Editor

9307 Posts
Yobe ta ɗage dokar haramcin hawa babur a wasu ƙananan hukumomin jihar

Yobe ta ɗage dokar haramcin hawa babur a wasu ƙananan hukumomin jihar

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗage dokar hana hawa babura a Yobe ta Gabas, yankin da ya ƙunshi ƙananan hukumomi bakwai a jihar. Ɗagewar ta soma aiki ne daga ranar yau Litinin, 6 ga Maris. Sanarwar manema labarai wanda ofishin mataimaki na musamman ga Gwamna kan harkokin tsaro ya fitar, Brigadier General Dahiru Abdulsalam (Mai ritaya) ta nuna cewa, Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni shi ne ya amince da ɗage haramcin. Ta ƙara da cewa, "An ɗage wannan haramci na hawa babur mai, daga yau 6 ga watan Maris 2023 a cikin ƙananan hukumomi…
Read More
Sabuwar cutar mashaƙo ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 61 a Kano

Sabuwar cutar mashaƙo ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 61 a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Ɓarkewar sabuwar cutar mashaƙo wacce ake kira da diphtheria a turance ta kashe mutum 61 a jihar Kano. An samu wannan rahoto a jihar Kano ranar 2 ga Maris, 2023. Shugabar kes ɗin cutar ta jihar Kano, Dakta Salma Suwaid, ita ta bayyana haka a ranar Litinin a wani taro wanda Cibiyar dadaitawa da kariya ga cututtuka ta shirya. Dakta Suwaid ta ƙara da cewa, jimillar marasa lafiya 783 ne yanzu haka suke kwance a asibiti. Inda 360 daga cikinsu mata ne, yayin da 423 daga ciki kuma maza ne. Diphtheria matsananciyar cuta ce wacce nau'in…
Read More
Kotu ta ba da belin Ado Doguwa

Kotu ta ba da belin Ado Doguwa

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano ta bayar da belin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa a kan naira miliyan 500. A makon jiya ne wata Kotun Majistare da ke zamanta a Unguwar Nomansland ta Jihar Kano, ta tura Alhassan Doguwa gidan waƙafi. A yayin zaman kotun a ranar Litinin, lauyan wanda ake zargi, Nureini Jimoh (SAN), ya gabatar da buƙatar bayar da belin wanda yake karewa a gaban Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa, bisa hujjar cewa doka ta ba shi wannan ’yanci da kuma cewa Kotun Majistare ɗin ba ta da hurimin tsare shi. Lauya…
Read More
Ɗan sanda ya bindige mutum don ya ce APC za ta lashe zaɓen gwamna a Filato

Ɗan sanda ya bindige mutum don ya ce APC za ta lashe zaɓen gwamna a Filato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani jami’in ɗan sanda ya harbe wani mutum mai suna Nyommena Salah Badapba a lokacin da suke taƙaddamar siyasa a unguwar Tudun Wada da ke garin Jos a Jihar Filato. Ɗan sandan, Solomon Damak, ya harbe Badapba ne a lokacin da suke muhawara kan wanda zai fito a matsayin wanda zai lashe zaɓen gwamna da za a yi ranar 11 ga watan Maris. An tattaro cewa, jami’in ya ce jam’iyyar APC ba za ta ci zaɓe mai zuwa ba, amma Badapba ya ƙi amincewa da shi. Ɗan sandan ya fusata da hakan, sai ya harbi Badapba…
Read More
Kotu ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a Zamfara

Kotu ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau. Kotun Ƙolin ta tabbatar da Dr. Dauda Lawal Dare a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar Gwamna ƙarƙashin Jamiyyar PDP a zaɓen da za a gudanar ranar Asabar Mai zuwa. Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu kafin zaɓen gwamnanoni da na 'yan majalisun jiha da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya a jihohi 36 na ƙasar nan. Kotun Ɗaukaka Ƙara reshen Sokoto ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a ranar 6 ga watan Janairun 2023 inda ta soke zaɓen fidda gwani…
Read More
INEC ta garzaya kotu kan sake fasalin na’urar BVAS

INEC ta garzaya kotu kan sake fasalin na’urar BVAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce za ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ba ta damar sake fasalin tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) a gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da za a yi ranar 11 ga Maris, 2023. Wani babban jami’in hukumar da bai so a ambaci sunansa ya shaida wa Aminiya irin ci gaban da aka samu a ƙarshen mako a Abuja. Majiyar ta yi nuni da cewa wannan umarni na da matuƙar muhimmanci biyo bayan umarnin da aka ba shi na hana…
Read More
BIDIYO: Atiku da wasu jiga-jigan PDP sun jagoranci zanga-zanga zuwa ofishin INEC

BIDIYO: Atiku da wasu jiga-jigan PDP sun jagoranci zanga-zanga zuwa ofishin INEC

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, tare da abokin takarsa, Ifeanyi Okowa sun jagoranci zanga-zangar lumana zuwa babban ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a Abuja. Daga cikin waɗanda aka hango su a dandazon masu zanga-zangar, har da shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, Abiye Sekibo, Dino Melaye da kuma Uche Secondus. Zanga-zangar ɓangare ne na ci gaba da nuna rashin yarda da sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da ya guda asabar ta makon jiya, inda mambobin jam'iyyar suke zargin ba a yi adalci ba. Zanga-zangar wadda aka faro ta…
Read More
Elon Musk ya sake ƙwato kambunsa na mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

Elon Musk ya sake ƙwato kambunsa na mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

Daga AMINA YUSUF ALI Elon Musk ya sake dawowa matsayinsa na mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya bayan ya tara maƙudan kuɗaɗe har Dalar Amurka biliyan $6.98 a cinikin awoyi takwas kacal. Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne dai attajiri Musk ya rasa muƙamin nasa na mai arzikin duniya bayan da wani Bafaranshen attajiri mai suna Bernard Arnault ya yi masa ƙafar baya tare da ture shi, kuma ya haye ƙaragarsa ta mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya, a ranar 8 ga watan Disambar, 2022. Al'amarin da ya jawo Musk ya rasa wancan…
Read More
Muhimmancin sada zumunci

Muhimmancin sada zumunci

Assalamu alaikum. Da farko dai, sada zumunci shi ne kyautatawa da jinƙai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk ɓangare ne na sada zumunci. Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga ɗan uwa yayin haɗuwa da gaishe shi da ce masa Yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi. Sannan zuwa duba…
Read More