13
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyoyin goyon bayan jam’iyyar AAPC sun yi kira ga jam’iyyun siyasa da su rungumi haɗin kai da ’yan uwantaka da Bola Ahmed Tinubu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya yi musu. Darakta Janar na ƙungiyar, Dakta Kailani Muhammad, ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a wajen wani taron Leadership of APC Grassroots Independent Campaign Council a Abuja. Muhammad ya buƙace su a matsayinsu na ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su haɗa kai da Tinubu wajen gina ƙasa domin ciyar da ƙasa gaba. “Muna kira ga jam’iyyun adawa, PDP, Labour Party da mambobinsu da su karɓi…
