20
Mar
Daga UMAR GARBA a Katsina Babbar jam'iyyar hamayya a jihar Katsina, wato PDP, ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar. Babban Daraktan yaƙin neman zaɓen Lado/Atiku, Mustapha Muhammad Inuwa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da Jam'iyyar ta kira a birnin Katsina. Inuwa ya ce sun yi Allah wadai da sakamakon da hukumar zaɓe ta fitar a jihar. Kazalika, ya ce ba su yarda da shi ba, kuma za su garzaya kotu. "Mun ƙi karɓar wannan zaɓen, ba mu yarda da shi ba kuma ba mu amince da shi ba a…
