Editor

9513 Posts
Ban janye daga takarar Gwamnan Jihar Kaduna ba – Sani Sha’aban

Ban janye daga takarar Gwamnan Jihar Kaduna ba – Sani Sha’aban

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar kujerar Gwamna a Jihar Kaduna a ƙarƙashin Jam'iyyar ADP, Honorabul Sani Sha'aban, ya bayyana cewa maganganun da wasu ke yi cewa ya janye takararsa bai san wannan zancen ba, domin kuwa shi ma ji ya yi kamar almara. Ɗan takarar, wanda ya bayyana cewa duka 'yan takarar da ke neman Gwamna a Jihar Kaduna 'yan'uwa ne domin duk daga Zazzau suka fito, ya bayyana cewa shi bai ƙullaci kowa ba, kuma ba shi da niyyar ƙullatar wani a zuciyarsa. Ɗan takarar, wanda ke magana a cikin wata hira da aka yi da…
Read More
Zan kafa gwamnatin nagarta da dacewa ba ta haɗin kan ƙasa ba – Tinubu

Zan kafa gwamnatin nagarta da dacewa ba ta haɗin kan ƙasa ba – Tinubu

Daga AMINA YUSUF ALI Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da suke a dukkan faɗin jam'iyyu mabanbanta da su ba da goyon baya ga gwamnatin da yake shirin kafawa a Nijeriya, yayin da ya bayyana cewa, ba zai yi kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa ba idan aka rantsar da shi, sai dai ya amince zai tafiyar da gwamnati mai nagarta. Tinubu ya ƙara da cewa, a yayin da zai zaɓi masu taimaka masa a fadarsa ta shugabancin ƙasa, zai zaɓa ne bisa la'akari da cancanta da dacewa. Wannan jawabi yana ƙunshe ne a…
Read More
Rayuwata na cikin hatsari bayan janye mini jami’an tsaro – Sanata Lado

Rayuwata na cikin hatsari bayan janye mini jami’an tsaro – Sanata Lado

Daga UMAR GARBA a Katsina Ƙasa da sa'o'i 24 kafin gudanar da zaɓukan gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a Jam'iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, ya zargi Babban Sufeton 'Yan Sanda da janye masa jami'an dake tsaron lafiyarsa. Sanata Lado ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da gidan Talabijin na Channels a cikin shirin 'Sunrise Daily' wanda Manhaja ta bibiya. A cewarsa, an janye masa jami'an tsaron ne tun mako biyun da suka gabata saboda bambancin ra'ayin siyasa. "Muna fuskantar tsangwama da barazana daga gwamnati, rayuwata na cikin hatsari maganar da nake yi…
Read More
Wadata a Musulunci

Wadata a Musulunci

Daga MUHAMMAD M. MUSTAPHA Talauci ɗan uwan kafirci, in ji malaman zaure. Al-Imamul Gazali a littafinsa Ihya'u Ulumiddin yana cewa: 'rabauta a lahira ba za ta samu ba sai addinin mutum ya gyaru, addini ba zai taɓa gyaruwa ba sai duniyar mutum ta tsaru, duniya ba za ta taɓa tsaruwa ba sai sana'u da harkokin naiman arziƙi sun tsaru', tsaruwar sana'u da harkoki kuma su ke korar talauci da samar da wadata da nutsuwa, wani abu da malaman zamani ke kira da gyaruwar ɗan Adam a farko kafin gudanar ibadun addini'', ko al-insaniyyatu qablat tadayyin. Malam Sufyan Assauri ya na…
Read More
Yadda Tinubu ya yaudari Obi ya yi takarar shugaban ƙasa don raba ƙuri’un PDP – Omokri

Yadda Tinubu ya yaudari Obi ya yi takarar shugaban ƙasa don raba ƙuri’un PDP – Omokri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya bayyana cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yaudari ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi takara don a rage ƙuri’un ‘yan adawa. Omokri ya ce Obi ba shi da wata hanyar samun nasara, domin ba shi da goyon bayan 'yan ƙasa, amma zai iya raba ƙuri’un Jam’iyyar PDP. A cewarsa, Tinubu ya yi amfani da amintattun ‘yan kasuwansa wajen yaudarar Obi ya shiga takarar shugaban ƙasa. Omokri ya ƙara da cewa, Tinubu ya nuna gwaninta wajen fahimtar tunanin ‘yan…
Read More
Wike bai taimake ni a zaɓen Shugaban Ƙasa ba – Peter Obi

