15
Mar
Daga NAFI'U SALISU An daɗe ana ruwa ƙasa tana shanyewa. A yau shekaru 63 da Nijeriya ta samu ‘yancin kai daga Turawan mulkin-mallaka, amma har yanzu ɗan Nijeriya bai bambance tsakanin mulkin-mallaka da mulkin dimokraɗiyya ba, sakamakon rashin iya shugabanci ko kuma dai rashin sanin kima da mutuntakar ‘yan ƙasa. Idan muka kalli yadda tsarin tafiyar da mulkin shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari yake tafiya, zamu iya cewa gara jiya da yau. Domin kafin zuwan wannan Gwamnatin ta Buhari a shekarar 2015 zuwa yau, ‘yan Nijeriya suna gudanar da rayuwarsu cikin sauƙi, don kuwa kayayyaki da kayan masarufi na abinci suna…
