21
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA Tsohon mai shiga tsakani wajen tattaunawa da 'yan ta'adda, Tukur Mamu, ya ƙi amsa tuhumar laifuka 10 da Gwamnatin Tarayya ke zarginsa da aikatawa. A ranar Laraba ofishin Babban Lauyan Nijeriya ya gurfanar da Mamu a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin taimaka wa 'yan ta'adda. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, Mai Shari’a Nkeonye Maha na wata kotun tarayya a ranar 13 ga watan Satumba, 2022, ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, izinin tsare tsohon ɗan mai sasanci tsakanin 'yan ta'addan…
