Editor

9513 Posts
Matawalle ya amsa shan kaye kuma ya nemi afuwar mutanen Zamfara

Matawalle ya amsa shan kaye kuma ya nemi afuwar mutanen Zamfara

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara ya amsa shan kaye a zaɓen da aka kammala tare kuma da neman afuwa. Ɗan takatar Jam'iyyar PDP Dauda Lawal Dare ne ya kayar da gwamnan. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani saƙon murya da ya fitar ga 'yan jihar, inda ya ce shi da magoya bayansa sun karɓi ƙaddara. Ya ce lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, ya zauna tare da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar wajen ganin an samo hanyoyin dawo da zaman lafiya ta…
Read More
FIRS: Ma’aikata sun koka da rashin bin ƙa’ida wajen ƙarin matsayi

FIRS: Ma’aikata sun koka da rashin bin ƙa’ida wajen ƙarin matsayi

Daga AMINA YUSUF ALI Ma'aikata a hukumar tattara haraji FIRS sun koka tare da nuna rashin gamsuwa a kan yadda aka gudanar da ƙarin muƙami a ma'aikatar. Wani ma'aikaci a hukumar ya bayyana yadda mahukuntan hukumar suka kasa bin tsari wajen gudanar da ƙarin matsayi ga ma'aikatanta.  Wannan ƙorafin yana qunshe ne a wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai ɗauke da jawabin ƙorafi wadda aka yi wa ministar kuɗi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed inda aka kira ta da ta shigo cikin maganar kuma ta taka wa mahukuntan burki a kan al'amarin.  A cikin takardar ƙorafin ma'aikatan sun zargi mahukuntan FIRS da keta…
Read More
Ramadan: Babu wani dalilin da zai sa ’yan kasuwa su riƙa ƙara farashi saboda azumi – Buhari

Ramadan: Babu wani dalilin da zai sa ’yan kasuwa su riƙa ƙara farashi saboda azumi – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi ’yan kasuwar dake ƙara farashin kayayyaki saboda zuwan azumi da su daina saboda ya saɓa da koyarwar Musulunci. Ya bayyana haka ne ranar Laraba, a cikin saƙonsa ga al’ummar Musulmi kan shiga watan Ramadan da aka fara ranar Alhamis. Buhari, ya kuma shawarci Musulman Nijeriya da su yi amfani da lokacin wajen haskaka kyawawan ɗabi’un addinin Musulunci a mu’amalolinsu, ba wai kawai a baki ba. Sanarwar, wacce Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, “Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen bayyana kyawawan ɗabi’un…
Read More
PDP ta sake tsunduma cikin rikici, ta dakatar da wasu jiga-jiganta

PDP ta sake tsunduma cikin rikici, ta dakatar da wasu jiga-jiganta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga-jigan mambobinta da suka haɗa da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Pius Anyim, Farfesa Dennis Ityavyar da Aslam Aliyu, bisa zargin katsalandan a harƙallar jam'iyyar. Bayanin Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Mista Debo Ologunagba, a ranar Alhamis. Sanarwar ta kuma cigaba da cewa, “Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na Jam’iyyar PDP ya yi nazari sosai kan al’amuran jam’iyyarmu a ƙasar nan da kuma bin tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin PDP (kamar yadda aka…
Read More
2023: Gwamnoni 17 sabbin yankan rake – 9 ’yan tazarce – 2 ’yan jiran tsammani

2023: Gwamnoni 17 sabbin yankan rake – 9 ’yan tazarce – 2 ’yan jiran tsammani

Daga SANI AHMAD a Abuja A ranar Asabar, wacce ta zo daidai da 18 ga Maris, 2023, ne aka gudanar da zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisun dokokin Nijeriya bayan kusan kammala wa’adin mulkinsa na yanzu. An gudanar da zaɓukan gwamnonin a jihohi 28, yayin da sauran takwas kuma aka gudanar da na majalisun dokokin jihohin tare da na jihohin 28. Ma’ana; an yi zaɓen ’yan majalisar dokokin jihohin Nijeriya 36 bakiɗaya, amma a jihohi 28 ne kawai aka yi na gwamnoni. Wannan ya biyo bayan wasu hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli ne da ya shafi zangon mulkin wasu jihohi ne, waɗanda…
Read More
Kotu ta tabbatar da Adeleke Gwamnan Osun

