binciki ƙin amincewa da gyaran wasu sassan Kundin Tsarin Mulki da Buhari ya yi

Majalisa za ta binciki ƙin amincewa da gyaran wasu sassan Kundin Tsarin Mulki da Buhari ya yi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Dattawan Nijeriya ta kafa wani kwamiti da zai binciki dalilin da ya sa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa da ƙuduri 19 cikin 35 na kundin tsarin mulkin ƙasar da majalisar ta miƙa masa. Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Talata, 21 ga watan Maris, 2022, ya bayyana hakan a jawabinsa yayin da ake ci gaba da zama bayan kammala zaɓen gwamna da na ’yan majalisun jihohi. A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan wasu dokoki 16 na gyara kundin tsarin mulkin qasar daga cikin ƙudirori 35…
Read More