Wike bai taimake ni a zaɓen Shugaban Ƙasa ba – Peter Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi, ya zargi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da ƙin taimaka masa. Obi wanda ya zanta da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, ya kuma yi zargin an tafka maguɗi a sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a Ribas, inda ya bayyana cewa ya yi nasara a jihar. A Ribas, Bola Tinubu na Jam’iyyar APC, ya samu nasara da ƙuri’u 231,591 yayin da LP ta samu ƙuri’u 175,071. Obi ya ce…
Read More
Gwamna Bala ya yi wa Buhari wasiƙa a gaggauta kama Sadique ɗan takarar gwamna na APC

Gwamna Bala ya yi wa Buhari wasiƙa a gaggauta kama Sadique ɗan takarar gwamna na APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya aika wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wasiƙa ta musamman yana roƙon shugaban ƙasa da ya gaggauta sawa a kama ɗan takarar gwamnan jihar na APC, Sadique Abubakar bisa zargin wai yana ƙoƙarin tada hankalin jama’a a jihar. Gwamna Bala ya ce: ”Tunda aka fara kamfen ɗan takarar APC Sadique Abubakar ya ke yin abin da ya ga dama a faɗin jihar. Yana yawo da dakaren jami’an tsaro yana tsorata mutanen jihar. ”Sadiq yana tafiya ne da ayarin jami’an tsaro ɗauke da makamai da ‘yan baranda da aka kawo daga…
Read More
Ba ni da jam’iyya a yanzu, amma ina goyon bayan wasu ‘yan takara – Dogara

Ba ni da jam’iyya a yanzu, amma ina goyon bayan wasu ‘yan takara – Dogara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya ce shi ba ya cikin jam’iyyar siyasa a yanzu amma yana goyon bayan ’yan takara a faɗin jam’iyya ne kawai don neman muƙamai a zaɓen 2023 mai zuwa. Dogara, wanda ke wakiltar mazaɓar Dass/Tafawa Balewa/Bogoro a zauren majalisar tarayya, ya yi magana a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba wanda News Point Nigeria ke sa ido. Ya kuma ce kasancewar yana goyon bayan ’yan takara na jam’iyyu daban-daban na kujeru daban-daban ba ya nufin cewa shi mutum ne mai “mara son kwanciyar hankali”…
Read More
Za mu yi aiki ba dare ba rana don ganin an yi zaɓen gwamnoni lafiya – Hukumomin tsaro

Za mu yi aiki ba dare ba rana don ganin an yi zaɓen gwamnoni lafiya – Hukumomin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumomin tsaro a Nijeriya, sun bada tabbacin cewa za su yi aiki ba dare ba rana don ganin an yi zaɓukan gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi lafiya a ƙasar. Babban mashawarcin tsaro na ƙasar, Janar Babagana Monguno, mai ritaya ne ya bayyana haka lokacin wani taron kwamitin tuntuɓa tsakanin hukumomin tsaro kan sha'anin zaɓe a ƙasar. Janar Babagana Monguno, ya ce zaɓen gwamnoni da na ‘yan majlisun jihohi na da sarƙaƙiya. Ya ce, “Zaɓukan gwamnonin sun sha bamban da na shugaban ƙasa don kuwa zaɓe ne guda 1,02, abin da ke nufin…
Read More
Har yanzu ban janye wa wani ba, inji ɗan takarar gwamnan Nasarawa a NNPP

Har yanzu ban janye wa wani ba, inji ɗan takarar gwamnan Nasarawa a NNPP

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a inuwar Jam’iyyar NNPP, Alhaji Yakubu Maidoya ya ƙaryata jita-jitar da wasu a jihar ke yaɗawa a yanzu cewa ya janye wa gwamnan jihar wanda shine kuma ɗan takarar Jam’iyyar APC mai ci a jihar, Injiniya Abdullahi Sule. Alhaji Yakubu Maidoya ya sanar da haka ne a jawabinsa a lokacin wata tattaunawar haɗin gwiwa da jam’iyyarsa ta NNPP da ‘yan takarar gwamnan a inuwar jam’iyyun SDP da ADC wadda suka gudanar da manema labarai a babbar sakatariyar ‘yan jarida dake Lafiya, babban birnin jihar ranar Laraba 15 ga…
Read More