Kotu ta tabbatar da Adeleke Gwamnan Osun

Daga WAKILINMU Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin Gwamnan Jihar Osun. Tun bayan zaɓen gwamna da ya gudana a jihar ranar 16 ga Yulin bara, ɗan takarar jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya tafi kotu inda ya ƙalubalanci nasarar da Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya samu yayin zaɓen. A ranar Juma'a, Kotun Ƙolin ƙarƙashin Mai Shari'a Mohammed Shuaibu, ta yanke hukunci kan shari'ar inda ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamnan jihar.
Read More
Buhari ya rattaɓa hannu kan Dokar Kare Haƙƙin Mallaka

Buhari ya rattaɓa hannu kan Dokar Kare Haƙƙin Mallaka

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu kan Dokar Kare Haƙƙin Mallaka ta 2022 da kuma wani ƙudiri guda da Majalisar Tarayya ta zartar kwanan nan. Rattaɓa hannun ya haɗa da Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya na Medical Laboratory da ke Jos, ta 2023. Babban Hadimin Shugaban Kan Harkokin Majalisar Wakilai, Hon. Nasiru Baballe Ila, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis. Baballe ya ce Buhari ya sanya wa dokokin biyu hannu ne a ranar 17 ga Maris. Ya ce Dokar Kare Haƙƙin Mallakar ta 2022 wadda ta maye gurbin…
Read More
CBN ya umarci bankuna su fito aiki ranakun ƙarshen mako

CBN ya umarci bankuna su fito aiki ranakun ƙarshen mako

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna da su ƙara kwanakin aikinsu zuwa Asabar da Lahadi. CBN ya ce ya yanke hakan ne domin tabbatar da wadatar kuɗi a bankuna don amfanin jama'a. Bankin ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a ta bakin Daraktansa, wato Isa AbdulMumin. Sanarwar ta ce tuni CBN ya fara tura kuɗaɗe zuwa bankuna a sassan ƙasa baki ɗaya. “CBN ya ba da umarnin bankuna su loda kuɗi a cikin na'urorin ATM, sannan su ci gaba da aiki har da ranakun karshen mako. “Bankuna za su yi aiki a…
Read More
Hisbah za ta cafke Musulmin da ba sa azumi a Kano

Hisbah za ta cafke Musulmin da ba sa azumi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi barazanar hukunta duk waɗanda aka kama su na aikata munanan ɗabi’u a wannan wata mai albarka na Ramadana, ciki har da ƙin yin azumin na watan Ramadana. Hakan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Ibrahim Lawan, ya fitar ranar Alhamis a Kano, inda ya ce, Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Dakta Harun Ibn-Sina, ya bayyana cewa, waɗanda suke aikata munanan ɗabi’u a cikin wannan wata mai alfarma, za a yi maganin su. “Wasu daga cikin matasan da ke cin abinci…
Read More
Muna fatan sabon Gwamnan Katsina ya tabbatar da Hukumar Hisba a jihar – Rabiu Garba.

Muna fatan sabon Gwamnan Katsina ya tabbatar da Hukumar Hisba a jihar – Rabiu Garba.

Daga RABI'U SANUSI a Kano An yi kira ga zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr Dikko Raɗɗa, da ya taimaka wajen tabbatar da Hukumar Hisbah ta ƙasa reshen jihar dan aikin cigaban jihar da ma ƙasa baki ɗaya. Wannan kira ya fito ne daga bakin sabon Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar Katsina, Alh. Muhammad Rabiu Garba (Aminchi), jim kaɗan bayan tabbatar da shi matsayin sabon Kwamandan Hukumar na jihar. Muhammad Rabiu Garba ya ce sahalewar Hukumar ta Hisbah a jihar zai taimaka wajen daƙile matsalolin yau da kullum da ke ƙara samun gindin za ma a wasu ɓangarorin jihar. Don haka…
Read More