17
Mar
*Ba a san maci tuwa ba..! Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gobe ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki na jihohi a Tarayyar Nijeriya, waɗanda ake sa ran rantsarwa a ranar 29 ga Mayu, 2023, bayan kammala wa’adin zangon gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na jihohi. Zaɓen da ya gabata na 2019 ya zo da wani sabon salon ƙa’idar da ba a saba gani ba a zaɓukan baya, inda ba a sanar da sakamakon zaɓe bisa dalilin wata kalma ta ‘inconclusive’, wacce ta ke nufin ‘rashin kammaluwa’ ko kuma ‘zaɓen da bai kammalu ba’. Shin mene ne…
