22
Mar
22
Mar
Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ta ina zan fara wannan rubutu da na so yi tun lokacin zafin babban zaɓen Nijeriya na shugaban ƙasa da ’yan majalisar dokoki a ranar 25 ga watan jiya. Mu na cikin ɗakin sauraron sakamakon zaɓe a lokacin da a ka kawo sanarwar farko ta sakamakon jihar Ekiti ne in zan tuna daidai sai Saleh Shehu Ashaka ya bugo min waya bayan mun ɗan yi taƙaitacciyar magana sai ya ce min “ka na da labarin rasuwar Shehu Saulawa?” nan fa na ɗauka da Inaa Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, Allah ya yi wa Saulawa rasuwa? Rayuwa…
22
Mar
Daga LARABI LARABEEN Zuwa ga jarumi Adam A. Zango, Ina fata wasiƙata ta same ka cikin ƙoshin lafiya. Game da maganar da ka yi cewa, ba za ka ƙara aure ba har abada, haba don Allah! Bai kamata ka ce haka ba. Da ma tin filazal fitattun mutane kan sha fama da matsaloli kala-kala. Amma kai naka kuskuren ya samo asali a kan yadda kake zaɓen macen aure mai kyawu fuska fiye da kyawun ɗabi'a da tarbiyya. Wata matsalar taka kuma ita ce, ka daina auren macen da take son Adam A. Zango na Film. Ka nemi macen da take…
22
Mar
"Ilimin manya makami ne na gyara al'umma" Daga ABUBAKAR M. TAHIR Amina Ahmed Sani Gumel 'yar Nijeriya ce wanda ta ke zaune a Ƙasar England inda ta ke koyar da ilimin manya masu koyon yaren Turanci a matsayin yare na biyu. A cikin tattaunawarta da wakilin manhaja, ta kawo irin hanyoyin da suke bi wajen koyar da mutane baƙi yaren Turanci wanda zama ya kama su a Ƙasar England. Haka kuma ta kawo irin ƙalubalen da ta fuskanta wajen yaren Turanci dama irin nasarorin da ta samu a matsayin mai koyar da yaren Turanci a Ƙasar England. A sha karatu…
22
Mar
Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Marubuciya Jamila Mamy Janafty, wacce sananniyar marubuciyar yanar gizo ce da ta wallafa littafan Hausa da dama da suka haɗa da 'Saifuddeen', 'Ta Fita Zakka', 'Gidanmu' da dai sauransu. Ta ƙaryata raɗe-raɗin cewar Allah Ya yi mata rasuwa a ranar Asabar da ta gabata 11 ga Marsi, 2023. Zancen da ya mamaye duniyar rubutu da marubuta cikin ƙanƙanin lokaci, kamar wutar daji. Marubuciya Janafty, cikin wani gajeren rubutu da ta fitar dai, ta bayyana cewa: ba ma ita ba ce a hoton da ake ta yaɗawa da nufin ita ce, asali ma ba ta da…
21
Mar
Daga RABI'U SANUSI a Kano Jam’iyyar APC a Jihar kano ta yi fatali da zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar ɗin da ta gabata, tare da neman hukumar zaɓe, INEC, ta soke zaɓen. Shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan lokacin taron manema labarai wanda ya gudana a ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar da ke cikin birnin a ranar Larabar. Abdullahi Abbas wanda mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Barr. Abdul Adamu Fagge ya wakilta, ya ce zaɓen da aka gudanar a ranar Aasabar, 18 ga watan Maris akwai kura-kurai…
21
Mar
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da kama wasu ɓata-gari da ake zargi da cinna wuta a gidan shaharrren mawaƙi, Dauda Kahutu Rarara. Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Kiyawa ya ce sun cafke mutanen ne bisa zargin ƙone wani ɓangare na gidan mawaƙin Jamiyyar APC, biyo bayan samun Nasarar Abba Kabir Yusif na Jamiyyar NNPP a zaɓen Gwamnan Jihar Kano. Ya ce za su gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu cikin lamarin da…
21
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire ta JAMB, ta gindaya wasu sabbin ƙa’idoji don daƙile jabun takardun shaidar 'A Level' yayin da ta kuma dawo da rajistar DE 2023. Sakataren hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya ce za a rufe rajistar DE ranar 28 ga watan Afrilu. Yayin da yake kokawa kan yadda ake amfani da takardar shaidar matakin 'A' na jabun takardu wajen yin rajistar, Mista Oloyede ya ce hukumar ta ɓullo da sabbin tsare-tsare don tantance irin…
21
Mar
Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar gwamna ƙarƙashin Jam'iyyar APC a jihar Neja, Mohammed Umar-Bago, shi ne ya lashe zaɓen da ya guda a jihar Asabar da ta gabata. Bago, wanda ɗan Majalisar Wakilai mai ci ne mai wakiltar mazaɓar Chanchaga, ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 469,896, in ji INEC. Baturen zaɓen, Clement Alawa, ya ce an tabbatar da Bago a matsayin wanda ya ci zaɓen ne bayan cika duka sharuɗɗan da suka dace. Alhaji Isah Liman Kantigi na Jam'iyyar PDP shi ne ya rufa wa Bago baya da ƙuri'u 387,476, in ji Mr Alawa.
21
Mar
Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Ɗan Marke, ya yi watsi da sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta bayyana. Cikin wata hira da ya yi da BBC, Sanata Lado, ya ce, zaɓe ne mai cike da maguɗi da aringizon ƙuri'u da barazana ga masu zaɓe, da dai duk wani ha'incin da bai taɓa gani a harkar zaɓe ba. Ya ce, "Ba mu gamsu da wannan sakamakon zaɓen ba tun da mun san ba abin da al’umma suka zaɓa ba ne aka bayyana.” Ɗan takarar ya…
