14
Mar
Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Alƙalin Babbar Kotun Jihar Yobe, Mai Shari'a Muhammad Lawu Lawan, ya garƙame Odita Janar na Ma'aikatar Ƙananan Hukumomin Jihar Yobe, Alhaji Idris Yahaya, a gidan yari na tsawon shekara biyar, sakamakon samunsa da aikata almundahana da kuɗaɗen al'umma, ranar Litinin. Kotun ta samu wanda ake zargin da laifin karkata akalar wasu kuɗaɗen da suka kai Naira miliyan 19,900,000 ba bisa ƙa'ida ba, wanda ofishin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na yankin, wanda yake a Maiduguri babban jihar Borno, ya gurfanar da shi. Bayanai sun nuna Alh. Yahaya ya karɓi wannan kuɗin…
