24
Mar
Daga MUHAMMAD M. MUSTAPHA A matakin farko, bayan Hijirarsa zuwa garin Madina Haskakkiya, Annabi Muhammadu SAW ya rubuta yarjejeniyar zamantakewa, don tabbatar da zaman lafiya da lumana. Ya zo a cikin wannan yarjejeniya, kamar yadda Malam Ibnu Hisham ya bayyana a littafinsa Assirah Annabawiyya, cewa: 'tabbas Yahudawan Banu Auf al'umma ɗaya ne tare da Muminai, Yahudawa su yi addininsu Musulmi ma su yi addininsu. Haka Yahudawan Banun Najar, Banul Haris, Banu Sa'idah…..duk al'umma ɗaya ne tare da Muminai'. Hakana wannan yarjejeniya ta ci gaba da bayanin haɗaka ta taimakekeniyar rayuwa a tsakanin wannan al'umma ɗaya masu mabanbantan addinai: kowa a…
